Yadda littafaina uku suka  ci gasar rubutu – Mahmud Bambale

A yau mun leka Kamfanin Wallafa Littafai na Najeriya ta Arewa (NNPC) da ke Zariya ne inda Manajan Kamfanin Malam Mahmud Barau Bambale, ya yi bayani kan adabi da ci gaban da ake samu da bambancin littattafan baya da na yanzu da kuma yadda littattafansa uku suka ci gasar rubutu a baya: Kamfanin NNPC an […]

Yadda littafaina uku suka  ci gasar rubutu – Mahmud Bambale

A yau mun leka Kamfanin Wallafa Littafai na Najeriya ta Arewa (NNPC) da ke Zariya ne inda Manajan Kamfanin Malam Mahmud Barau Bambale, ya yi bayani kan adabi da ci gaban da ake samu da bambancin littattafan baya da na yanzu da kuma yadda littattafansa uku suka ci gasar rubutu a baya:

Kamfanin NNPC an samar da shi ne a zamanin Turawan mulkin mallaka a 1939 inda ya rika buga jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, daga baya a 1966 ya koma mallakar Jihar Arewa, aka kira shi da Kamfanin Wallafa Littattafai na Arewacin Najeriya (NNPC).

Kamfanin ya wallafa littattafai da dama kamar su Magana Jari Ce Littafi na 1 zuwa na 3 wanda marigayi Alhaji Abubakar Imam, ya wallafa. Da Tafiya Mabudin Ilimi da Iliya Dan Maikarfi da Ruwan Bagaja. da Gandoki na Walin Katsina, Alhaji Bello. Saura sun hada da littattafan; Wasannin Tashe na Muhammad Belle Muhamud da Da’u Fataken Dare da Malam Tanko Zango ya rubuta. Da littafin wakokin Infiraji da Tsarabar Madina na Dokta Aliyu Na Mangi. da Duniya Ina Za Ki Da Mu na Malam Na’ibi Sulaiman Wali da Bala da Babiya na marigayi Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki. Sannan akwai littafin, Bora da Mowa na Umar Balarabe Ahmed da Zaman Mutum da Sana’arsa da Muguwar Kishiya. Da littafin Gan Doki na. Sai kuma bangaren littattafan soyayya akwai irin su So Aljannar Duniya da sauran littafai da dama.

Malam Mahmud Barau Bambale  ya ce, “Adabi ya kasu kashi biyu, akwai Rubutaccen Adabi akwai kuma Adabin Baka. Rubutaccen Adabi shi ne wanda ya kunshi duk abin da aka rubuta aka wallafa, ko na wasan kwaikwayo, ko kuma wake.

Adabin Baka kuma ya kunshi wakoki irin wadanda su Alhaji Mamman Shata da sauransu suke yi. Duk da daliban nazari a wannan fage sukan rubuta su, amma su wadanda suka yi su na asali ba su rubutawa suna yin wakokinsu ne da ka.”

Ya ce shi kansa ya rubuta littattafai inda ya ce: “Na fara rubuta littafi ne a 1983 a lokacin ina ajin karshe na Makarantar Share-Fagen Shiga Jami’a, littafina mai suna, Komai Nisan Dare, rubutun zube ne. Cikin karin magana Malam Bahaushe ya ce komai Nisan Dare Gari Zai Waye.

Littafina ne ya ci gasar kagaggun labarai a gasar rubuce-rubucen littafai na harsunan jihohin Arewa da aka yi a 1989 aka kammala a1990 a Hotel din Daba da ke Kaduna zamanin Gwamna Abdullahi Sarki Muktar. Kuma manyan shaihunan malamai masana Adabi suka zama alkalai a gasar.  Kuma an shirya gasar ce saboda a zamanantar da rubuce- rubacen Adabi. Littafina mai suna Komai Nisan Dare ya zo na daya a gasar, na gina lattafin ne a kan soyayya.”

Tsokaci a kan littafin

Da yake tsokaci kan littafin nasa, Bambale ya ce: “Soyayya dai ruwan zuma ce, an kuma ce idan ka sha ka ba masoyi. Binta da ta sha ta ba Tanimu don haka ne ma aure ya tabbata a tsakaninsu, amma fa sai da Tsigarallahu ta riga ta.

Rashin da’a da zafin kishi tare da mugun nufi ya jefa Tsigarallahu cikin matsananciyar rayuwa wadda ta kai ta ga zuwa wajen bokaye daban-daban domin neman biyan wasu bukatu.

Allah Ya biya wata bukatar, amma wata bukatar da ta leko sai ta koma.Jiki dai an ce magayi ne, baki kuwa mafadi. Kasancewar mugunta fitsarin fako ce ta sa miyagun manufofin Tsigarallahu na hallaka abokiyar zamanta sun koma mata. Sakamakon haka ’ya’yanta suka kaurace mata mijinta ya sake ta, sannan daga karshe ta haukace.

Allah Gatan bayinSa, Salihu kuma ta wani bangaren, gatan Tsigarallahu, domin shi ya tsinto ta, ya taimake ta a lokacin da ta rasa mai taimakonta.

Ashe dai gaskiyar masu iya magana da suka ce Komai Nisan Dare Gari Zai Waye!” Tabbas, gari ya waye wa Tsigarallahu kaico!

Da ya koma kan littafinsa na biyu mai suna Kowa Ya Bar Gida; Bambale ya ce:

“Ja’e Al’amin ya tashi tun yana dan karami cikin maraici. Don haka kawunsa ya rungume shi hannu bibbiyu da kyautatawa, ya hada shi da ’ya’yansa ya tarbiyantar da su.

Haduwa da abokin banza, Bubuga Liman, dan masu sukuni ta canja rayuwar Ja’e wanda har ta kai shi ga wuce makadi da rawa, ya rika raina iyayensa da asalinsa. A maimakonsu sai ya rika sha’awar Turawa da dabi’unsu.

Al’amarinsa ya yi kamari a yayin da ya shiga cikin kungiyar masu fataucin haramtattun miyagun kwayoyi da Hodar Iblis.

Matsanancin son auren Tina, Baturiyar Amuruka da makantacciyar son dukiya sun kai Ja’e sun baro domin sun yi sanadiyar kashe babban abokinsa, Babuga, domin gudun kada ya soki lamarin aurensa da Tina.

Ruwa ya kare wa dan kada ne a yayin da aka kama shi,  aka daure. Tina kuma ta yashe  shi karkaf! Ya koma ba shi ga tsuntsu ba shi ga tarko. Kaico! Ashe dai gaskiyar masu iya magana ne da suka ce, kowa ya bar gida, gida ya bar shi!

Da ya koma kan littafinsa na uku mai suna Kukan Kurciya Bambale ya ce shi kuma gasa ce aka shirya a kan yadda za a mika mulki a hannun farar hula wanda Gwamnatin Jihar Kaduna ta wancan lokacin ta shirya, “Sai na rubuta wannan littafi na aika da shi inda na wakilci Karamar Hukumar Zariya, kuma aka yi sa’a littafin ya zo na daya,” inji shi.

Malam Mahmud wanda gogaggen ma’aikacin gwamnati ne da ya rike manyan mukamai, inda daga baya ya yi ritaya, ya ce kudirin Gwamnatin Tarayya na kafa mulkin dimokuradiyya mai dorewa ya sa jama’a suka hada kai, suka nufo shi kan ya shiga siyasa, amma sai ya noke saboda rashin kwadayin mulki da juyayin rashin sukunin da zai fuskanta. Sai dai kuma jama’a sun ki amincewa da uzurinsa, suka nuna masa shi suke so don haka dole ya amince da bukatarsu.

Ya ce littattafan nasa uku hukumomin jarrabawa kammala sakandare sun amince da su kuma suna amfani da su a manhajarsu kamar Hukumar Jarrabawar ta Kasa (NECO) da Hukumar Jarrabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) da kuma Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), kuma akwai manyan makarantun kasar nan da suke amfani da su.

 

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato