NAJERIYA A YAU: Yadda Mabaratan Zamani Ke Neman Hana Bayar Da Sadaka
Yadda lafiyayyu mutane da ke barar zamani suke karuwa fiye da nakasassu da almajirai.
Lafiyayyun mutane da ba nakasassu ko ’yan makarantar allo ba, da suka rungumi dabi’ar bara sai kara karuwa suke.
Lamarin ya kai da wuya mutum ya fito ya koma gida ba tare da wani ya yi masa ba-zata ya roke shi kudi ko abin ci ba.
- DAGA LARABA: Ƙalubalen Da Matan Aure Ma’aikata Ke Fuskanta
- Abin Da Ya Sa Masu Zaman Waƙafi Ke Shafe Shekaru Ba Hukunci
Yawancin masu irin wannan rokon sukan fito ne tsaf-tsaf kamar wasu ma’aikata ko ’yan kasuwa.
Shin yaya jama’a ke kallon wannan dabi’a da ta zama ruwan dare?
Shirin Najeriya A Yau na wanna lokaci na tafe da karin bayani.
Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan