Yadda ma’aikatan gwamnati ke satar kudade ta Asusun TSA
Dabarun da jami’an gwamnati suka bullo da su domin sace kudade a karkashin tsarin TSA.
Shekara shida bayan fara amfani da Asusun Bai-Daya na Gwamnatin Tarayya (TSA) da nufin toshe hayoyin da barayin gwamnati suke sace kudadenta, binciken Aminiya ya gano yadda har yanzu ake ci gaba da yin ruf da ciki a kan kudaden.
A ranar 7 ga Agusta, 2015 ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci daukacin Hukumomi da Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya su rika sanya duk kudaden shigarsu da haraji da dangoginsu a asusun TSA.
- Babban taro: Rikici ya yi awon gaba da kujerar shugaban kungiyar Gwamnonin APC
- N100m muka biya kudin fansa a kauyenmu —Al’ummar Nahuche
Bisa umarnin na Buhari, za a rika sanya duk kudaden hukumomi da ma’aikatun gwamnati a asusunta na musamman da ke Babban Bankin Najeriya (CBN), sai wanda gwamnati ta ba da izinin yin sabanin hakan.
Ya ce TSA asusu ne da zai tattare kudaden da gwamnati ke da su a wuri daya, kuma an yi hakan ne domin tabbatar da yin komai a fili kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Fara amfani da TSA
An fara amfani da TSA a 2015 ne bayan hawa mulkin Buhri da nufin magance matsaloli da kuma inganta tsarin gudanar da kudaden gwamnati, bisa shawarar da Bankin Duniya ya bayar a 2004 kan habaka tattalin arzikin Najeriya.
Gabanin fara amfani da TSA din, hukumomi da ma’aikatu gwamnati kan yi amfani da asusun banki fiye da guda daya, inda shugabanninsu suke juya akalarsu yadda suka ga dama da kuma a matsayin hanyar satar kudaden shigar gwamnatin da suke tarawa.
Hakan ya sa a wancan lokaci hukumomin yaki da rashawa da masu binciken kudade ba sa iya bankado wasu badakalar kudaden gwamnati yadda ya kama.
Amma wadanda suka bullo da TSA suna ganin idan har aka aiwatar da shi yadda ya kamata, zai toshe hanyoyin zurarewawr kudaden gwamnati tare da tabbatar da yin komai a fili da taimaka wa gwamnati wajen bibiyar hanyoyin da ake sace kudaden shigarta domin ta samu ta inganta raywuar talakawa.
Tsugene ba ta kare ba
Wasu jami’an gwamnati da muka tattauna da su tabbatar mana a asirce (saboda ba su da izinin magana) cewa duk da kyakkyawar manufar ta TSA, har yanzu ba ta toshe hanyoyin da ake sace kudaden gwamnati ba; Hasali ma, makudan kudadan kudade ake sacewa a yanzu.
Jami’an gwamantin sun bayyana mana a asirce cewa bayan bullo da TSA, shguabannin hukumomin gwamnati sun koma amfani da damar kashe kudaden gwamnati wajen yin satarsu.
Wakilinmu ya gano yadda shugabannin hukumomin suke kauce wa TSA ta hanyar bayar da izinin sanya kudaden aikin da aka yi wa hukumominsu a asusun wani jami’in gwamanti, maimakon biyan wanda ya yi aikin kai-tsaye.
“Akwai jami’an gwamanti da asusun bankinsu ke da rajistar GIFMISS ta biyan kudade da gwamnati ta amince.
“Ana amfani da su a sanya kudaden da aka karbo daga asusun gwamanti domin biyan kudaden ayyukan da aka yi wa hukumomi da ma’aikatun gwamnati,” inji daya daga cikinsu.
Ya ce hakan ya bude wata sabuwar kofar cuwa-cuwa inda jami’an gwamnati kan kara kudadena aikin; Saboda haka babu wani abin a-zo-a-gani da TSA ya yi wajen inganta tsarin gudanar da kudaden gwamnati ko tabbatar da gaskiya.
“Abin da yake yi kawai shi ne tattara kudaden shigar gwamanti, amma kudaden da take kashewa kuma rashawa ta yi musu kututu,” inji wata majiyar.
Waji jami’i a Ofishin Akanta-Janar na Tarayya, wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sun gano cuwa-cuwa da kuma yadda ake hada baki da wasu daraktoci da manyan sakatori a ma’aikatun gwamnati wajen yi wa TSA danwaken zagaye.
Ya ce, in banda wasu manyan sayayya da harkoki, yawancin kudaden da hukumomi da ma’aikatun suke biya, turawa ake yi zuwa asusun kashin kan wasu jami’an gwamnati.
Hakan ya sa suke samun saukin kara yawan kudaden, su kuma cire su yi amfani da su, da zarar an samu takardar izinin fitar da kudaden.
A cewarsa, wasu manyan jami’an gwamnati na da masaniyar hakan, amma ba su da kwarin gwiwar dakatarwa.
Abin da gwamnati ta yi
Aminiya ta gano cewa bayan bankado wannan harkallar ce ta sa Gwamnatin Tarayya ta sake kaddamar da Kwamitin Tabbatar da Sake Aiwatar da Amfani da Tsarin TSA.
Kwamitin, wanda Ministar Kudi, Zainab Ahmed ke jagoranta da kuma Akanta-Janar na Tarayya a matsayin mataimaki, da kuma Daraktan TSA a Ofishin Akanta-Janar na Tarayya a matsayin sakatare sai kuma Kwamitin Daraktocin TSA da na Kwamitin Ministoci kan Aiwatar da Tsarin TSA.
Sauran sun hada da Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kan Ayyuka, Daraktan Ofishin Kula da Basuka na Kasa, wakilan Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS), Babban Jami’in Kudin NNPC, Daraktan TSA a Ofishin Akanta-Janar na Tarayya da Darakta-Janar din Hukumar Gyare-gyare a Aikin Gwamnati da sauranasu.
Aikin kwamitin ya hada da samar da tsarin aiwatar da TSA, karbar rahoton kwamitin aiwatar da TSA, bayar da shawarwari a kan rahoton.
Matsalolin TSA
A lokacin kaddamar da kwamiatin, Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta ce tsarin TSA ya yi rawar gani wajen kara yawan kudaden shigar gwamnati.
Ta ce, “Saboda amfani da TSA, tuni muka koma cirar kudaden da suka dace daga hukumomi akalla 16 nan take, a watannin da ke tafe nan gaba kuma za a shigar da karin hukumomi.
“Ya yi tasiri matuka wajen kara yawan kudaden shigar gwamnati; Daga watan Janairu zuwa Oktoban 2021, an tare kudaden shigar Naira biliyan 86 ta wannan hanyar.
“Mun kuma tara Naira tiriliyan bakwai daga kudaden da aka biya mu daga watan Janairu zuwa Nuwamban 2021, muka kuma ba da izinin fitar da Naira tiriliyan tara a tsawon lokacin,” inji ta.
Sai dai ta ce har yanzu akwai matsala wajen aiwatar da tsarin, saboda kudade na ke ci gaba da zurarewa, wanda daya ne daga cikin ayyukan da aka sa kwamitin ya magance.
“Gwamnati tana sane da matsalolin da hukumomi da ma’aikatun gwamnati suke fuskanta tun a farkon watan Disamban 2020 wajen amfani da TSA,” inji ministar.
Aikin kwamitin, a cewarta, zai bayar da muhimmanci wajen samo mafita ga matsalolin da suke hana hukumomi ma’aikatun gwamnati fitar da rahoton harkokin kudadensu na shekara-shekara a kan lokaci.
‘Baki da goro’
Duk da cewa shi ma Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris, ya tabbatar cewa kudade na ci gaba zurarewa daga asusun na TSA, amma a lokacin da wakilinmu ya nemi karin bayani, sai ya ki cewa uffan.
Ita kuma ministar, da wakilinmu ya tambaye ta hakikanin matsalolin da ke addabar tsarin, cewa ta yi, “Shi ya sa aka kafa kwamitin domin yin gyara da nemo mafita, idan na bayyana kuma, zai kawo wa aikin kwamitin cikas.”
Ta ce duk ma matsalar da ake da ita, kwamitin zai magance ta tare da bullo da tsauraran hanyoyin toshe zurarewar kudaden shiga.
Mun yi kokarin sanin adadin kudaden da suka bi ta asusun na TSA tun daga 2015 da aka fara amfani da shi, amma ministar da kuma Ofisihn Akanta-Janar na Tarayya, kowannensu ya ki yarda ya bayyana.
Sai dai a baya can Ofishin Akanta-Janar din ya taba shaida wa wakilinmu cewa adadin kudaden da ke cikin TSA na sauran canzawa, kosan bayan kowane minti daya saboda yadda kudaden suke yawan shiga da kuma fita daga cikinsa.
‘Ya kamata a inganat TSA’
Masana dai na ganin akwai babbar bukatar inganta tsarin, lura da irin yawan kudaden da ke bi ta cikinsa.
Marubucin littafin ‘Treasury Single Account Policy in Nigeria’ a kan tsarin TSA a Najeirya, ya ce, “Ya kamata a inganta tsarin sanya ido da kuma auna nasarar amfanin tsarin, musamman daga Ofishin Akanta-Janar na Tarayya da kuma CBN (wadandan su ne manyan masu kula da amfani da shi).”
David Akwu, malami ne a Jami’ar Najeriya ta Nsukka, ya ce ba za a rasa ci gaban zurarewar kudade daga asusun ba, duk da cewa ya inganta yadda ake gudanar da kudaden gwamnati da tara haraji a wuri daya.
Shi ma wani babban masanin tattalin arziki a kamfanin SMP, Paul Alaje, ya ce, “TSA ya taimaka wajen kara yawan kudaden shigar gwamnati, musamman wadanda suke zurarewa kafin a fara amfani da tasrin.
“Zuwa yanzu dai an toshe wasu kofofin amma ba dukkansu ba,” inji shi, yana mai cewa tsarin ya bunkasa yawan kudaden shiga da gwamnati ke samu.”
Ya ce sauran amfanin tsarin sun hada da karbar kudaden gwamnati ba tare da bata lokaci ba, karin kudaden harajin da take samu da kuma raguwar kudaden da suke ajiye amma ba a amfani da su.
Hikimar bullo da TSA
Daraktan TSA da Kudaden Shiga ta Intanet a Ofishin Akanta-Janar na Tarayya, Sylva Okolieaboh, a cikin wata makala da ya gabatar ya ce, TSA tsari ne na karbar kudade amma ba na haraji ba.
Ya ce an bullo da shi ne domin magance matsalolin gudanar da kudade da suka hada da amfani da asusun ajiya fiye da daya, asusun ajiya da ke da makudan kudade da ba a amfani da su, da kuma matsalar rashin iya sanin ainihin kudaden da gwamnati ke da su a kasa.
Sauran matsalolin sun hada da yawan kudaden da ake cazar kan asusun ajiyar ma’aikatun gwamnati, rashin kyakkyawan tsarin gudanar harkokin hukumomin tara kudade, rashin kudaden aiwatar da kasafin kudi da kuma jinkirin bankuna wajen biyan kudaden da ya kamata a sanya a asusun Gwamantin Tarayya.
Ya ce a yanzu TSA ya taimaka gwamnati tana iya sanin hakikanin kudaden da take da su, sannan ya kawar da kudaden da cajin da take biya Naira biliyan bakwai a duk wata tare da samar da ingantacciyar hanyar lura da ayyukan ma’aikatu da hukumomin gwamanti.