Yadda mabarata ke damfarar alhazai a Saudiyya
Ga alama mabarata na cin karensu ba babbaka a kasar Saudiyya, inda suke yin amfani da dabaru iri-iri suna karbar makudan kudi daga wurin alhazai. Wadansu mabaratan sukan bi alhazan a garuruwa daban-daban, kamar Makka da Madina da masaukan alhazan da wuraren Ibada da shemomi inda aka sauke alhazai a Mina, suna bara suna cewa […]

Ga alama mabarata na cin karensu ba babbaka a kasar Saudiyya, inda suke yin amfani da dabaru iri-iri suna karbar makudan kudi daga wurin alhazai.
Wadansu mabaratan sukan bi alhazan a garuruwa daban-daban, kamar Makka da Madina da masaukan alhazan da wuraren Ibada da shemomi inda aka sauke alhazai a Mina, suna bara suna cewa daga yankin Kashmir na kasar Indiya suka taho, saboda neman taimakon kudi don kai wa ’yan uwa Musulmi da yaki ya daidaita.
Wadansu mabaratan kuma nade wadansu gabobin jikinsu suke yi da bandeji ta yadda zai nuna suna da wata nakasa, ko dai ta hannu daya ko ta kafa daya, ko kuma su shafa wa bandejin da suka nada jan fenti ta yadda daga nesa alhaji zai yi tsammanin mugun rauni suka ji.
Wadansu mata kuwa lullube jikinsu suke yi da hijabi da nikabi ta yadda ba za a gane kamanninsu ba su tsaya a tsakiyar hanya suna bara. Wadansu mabaratan kuma jarirai da yara kanana suke kwantarwa a kan hanyar da alhazai suke wucewa suna rokonsu kudi.
Mabaratan sun hada da fararen fata da bakake, amma mafi yawa mutanen Najeriya da Nijar da Bangaladash da Indiya da Pakistan da Indonesiya da kuma Yamen ne.
Wani mabaraci wanda ya ce daga yankin Kashmir na kasar Indiya yake, mai suna Almukan Shaje, ya ce, “Ni ba damfara nake yi ba kuma ba bara nake yi ba, ina nemen taimakon kudi ne don kai wa ’yan uwana Musulmi da suka tagayyara sakamakon yakin da ake yi a yankin Kashmir na kasarmu.”
Ya ci gaba da cewa, “Zan tattara kudin na kai musu, ko kwabo ba zan ci ba, haka nake yi duk shekara, ba damfarar mutane nake yi ba, saboda yin haka haramun ne a Musulunci. Ba na takura wa kowa dole sai ya ba da taimako, sai wanda ya ga dama zai bayar, ba lallai ba dole. ’Yan uwanmu ne, idan ba mu nema musu taimako ba babu wanda zai taimaka musu.”
Shi ma wani mabaraci da ya nade hannunsa da bandeji, wanda ya ki bayyana sunansa ko kasar da ya fito, ya musanta zargin da mutane suka yi masa na yaudarar jama’a. Mutumin wanda Hausarsa ta yi kama da ta dan Najeriya, ya ce, “Ba karya nake yi ba, ciwo na ji sakamakon hadarin da muka yi a mota.”
Wata mata kuma da ke yin bara a kan hanyar zuwa wurin jifar Shaidan, mai suna Hajiya Maryam Sulaiman daga kasar Nijer, ta ce talauci ne ya ya sa take yin bara. “Mijina ya mutu ya bar ni da ’ya’ya tara a garin nan. Babu wanda zai taimaka mini ya dauki nauyina da na ’ya’yana. Ka ga dole na yi bara don na samu abin da za mu rika cin abinci.” In ji ta.
Da wakilinmu ya tambaye ta me ya sa ba za ta koma gida Nijar ba, sai ta ce, ‘Mun dade rabonmu da Nijar. Tun ina amarya mijina ya kawo ni garin nan. A nan na haifi ’ya’yana gaba daya. Idan na koma Nijar wurin wa zan je, waye zai dauki nauyina da ’ya’ya tara? A nan kuwa kullum ka fito ba za ka rasa kudin da za ka sayi abinci ba, don wadansu sukan ba mu Riyal biyar zuwa goma. Mu ma ba a son ranmu muke yin barar ba, dole ce ta sa muke yi.”
Ita ma Saudatu wacce ta ki bayyana gari ko kasar da ta fito da take yin bara da kananan yara cewa ta yi, ‘Dole ce ta sa muke zuwa nan garin mu yi bara saboda shugabaninmu ba sa kula da mu, talauci ya yi yawa a kasarmu, gashi kuma babu zaman lafiya da kwanciyar hankali.’
Hajiya Saudatu wacce take yin Hausa irin ta Nijeriya ta ci gaba da cewa, ‘Shi ya sa da muka rabu da mijina sai na taho Saudiyya don na nemi na kaina. Wadannan yara da ka gani a nan na yi aure na haife su, da ubansu, muna tare da shi a nan Makka, shi ma yana fita nema, a haka muke rufa wa kanmu asiri.”
’Yan kasashen Najeriya da Nijar da dama da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana rashin jin dadinsu da yadda mabaratan suke zubar da mutuncin kasashen nasu.
Alhaji Ibrahima Yusuffu daga Nijar cewa ya yi, ‘karya suke yi ba talauci ba ne ya sa suke yin bara ba tsabar neman kudi ne kawai. Sauran talakawan da suke Nijar mutuwa suka yi? Ka san idan zuciyar mutun ta mutu ba zai iya sana’a ba sai roko. Babu abin da zan ce sai dai Allah Ya sauwake, Allah Ya ganar da su gaskiya.’
Shi ma Alhaji Muhammadu daga Najeriya cewa ya yi, “Gaskiya wadannan mutane da suke irin wannan dabi’a ta bara da roko a nan Saudiyya suna zubar mana da mutunci, ba ma jin dadi idan mun gan su, shi ya sa za ka ga wadansu daga cikinsu suke lullube fuskokinsu saboda kunya. Allah Ya shirye su.”
Wani dan kasar Indiya mai suna Muhammad Khan ya karyata masu karbar kudi da sunan taimaka wa mutanen Kashmir, inda ya ce, “karya suke yi ba wanda ya turo su daga Indiya su karbi taimako saboda mutanen Kashmir. Ba wani yaki da ake yi a can, babu wanda ya shiga wani mawuyacin hali, kawai damfarar mutane suke yi suka karbe musu kudi.”
Wani malami mai wa’azin Musulunci mai suna Malam Muhammad Mustafa, kira ya yi ga mabaratan su ji tsoron Allah su koma kasashensu, domin zubar da mutuncin kasa abu ne marar kyau.
Wani Jami’i a hukumar da ke hana tallace-tallace da barace-barace a kan tituna a birnin Makka mai suna Muhammad Harbiyyun ya bayyana cewa, hukumar Saudiyya ta hana bara ne saboda akwai tsari da tanade-tanade da aka yi na kula da miskinai da nakasassu kamar yadda tasrin shari’ar musulunci ya tanada.
Ya ce, “Shi ya sa muke kama duk masu yin bara a kan titi don mayar da su kasashen da suka fito ba tare da wani bata lokaci ba.”