Yadda mace ta kwato wa ’yan fansho 300 hakkinsu
Wata da mijinta ya rasu ba tare da an biya shi kudin fansho ba bayan sallama daga aikin gwamnati da ya yi shekara 30, ta samu nasarar zaburar da gwamnatin ta fara aikin biyan ragowar kudin ma’aikata sama da 300 a Hukumar yi wa kasa Hidima (NYSC). Matar mai suna Hadiza Ali Barka wadda ’yar […]

Wata da mijinta ya rasu ba tare da an biya shi kudin fansho ba bayan sallama daga aikin gwamnati da ya yi shekara 30, ta samu nasarar zaburar da gwamnatin ta fara aikin biyan ragowar kudin ma’aikata sama da 300 a Hukumar yi wa kasa Hidima (NYSC).
Matar mai suna Hadiza Ali Barka wadda ’yar asalin karamar Hukumar Gamboru-Ngala ce da ke Jihar Borno, ta yi ta jigila daga kauyensu zuwa hedikwatar Hukumar NYSC da ke Abuja a tsawon shekara 7, kafin hukumar ta biya ta Naira dubu 223 kari a kan Naira dubu 334 da tun farko aka biya mijinta, a matsayn somin tabi.
Matar wadda a yanzu ta samu matsuguni da wadansu suka taimaka mata da shi a garin Kubwa, Abuja, inda take tare da biyu daga cikin ’ya’ya 6 da ta haifa da minjinta, ta bayyana wa Aminiya cewa marigayi mijinta, Malam Ali Barka wanda suka fito daga yanki daya a Jihar Borno ya shafe shekara 30 a matsayin maigadi a hukumar; tun a loakcin hedikwatarta na Legas. Ta ce an yi masa ritaya ne a farkon shekarar 2007, bayan fara amfani da tsarin gwamnati na rage kananan ma’aikata a lokacin da gwamnatin Obasanjo ta kirkiro.
Sai dai ta ce ta yi amfani da bangaren kudin da aka ba ta wajen gyara gidansu, wanda mijinta ya gina bayan nasarar karbar kudin somin- tabi, ita kuma ta yi wa gidan gyara sakamakon lalata shi da maharan Boko Haram suka yi, lokacin da suka kai hari a yankinsu.
“Da farko ina da burin amfani da abin da ya rage na kudin wajen yin wata sana’a, sai dai bayan gyara gidan da biyan basussukan hidimar auren babbar ’yarmu, babu abin da ya rage a cikin kudin kuma a dalilin haka ne na sake dawowa yanzu don karbar kudinsa da hukumar ta rike bayan an sanar da ni cewa hakkinsa ya dara abin da aka bayar nesa ba kusa ba,” inji ta.
Wakilinmu wanda ya ziyarci Hedikwatar Hukumar NYSC ta kasa a Abuja, inda Malama Hadiza ta zama sananniyar fuska, ya gano cewa matsalar rashin biyan cikakken kudi ga rukunin ma’aikatan da aka sallama yau shekara 11, ya shafi masu ritaya da dama. Bayanai sun ce ma’aikatan da lamarin ya shafa sun hada da masu gadi da direbobi da masu shara da masu kula da fulawa da sauran ma’aikata ’yan kasa da matakin albashi na 7. Kuma sun shiga matsala ce dalilin rashin sanin takamaiman inda za su nemi hakkinsu da hanyar da za su bi, wanda karancin ilimi ya haifar.
Haka bayanai sun ce akwai matsalar rashin cikakken lafiya da wadansu daga cikinsu suke ciki a halin yanzu, ta yadda ba zai ba su iya dawainiyar kai-komo ba a yayin da wadansu kuma tuni suka rasu kuma iyalansu ba su da sha’awar ci gaba da gwagwarmayar da suke gani a matsayin mara amfani.
Sai dai duk da wadannan matsaloli matar marigayin ta nuna halin rashin gajiyawa, kuma kokarin nata ya haifar da sakamako mai kyau, inda Hukumar Sake Fasalin Aikin Gwamnati (BPSR) da ke da alhakin tattara bayanan ma’akatan Gwamnatin Tarayya da aka sallama daga hukumominta 300, ta umarci Hukumar NYSC ta tattaro mata bayanan wadanda lamarin ya shafa su 300 da nufin biyan su hakkinsu.