Yadda likita ya yi wa mara lafiya fyade a asibiti

Ana zargin likitan ya yi wa mara lafiyar, wadda kwararriyar ma’aikaciyar jinya ce, allurar kashe kuzari, sannan ya yi mata fyade.

Yadda likita ya yi wa mara lafiya fyade a asibiti

An zargin shugaban wani asibitin da ke Ilori a Jihar Kwara da yi wa wata mara lafiya fyade a lokacin da ta je duba lafiyarta.

’Yan sanda sun bayyana wa kotu cewa Dokta Ayodele, ya yi wa mara lafiyar, wadda kwararriyar ma’aikaciyar jinya ce, allurar kashe kuzari, sannan ya yi mata fyade.

“A yayin bincike an gano bidiyon fyaden da ya yi, sannan gwajin asibiti ya tabbatar cewa an yi wa wadda ke karan fyade,” in ji takardar cajin da aka gabatar wa kotun.

Dan sanda mai gabatar da kara, Gbenga Ayeni, ya ja hankalin kotun cewa likitan, wanda ya shekara 27 yana aiki, ya aikata laifuka masu girma na fyade da kuma rashin dattaku, don haka ya kamata a tsare shi.

A kan haka ne alkalin kotun majistare, Gbadeyan Jumoke Kamson, ya anince a tsare likitan sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Mayu da muke ciki.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan