Yadda mafarauta suka kubutar da yaron da aka yi garkuwa da shi

A yanzu haka mutanen kauyen Gurusu da ke garin Gadan ’Yanbiyu da ke karamar Hukumar Bosso da ke Jihar Neja, suna cikin farin ciki bayan mafarauta suka ceto daya daga cikin ’ya’yan Wazirin garin mai suna Abdul Musa daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.Wazirin Gurusu, Malam Musa Yiko ya bayyana wa Aminiya cewa […]

Yadda mafarauta suka kubutar da yaron da aka yi garkuwa da shi
Yadda mafarauta suka kubutar da yaron da aka yi garkuwa da shi

A yanzu haka mutanen kauyen Gurusu da ke garin Gadan ’Yanbiyu da ke karamar Hukumar Bosso da ke Jihar Neja, suna cikin farin ciki bayan mafarauta suka ceto daya daga cikin ’ya’yan Wazirin garin mai suna Abdul Musa daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.
Wazirin Gurusu, Malam Musa Yiko ya bayyana wa Aminiya cewa barayin sun sace dansa Abdul a ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe 8:00 na yamma yayin da ake bikin aure a garin.
Ya ce “Ina gida da safe sai suka bugo mini waya suka ce wai dana Abdul yana hannunsu sun sace shi saboda haka idan ina bukatarsa, sai na biya su Naira miliyan biyar. Sai na ce musu ba ni da Naira miliyan biyar. Daga baya sai suka rage zuwa Naira miliyan biyu. Haka muka yi ta yi har kudin ya koma Naira miliyan daya, a karshe suka rage zuwa Naira dubu dari biyu. Sai na ce zan kawo musu kudin, suka ce in kai musu kudin tsohon garin Gurusu akwai wani labin shanu in ajiye a wurin. Sai na kai rahoto wurin ’yan sanda, suka karbi lambobin wayar da suke kirana suna yi mini barazana,” inji shi.
Malam Yiko ya ce ana cikin neman yaron ne sai wadansu mafarauta suka tsinto yaron cikin dare suka dawo da shi gida. Ya ce dansa ya dawo gida lami lafiya ba tare da wata matsala ba, bayan kwana biyun da ya yi a hannun wadanda suka sace shi. Sai dai ya ce abin da yake damunsa shi ne har yanzu barayin suna bugo masa waya suna cewa dole ya ba su Naira dubu dari muddin yana son ransa. Yiko ya ce barayin sun sha alwashin kashe shi muddin bai ba su kudin ba.
Abdul Musa wanda dan aji biyar ne a makarantar Gadar ’Yanbiyu  ya ce suna cikin wasa da yara a yayin da aka kawo amarya sai wani mai suna Daniel ya kira shi daga nan sai ya shake shi. “Da Daniel ya kira ni sai kawai ya shake ni shi da wani mutum suka dora ni a kan babur suka rufe mini ido. Daga nan sai ganina na yi a cikn kungurmin daji,” inji yaron.
Ya ce wadanda suka sace shi sun yi kama da Fulani kuma su hudu ne suna yin magana da Fulatanci. Kuma ya ce sukan ba shi abinci sau daya da ruwa sau daya kuma suna canja wuri daga lokaci zuwa lokaci.
Yaron ya kara da cewa dukkansu babu wanda ya rufe ido sai mutum daya daga cikinsu, kuma ya ce yana zaune da dare tare da wadanda suke tsare da shi sai kawai wasu masu farauta suka nufo su. “barayin na ganinsu sai suka gudu suka bar ni a wurin. Nan take mafarautan suka tambayi sunana da kauyenmu na gaya musu, shi ne suka kawo ni gida,” inji shi.
daya daga cikin mafarautan wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya bayyana wa Aminiya cewa sun samu labarin sace yaron. “Mun samu labarin an sace yaron da muka fita sai muka yanke shawarar mu shiga dajin da nufin farautar namun daji da kuma farautar wadanda suka sace shi. Sai muka yi sa’a muka same su, ba mu kama su ba amma mun samu nasarar ceto yaron,” inji shi.
Wani da ake zargi da a yanzu yake tsare a hannun ’yan sanda mai suna Abubakar Sa’idu ya ce yaron karya ya yi masa. Ya ce sunansa Abubakar Sa’idu ba Daniel ba, kamar yadda aka ce yaron ya fadi.
“Na je na aiki yaron amma ni ba hannuna a sace shi. Ni manomi ne kuma almajiri, ina da aure da da daya. Ni ba barawo ba ne mutanen garinmu ma za su yi mini, shaida kuma ni sunana Abubakar Sa’idu ba Daniel ba kamar yadda aka ce yaron ya fadi,” inji shi
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, ASP Bala Elkana, ya ce daya daga cikin wadanda ake zargi yana hannu, kuma ya ce ’yan sanda da hadin gwiwar mafarauta sun shiga dajin inda suka ceto yaron kuma yana cikin koshin lafiya tare da iyayensa.
Ya bayyana cewa rundunar na ci gaba da bin sawun sauran wadanda ake zargi da sace yaron, kuma za su gurfanar da wadanda suka kama a gaban kotu don fuskantar shari’a.