Yadda Likitan ’Yar-tsana ke dora masu karaya
Wani mutumin kasar Ajentina a birnin Buenos Aires mai shekaru 52 ya bude asibitin gyaran ’yar tsana, a wannan zamanin da ake zubar da kayayyakin da suka lallace. Mutumin mai suna Julio Roldan ana yi masa lakabi da “Likitan ’Yar tsana.” Roldan ya bayyana wa manema labarai cewa wannan aiki nasa daidai yake da na […]
Wani mutumin kasar Ajentina a birnin Buenos Aires mai shekaru 52 ya bude asibitin gyaran ’yar tsana, a wannan zamanin da ake zubar da kayayyakin da suka lallace. Mutumin mai suna Julio Roldan ana yi masa lakabi da “Likitan ’Yar tsana.”
Roldan ya bayyana wa manema labarai cewa wannan aiki nasa daidai yake da na likitoci da masu dorin karaya, in an yi la’akari da yadda yake taimaka wa majiyatansa su “farfado,” baya ma ga farfadowar suna ma kara zama abin kauna ga masu su.
Na gaji wannan sana’ar ne daga marigayi mahaifina. Mafi yawan ’yar tsanar da aka yi ta tangaran da na gyara shekarun yakanm kama daga 80 zuwa 130, wadanda asalinsu a kasashen faransa da Jamus aka kera su,” inji Roldan.