Yadda likitoci suka ceci kunkuru mai shekara 79 a Sakkwato
Daga wata jiha sai da aka kai dattijon kunkurin asibitin koyarwa aka iya ceto ransa
Likitocin Dabbobi a Jihar Sokoto sun ceci rayuwar wani kunkuru mai shekara 79 da mota ta taka a garin Argungun na jihar Kebbi har ta tarwatsa kwaryar bayansa.
Dattijon kunkurun wanda mallakin mahaifin Jarman Argungu ne, Alhaji Suleiman Jarma, an ce a halin yanzu yana samun sauki.
- Ya kashe agola don amarya ta so shi
- Mata ta kashe aurenta saboda zargin miji da daukar mata dan kamafai
- Za a fara dandake masu yin fyade a Jihar Kaduna
Dakta Nura Abubakar, wanda ya jagoranci yi wa kunkuru tiyatar gaggawa ya ce sai da aka fara kai shi Asibitin Dabbobin garin Argungu kafin abun ya ci tura aka turo su Sakkwato.
“Raunin da aka ji wa kunkurun na iya sanadiyyar mutuwarsa, kuma yana bukatar a gaggauta yi masa tiyata.
Ya ce kwaryar bayan kunkurun ta fashe a lokacin da aka kawo shi, “Nan da nan muka hada wadanda za su yi masa aiki daga Asibitin Dabbobin Jami’ar Usmanu Danfodio aka farfado da shi”, inji likitan.
Sadiq Suleiman, shi ya taka kunkurun da mota, kuma ya ce mahaifinsa ya gaji dabban ne daga wurin kakansa.
– Yadda abin ya faru –
Da ya ke bayanin yadda abun ya faru, Sadiq ya shaida wa wakilinmu a waya cewar yana sauri ne zai fita da mota bai san kunkurun na bayansa ba ya taka shi.
“Ina sauri ne inje wajen wani alkawarin da na yi, na yi ribas kansa, har kwaryar bayansa ta fashe.
“Na yi sauri na kai shi asibitin Dabbobi Argungun su kuma suka ce a zo da shi Sakkwato.
“Mun gode Allah da aka dinke kwaryar bayansa. Inda babu kwaryar sun yi amfani da wani abu mai kwari suka rife shi.
“Yanzu haka yana samun sauki sosai. Maganar da nake yi da kai ga shi nan yana wasa da yara”, inji Sadiq.
Ya kuma ce nauyin kunkurun zai kai buhun siminti daya, “ba na iya daukar sa sai dan uwana ya taimake ni”.
Ya ce, kunkurun na kakansa ne kafin mahaifinsa ya gaje shi bayan rasuwar kakansa.
“Kunkurun zai cika shekara 80 idan watan fabrailun 2021 ya kama”, in ji Sadiq.