Yadda Labaran Kanzon Kurege Ke Haifar Da Illoli Ga Al’umma

Ana dora alhakin rura wutar munanan rikice-rikice a kan labaran kanzon kurege

Yadda Labaran Kanzon Kurege Ke Haifar Da Illoli Ga Al’umma

Shafukan Yanar Gizo


Domin sauke shirin latsa nan

A lokuta da dama, akan dora alhakin faruwar wasu abubuwa marasa dadi a kan yada labaran kanzon kurege, musamman a kafofin sada zumunta.

A baya-bayan nan ma hukumomi a Najeriya sun yi gargadin cewa wasu na yada irin wadannan labarai da nufin tayar da zaune tsaye ko rura wutar rikici.

Su wane ne suke kirkirar labaran kanzon kurege, mece ce manufarsu, kuma wacce illa suke haddasawa?