Yadda likitoci 400 suka fadi jarrabawa a Najeriya
A cikin wani rahoto da gidan rediyon BBC ya fitar, ya nuna cewa sama da mutum 400 daga cikin ‘yan Najeriya 680 da suka karanta aikin likita a jami’o’in kasashen waje ne suka fadi jarrabawar tantance likitoci ta Najeriya. Sai dai kuma wadanda suka fadi jarrabawar sun ce babu adalci a jarrabarwar, inda suka yi […]

A cikin wani rahoto da gidan rediyon BBC ya fitar, ya nuna cewa sama da mutum 400 daga cikin ‘yan Najeriya 680 da suka karanta aikin likita a jami’o’in kasashen waje ne suka fadi jarrabawar tantance likitoci ta Najeriya.
Sai dai kuma wadanda suka fadi jarrabawar sun ce babu adalci a jarrabarwar, inda suka yi zargin cewa kyashin karatun da suka yi a kasashen wajen ne ya sa aka kayar da su.
daliban da suka yi karatun likitanci a jami’o’in kasashen wajen sun garzaya zauren Majalisar Dattawa domin su nemi ‘yan majalisar su bi musu kadi kan zargin da suke yi cewa an kayar da su ne a jarrabawar tantance likitoci ta Najeriya.
daliban sun dauki lokaci suna muhawara a tsakaninsu game da yadda ya kamata su bullo wa matsalar domin samun nasara. Haka gidan rediyon ya tuntubi wani daga cikin iyayen dalibai likitocin da suka fadi jarabawar, Malam Muhammad Bala Jibrin don jin yadda suka ji bisa faduwar.
Sai ya ce “Na taba yin aikin Kwamishinan ilimi a Jihar Bauchi kuma kafin gwamnatin jihar ta kai yara karatu a kasar wajen, sai da suka dauki shugaban hukumar MDCN mai tantance likitoci na wancan lokacin zuwa kasar Masar, domin ya amince da yadda ake koyar da aikin likitanci a jami’o’in da za su kai daliban.”
Ya kuma kara da cewa hukumar MDCN ta amince da yadda ake koyar da aikin likitanci a jami’o’in tare da amincewa da yadda za a yi aikin likitocin a kasar Masar.
Haka kuma daya daga cikin daliban da suka fadi jarabawar, Dokta Bashir Isa, ya yi zargin cewa an kayar da su ne ba bisa ka’ida ba. Ya ce, “Ai wannan faduwar magana ce kawai. Ta ya ya za a ce mutum kusan 700 sun rubuta jarrabawa, kuma wajen mutum 400 da wani abu su suka fadi jarrabawar? Ya kamata a yi tambaya. Na farko dai ka sani wannan jarrabawar tana da sauki ta yadda duk wannan saukin nata kuma aka zo aka ce mun fadi”
Likitocin da suka fadi jarrabawar dai sun yi zargin cewa ana aikata ba daidai ba a jarrabawar tantance likitocin. “Sannan inda suke cewa mun fadin, shi ya fi ko wane bangare sauki a koyarwar likitanci, shi ne ka zo ka yi abu a fili a gani sabanin wani in kace ka tambaye shi ilimi a kwakwalwarsa zai sha wuya kafin ya gaya ma.”
Faduwa jarabawar ta dalibai likitocin har sama da 400 dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fama da karancin likitoci tare da tabarbarewar harkokin lafiya a dukkan sassan kasar.