Yadda ma’aikaci zai kashe mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 70 a Nijeriya

Ko da ma’aikaci ne ya kamata ya samu wata sana’a a gefe don ƙarin samun kuɗi.

Yadda ma’aikaci zai kashe mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 70 a Nijeriya

A ranar Litinin da ta gabata ce Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannun kan dokar fara biyan Naira 70,000 a matsayin albashi mafi ƙaranci ga ma’aikata a Nijeriya.

Shugaban ya rattaba hannun ne a lokacin taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC), wanda Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da sauran jagoroin ɓangaren majalisa suka halarta a Fadar Shugaban Ƙasa.

Wasu na ganin amincewa da fara biyan sabon albashi bai rasa nasaba da ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na ɗaukar wasu matakai domin daƙile zangazangar matasa.

Aminiya ta ruwaito yadda a ranar Litinin ɗin, kafin sa hannun Shugaban Ƙasan, wasu matasa a Jihar Neja suka fara zanga-zanga kan halin da ƙasar ke ciki.

Masu zanga-zangar sun riƙa rera waƙoƙin nuna adawa da gwamnati a yayin da suke tattaki a kan tituna a hanyar Abuja zuwa Kaduna, kafin ’yan sanda suka je tabbatar da kwanciyar hankali a wajen.

Aminiya ta ruwaito a makon jiya cewa, Majalisar ƙasar ta gaggauta zartar da ƙuduri dokar mafi ƙarancin albashin ta shekarar 2024.

Ƙudurin wanda aka yi masa karatu na biyu da na uku a dukkanin majalisun guda biyu, inda cikin ƙanƙanin lokaci suka amince da shi.

Ƙungiyar Ƙwadago da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu sun cim ma yarjejeniya a kan mafi ƙarancin albashi a ranar Alhamis 18 ga Yuli, 2024 bayan ɗaukar makonni ana musayar yawu tsakanin Gwamnatin Tarayya da kuma ƙungiyoyin ƙwadago, waɗanda tunda farko suka kafe cewa sai mafi ƙarancin albashi ya zama Naira dubu 615 ko kuma Naira dubu 250.

Abubuwan da za a iya saya da Naira 70,000 a Nijeriya

A yanzu haka tashin farashin kayayyaki yana ƙara gaba, inda ya kai kimanin kashi 34.2. A watan Yuni abin ya kai 200% kimanin kashi 11.40 da aka samu a 2019, lokacin da aka yi mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 30.

Aminiya ta karkasa yadda za a iya amfani da sabon mafi ƙarancin albashi, ma’ana abin da za su iya saya wa mutum.

An gudanar da wannan bincike ne a kan wasu ma’aikata a Kano da Legas da kuma Abuja.

Haka kuma nazarin zai ƙunshi irin abubuwan da mutum zai kashe kuɗin a kan abubuwan da suka zama dole ga rayuwar bil’adama da suka haɗa da abinci da tufafi da hayar gida da kuɗin zirgazirga da biyan kuɗin wutar lantarki da sauran abubuwa da suka zama wajibi irin su kuɗin wankin tufafi da sauransu.

Lissafi ne da aka yi a kan ma’aikacin da ba shi da wani mutum a ƙarƙashinsa.

Ma’aikatan Legas

A tattaunawar ɗaya daga cikin wakilanmu da wasu daga cikin ma’aikata a Legas da suke kan matakin albashin Naira 70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, sun bayyana cewa, suna kashe Naira 2,000 a kullum a matsayin kuɗin abinci, ci uku wanda wata ranar suke tsallake wani cin ma, inda in ka haɗa zai ba da dubu 60 a wata.

Wannan ya nuna cewa, ma’aikata a Lagos suna kashe kaso 90% cikin ɗari na albashinsu a kan abinci da kai komo.

Wasu daga cikin ma’aikata sun bayyana wa Aminiya cewa, suna kashe Naira 600 zuwa 1,500 a matsayin kuɗin mota,wanda ya danganta da nisan wurin ayyukansu.

A ƙiyasi, Naira dubu ɗaya a kullum, ma’aikaci yana kashe 20,000 a kan sufuri a kowane wata.

Game da batun gidan haya kuwa, gidan da yake ɗauke da ɗakin kwana da ɗakin girki da ban ɗaki a ciki, ana biyan Naira 120,000 zuwa 350,000 a duk shekara a mafi sassan Legas da ke iyaka da jihar Ogun. Kusan 180,000 ke nan ma’aikaci ke biya 15,000 a matsayin kuɗin haya duk wata.

Wani ma’aikaci wanda yake aiki a ɗaya daga cikin ma’aikatun Legas, ya bayyana sunansa a matsayin Sola, inda ya bayyana wa Aminiya cewa:

“Idan kuma kana rayuwa ne a ɓangaren ’yan ajin farko Band A, za ka biya Naira 10, 000 ne na wuta.

“Ba tare da la’akari da matsayin abin da ake cire maka ba, mafi ƙarancin abin da suke biya shi ne Naira dubu 4,000 a duk wata.”

Shi kuwa Josephine Alabi, wanda mai shara ne a wani shakatafin asibiti a jihar ya ce: “Ɓangaren suttura da takalmi, mafi ƙarancin abin da za ka kashe a shekara ba zai gaza Naira 30,000, kuma mafi yawancin lokuta kayan na gwanjo ne”.

Wannan ya nuna cewa ma’aikata kamar Alabi suna kashe kimanin Naira 2,500 a sayan kaya da takalmi a kowane wata.

Alabi da sauran makamantanta sun bayyana wa Aminiya cewa, suna kashe Naira 5,000 gurin yin aski da kitso da wanki da man goge haƙori da sabulun wanka da sauran ƙananun abubuwan buƙatar yau da kullum.

A tattaunawar da wakilanmu ya tattara ya gano cewa, ƙaramin ma’aikaci a Legas yana buƙatar kimanin Naira 106, 500 domin ya biyan buƙatunsa na wata.

Amma da Naira 70,000 ɗin da ake ƙoƙarin fara biyan sa, zai iya kawai sayan abinci ne, tare da fafutukar biyan kuɗin sufuri da kuma kuɗin lantarki da sauran ƙanana da manyan buƙatun yau da gobe.

Naira dubu 70,000 ba za ta iya wadatarwa ba a Babban Birnin Tarayyar

A wata tattaunawa ta daban da Aminiya, ma’aikata a Babban Birnin Tarayyar ƙasar sun ce sabon mafi ƙarancin albashin ba zai taɓa gamsar da yanayin da ake ciki na tattalin arziki ba.

Bello Yunusa, wanda yake rayuwa a wani fallen ɗaki a wani gida a Kubwa da ke Abuja, ya ce, mafi ƙarancin albashin ya kamata a ce ya kai Naira 150,000.

Yunusa, wanda yake aiki a matsayin mai gadi a wani banki da ke a cikin garin Abuja ya ce, kuɗin hayarsa ya ƙaru daga dubu 60,000 zuwa dubu 90,000 a duk shekara.

Ya ce, “gaskiya ba wani ɗan Nijeriya da zai iya rayuwa da Naira 70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a wannan yanayi na tsadar rayuwa da ake ciki.

“Ina kashe mafi ƙarancin Naira dubu 2,000 a matsayin kuɗin motar zuwa wajen aiki a kullum, wanda in ka lissafa a mako zai ba ka Naira dubu 10, ka ga ya zama Naira 40,000 kuma a wata.”

Ya ƙara da cewa, a kuɗin abinci kuma ina kashe 3,000 a kullum, Naira 90,000 ke nan a wata.

“Saboda faranti ɗaya da nake saya daga gamagarin wurin sayar da abinci yana kaiwa Naira 1,500 zuwa sama.

“Kuɗin wutana kuwa a duk wata ina biyan Naira.1,400. Ina ajiye dubu 80,000 aƙalla kuɗin kayan sawa da takalmi a duk sheakara, kusan 6,600 a duk wata.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa yake wuya ga ƙaramin ma’aikaci kamar ni ya iya rayuwa a Abuja da sabon mafi ƙarancin albashi.

“Har yanzu dai bai isa a ce ya wadatar, ta yadda mutum zai iya rayuwa a wannan yanayin na tsadar rayuwa ba. Saboda haka Ƙungiyar Ƙwadago dole su dage a kan neman ƙari.”

Yadda ma’aikaci zai kashe mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 70 a Nijeriya

Wani mai ƙaramin ƙarfi mai suna Abiodun Michael ya ce, inda ya fi kashe kuɗi shi ne biyan kuɗin motar zuwa aiki da dawowa.

Ya ƙara da cewa, ya dogara ne da shugabanninsa da abokai da ’yan uwa wajen rayu.

Michael ya ƙara da cewa, “Shin wannan ƙarin mafi ƙarancin albashi zai tsai da ƙarin kuɗin abinci da sauransu?”

Ma’aikaci a Kano yana buƙatar Naira 72,900 ne a wata

Binkicen wakilinmu ya nuna cewa, ƙaramin ma’aikaci a Kano yana kashe Naira 1,500 a kan abinci a kullum ci uku (500 duk ci ɗaya), wanda zai ba ka Naira 45,000 a wata.

Kuɗin mota gurin zuwa da dawowa kuma yana iya kashe Naira 600 wato Naira 12, 000 a wata.

Yayin da kuma kuɗin hayar ɗaki ya kama daga Naira 50,000 (4,166 duk wata) ko kuma 150,000 (12,500 a wata) ya danganta da wuri a mafi ƙarancin N100,000 (N 8,300) duk shekara.

Haka kuma kuɗin wuta yakan kai Naira 2,500 da 6,500.

“Kuɗin sabulu da na man goge baki da man shafawa da sabulun wanki da ruwan sha da na aikin gida da sauransu, ina kashe kimanin Naira 6,500 a duk wata.”

Abdullahi Idris ya ce, idan ka zama mai tsantseni, shi ne za ka sai kaya kala uku a shekara a kan kimanin kuɗi Naira 8, 000 duk kala ɗaya da kuma kala biyu na takalmi a kan Naira 4,000 duk ɗaya. Gaba ɗaya ya kama Naira 32,000 (2,600 duk wata).

A ɗaya ɓangaren, matsaikacin ma’aikaci a Kano yana buƙatar N 77,900 a kowane wata a rayuwarsa shi kaɗai ba tare da ya ɗauki nauyin mata ko ɗa ko wani ba.

Mutanen da ba sa ɗaukar albashi

Haka kuma a nazarin da Aminiya ta gudanar game da mutane masu ƙaramin ƙarfi, waɗanda ba su yin aikin albashi ya nuna cewa, mafi yawansu suna rayuwa ce a kan ƙasa da Naira dubu 70.

Wani mai sayar da ruwa mai suna Lawwali Maga ya bayyana cewa, a kullum daga safiya zuwa yamma ba ya samun kuɗin da ya wuce Naira dubu biyu.

“Kamar yadda kike gani ita wannan kurar tana ɗaukar jarkoki 10. Ina sayar da ruwa a kan Naira 50.

“Idan na cika ta, ina biyan Naira 200 na masu ruwan.

“ A yanzu da yake damuna ta zo babu cinikin ruwa sosai bai fi in yi sawu biyu zuwa uku ba. Idan na sayar shi ne nake iya haɗa Naira 1500.

“A ciki zan ci abincin sau uku. Zan biya kuɗin zagawa banɗaki da sauran buƙatun yau da gobe.”

Shi ma wani mai sayar da gawayi mai suna Abdullahi Adamu ya bayyana cewa, idan ba kasuwa ya samu ba a kullum ba ya sayar da gawayi da ya wuce buhu guda, wanda kuma kuɗinsa bai wuce Naira dubu shida ba.

“Idan na sayar da buhu ɗaya nakan samu ribar Naira 500. Idan kuma na sayar da shi da kaɗan-kaɗan nakan sami kimanin Naira 800.

“Da wannan kuɗin ne zan yi buƙatuna na yau da gobe. Abinci daman garaugarau nake saya, na ci irin su dambu ko shinkafa da wake, inda nakan samu a zuba min na Naira 200 zuwa 300.”

Shi kuwa Malam Ismaila Muhammad wani mai wankin takalmi ya bayyana cewa, a kullum ba ya samun abin da ya wuce Naira 150, wanda idan ka lissafa bai wuce Naira dubu 45 a wata ba.

“A kullum tsakanin wankin takalmi da gyaran takalmi nakan ɗan samu abin da bai wuce Naira dubu ɗaya wani lokacin ma yana fin haka.

“A cikin wannan kuɗi da shi nake yin komai na rayuwata. Idan aka samu na ci abinci garau-garau an gode wa Allah a rana. Idan kuma ba a samu ba sai a rage cin abinci. A maimakon a ci sau uku, sai a ci sau biyu.

“Dama batun hawa mota don zuwa nan ba a yin sa a kullum, da ƙafata nake zuwa kasuwa, na koma gida. Domin idan na ce zan hau mota to fa abin ba zai yi min kyau ba.

“Mu dai Allah ne kaɗai yake riƙe da mu ba wai abin da muke samu ba. Domin idan ka kwatantana abin da kake samu da abin da kake kashewa ka san akwai bambanci.

To shi ya sa a kullum sai dai mutum ya gode wa Allah. Abin da ya zama dole shi mutum ya yi wato cin abinci. Sayen sutura kuwa tuni na ajiye shi. Domin a yanzu kuɗin bai samuwa ballantana mutum ya ɗauka ya sayi tufafi. Sai dai idan wani ya cire daga jikinsa ya ba ni,” inji shi.

Dukkanin mutanen da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana fargabarsu game da yadda farashin kayayyaki ke tashin gwaron zabo a kullum, lamarin da yake ƙwarewa a kan mai ƙaramin ƙarfi.

Abdulnasir Turawa Yola malami ne a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Jigawa, ya bayyana cewa mafi ƙarancin albashin da ake magana ba abu ne da zai ishi talaka ba ko da kuwa a kan kansa ne ballantana mai iyali.

“Idan kuka lura da wannan kuɗi da ake magana na Naira dubu 70 ko da an fara bayarwa ba zai ishi ƙaramin ma’aikaci wajen gudanar da rayuwarsa ba.

“Da babban ma’aikaci da ƙarami duk kasuwa ɗaya suke zuwa sayen kayayyaki.

“Haka kuma a wasu lokutan za ka samu mutanen nan suna da ’ya’ya da mata da ke ƙarƙashinsu waɗanda su ma suna da nasu buƙatun a wajensu. Haka kuma duk a cikin wannan kuɗin za a yi su.

“Kai kanka idan ka ɗauki Naira dubu 70 ka san cewa ba za ta ishi mai iyali rayuwa a wata ba. Sai dai kawai a yi maleji.”

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar wa ’yan Nijeriya mafita a kan hauhawar farashi kayayyaki da ake fama da shi a ƙasar nan, ta hanyar fito da sabbin tsare-tsaren da za su kawo rangwame a rayuwar alummar ƙasar.

Haka kuma ya yi kira ga al’umma da su sake nema wa kansu wasu sana’o’i na daban da za su ƙara a kan waɗanda suke yi don samun ƙarin kuɗin shiga wanda zai zama ya ishe su yin amfanin yau da gobe.

“Ko da ma’aikaci ne ya kamata ya samu wata sana’a a gefe don ƙarin samun kuɗin shiga da mutum zai gudanar da rayuwarsa.”

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta

Jerin Manyan Dambarwan Kano a 2024