Yadda likita ya rasu minti 15 bayan isa asibiti domin duba marasa lafiya a Kano

Likitan ya rasu jim kaɗan bayan isarsa asibitin domin duba marasa lafiyan da ke jiransa.

Yadda likita ya rasu minti 15 bayan isa asibiti domin duba marasa lafiya a Kano

Wani Babban Ƙwararren likita a Jihar Kano, Dokta Ibrahim, ya rasu bayan ya faɗi jim kaɗan bayan isa wani asibiti domin duba marasa lafiya da ke jiransa.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar a Asibitin Arewa Surgery da ke Hotoro, a Kano.

An nemi Dokta Ibrahim ya maye gurbin wani likita da ba zai samu damar duba marasa lafiya a yammacin ranar ba.

Wani hadimin gwamnan Jihar Jigawa, Suleiman Harbo, wanda ya kai mahaifiyarsa asibitin domin ganin likita, shi ne ya bayyana yadda lamarin ya faru.

Harbo, ya ce sun isa asibitin da misalin ƙarfe 5 na yamma, inda aka sanar da su cewa likitan da aka tsara ba zai zo ba.

Daga nan aka kira Dokta Kbrahim domin ya maye gurbinsa.

Ya ce aƙalla marasa lafiya shida, waɗanda yawancin su masu shekaru sama da 80 ne suke jira zuwan likitan.

Bayan ya tambayi ma’aikatan asibitin dalilin jinkirin, aka kira Dokta Ibrahim ta waya, inda ya ce zai zo bayan sallar Magariba.

Bayan isarsa asibitin, Dokta Ibrahim ya fara jin jiri bayan ya fito daga motarsa wanda nan take ya faɗi.

Nan take aka garzaya da shi sashen gaggawa, inda likitoci suka yi ƙoƙarin ceto rayuwarsa, amma bayan minti 15 aka tabbatar da rasuwarsa.

Harbo, ya ce lamarin ya girgiza marasa lafiyar da ke jiran ganin likitan da kuma ma’aikatan asibitin.

Ya ce manyan likitocin da suka yi ƙoƙarin ceton rayuwarsa sun kasa ɓoye alhininsu.

Harbo ya ce da mahaifiyarsa ta samu labarin rasuwar likitan sai ta yi masa addu’a tare da cewa: “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Allah Ya jiƙansa. Mu koma gida, ni riga na warke.”

Harbo ya ƙara da cewa mutanen da suka kasance da Dokta Ibrahim a lokacin da lamarin ya faru sun dinga furta kalmar “La ilaha illallah” kafin rasuwarsa.

Har zuwa yanzu, ba a bayyana musabbabin  rasuwar likitan ba.