…Yadda lamarin yake

Idan dai za a iya tunawa, sarki Salman yanzu ya tsufa sosai, domin ko lokacin da ya karbi mulki a shekarar 2015 bayan rasuwar sarki Abdullah, yana da shekara 79 ne a duniya. Tun bayan darewarsa karagar mulki, Bin Salman wanda a lokacin yana dan shekara 29 ne kawai, sai ya zama shi ne ake […]

…Yadda lamarin yake

Idan dai za a iya tunawa, sarki Salman yanzu ya tsufa sosai, domin ko lokacin da ya karbi mulki a shekarar 2015 bayan rasuwar sarki Abdullah, yana da shekara 79 ne a duniya.

Tun bayan darewarsa karagar mulki, Bin Salman wanda a lokacin yana dan shekara 29 ne kawai, sai ya zama shi ne ake tunani zai ci moriyar zaman mahaifinsa sarki a wannan kurarren lokacin na rayuwarsa.

Daga baya sai aka nada shi Ministan tsaro, inda ba da jimawa ba ya fara aiki, inda ya jagoranci yaki da ‘yan kungiyar Houthi na kasar Yemen a shekarar 2015. Wannan yakin ya janyo cece-ku-ce da yawa a fadin duniya, domin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da yawa.

Yanzu haka dai, Bin Salman shi ne baban jami’in gwamnatin kasar, domin yana da ta cewa a duk lamuran da suka shafi kasar, kamar dokokin cikin gida, alakar kasar da kasashen waje da batun tattalin arziki, da dai sauransu.

Sannan kuma a watan Yulin bana, sarki Salman ya tunbuke Yarima Mohammed bin Nayef a matsayin yarima mai jiran gado, ya nada Bin Salman sabon yariman mai jiran gadon. wanda hakan ya nuna cewa shi ne ake so ya gaji mahaifinsa.

Gidan sarautar Saudiya ya dade cikin rudani da rikici, duk da cewa suna kokari wajen boye bambancinsu. Farfesa Maghraoui yana cewa a game da gidan“Gidan sarautar dama ya dade cikin rikici da rudani. Kawai dai suna boye lamarin ne. Amma wannan sabon shirin na kame-kame da sunan yaki da cin hanci da aka yi, ya kara fito da rikicin gidan fili,” inji Maghraoui.

…Donald Trump ya yaba wa Bin Salman

Shi kuma a nasa  bangaren, shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yaba wa sarki Salman da dan nasa  Bin Salman bisa wannan kokari da suke yin a yaki da cin hanci. Donald Trump ya wallafa a shafinsa na twitter cewa “Ina jinjina wa Sarkin Salman, da Yarima bin Salman, domin sun san abin da suke yi.

“Wadansu daga cikin mutanen da suka kama, sun dade suna cinye dukiyar kasar,” inji shi.