Yadda ladani ya sauya kiran Sallah a Masar
A ranar Litinin da ta gabata ne wani ladani a kasar Masar ya fara fuskantar hukunci bayan ya sauya yadda ake yin kiran sallar Asuba a wani masallaci da ke lardin Beheira na birnin Alkahira.Ma’aikatar da ke Kula da Addini a kasar ta ce za ta dauki matakin shari’a a kan ladanin, mai suna, Mahmoud […]
A ranar Litinin da ta gabata ne wani ladani a kasar Masar ya fara fuskantar hukunci bayan ya sauya yadda ake yin kiran sallar Asuba a wani masallaci da ke lardin Beheira na birnin Alkahira.
Ma’aikatar da ke Kula da Addini a kasar ta ce za ta dauki matakin shari’a a kan ladanin, mai suna, Mahmoud al-Moghazi, wanda lokacin da yake kiran sallar Asubar ranar Asabar da ta gabata ya ce: “Assalatu Khairun minan-Facebook, wato yin Sallah ya fi yin Facebook alheri”. Maimakon ya ce: “Assalatu Khairun minan-naum, wato yin Sallah ya fi yin barci alheri.”
Da marecen ranar Lahadi ne kuma ladanin ya shaida wa wani gidan talabijin cewa zai fara “yajin cin abinci”, inda ya karyata zargin kuma ya zargi kungiyar ’Yan uwa Musulmi da kitsawa saboda “suna son ganin bayana,” inji shi. Daga nan ya yi kira ga Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na kasar da ya tsoma baki a cikin lamarin.
An dai dakatar da shi daga yin kiran Sallah har sai an gama bincike a kan batun.