Yadda mafi lalacin kulob ya yi nasara ɗaya cikin shekara 20

Nasarar karshe da kungiyar ta samu ita ce wasan sada zumunci da Liechtenstein a shekarar 2004.

Yadda mafi lalacin kulob ya yi nasara ɗaya cikin shekara 20

Jiran shekaru 20 domin cin nasarar wasan kwallon kafa lokaci ne mai tsawo da ba kowace kungiya za ta iya jurewa ba, koda kuwa a hukumance kulob din ne mafi muni a fagen tamaula a duniya.

Amma ga San Marino, wadancan shekaru 20 da ke cike da damuwa zullumi sun koma farin cikin a ranar Alhamis din makon jiya inda kulob din ya doke Liechtenstein da ci 1-0.

Koda dai ba sabon abu ba ne ga magoya baya su shiga yanayi na zullumin rashin tabuka rawar gaban hantsi na kulob dinsu, amma magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta San Marino za su iya daukar kansu a matsayin mafiya dadewa cikin zullumin.

Karamar kasar mai mutane dubu 33,000 kacal, wacce Italiya ke kewaye da ita – da Italiyar ta zama daya daga cikin kasashen da suka fi samun nasara a fagen kwallon kafa a duniya – ta yi tarihin rashin nasara na tsawon shekaru 20.

Nasarar karshe da kungiyar ta samu ita ce wasan sada zumunci da Liechtenstein a shekarar 2004.

Wannan tarihin ya sa karamar kasar ta zama ta 210 a cikin 210. Abin da ya hana su wasannin sada zumunta da kungiyoyin UEFA.

Shekaru 17 ke nan da kyaftin din San Marino, Matteo Vitaioli, dan wasan da ya fi yawan buga wasanni a tarihin kasar, ya fara wakilcin tawagar kasarsa, amma har yanzu bai taba murnar samun nasara ba.

Shekaru 20 da wasanni 140 daidai a ciki har da rashin nasara da kasancewa a gabar rashin nasarar, yanzu wadannan duk sun gabata sakamakon San Marino, kasa ta biyar mafi kankanta a duniya, ta samu nasara daya tilo a tarihin kulob din – inda ta yi nasara a wasan sada zumunci da Liechtenstein da ci 1-0.

Amma Vitaioli da takwarorinsa sun samu damar rubuta wani sabon babi ga kasarsu a ranar Alhamis (29 ga watan jiya) lokacin da suka nemi samun nasarar farko a karawar da suka yi da abokiyar karawarsu daya tilo da ita San Marinon ce kadai ta taba doke su – inda a lokacin Liechtenstein ya ziyarci kasar a gasar cin kofin kasashen Turai.

Kulob 11 ne kawai a halin yanzu tsakanin kungiyoyin biyu a cikin jerin kasashen da suka fi iya murza leda da hukumar FIFA ta fitar, inda Liechtenstein take 199 a jerin, sannan ta zama kurar baya a kulob din da suka fi rashin nasara cikin wasanni 40 da suka buga a jere.

Kasar San Marino tana da yawan mutane 33,000 kadai sannan tana da fadin murabba’in kilomita 61 – kusan rabin girman Manchester.

Bisa kididdigar da FIFA ta yi, ita ce jagaba a tawagar kwallon ta kasa mafi muni a duniya – kulob din da ke matsayi na 210 wanda ya yi rashin nasara a wasanni 196 cikin 205 da ya fafata.

Vitaioli ya shaida wa BBC cewa “Babban abin tunawa mafi muni, shi ne wasan da muka yi a waje da kasar Netherlands a 2011, wanda aka tashi 11-0 aka doke mu.

“Ko da ake cin mu kwallo takwas ko tara da sauran lokaci kafin a tashi wasan, amma a hakan na tuna magoya bayan Netherlands sun yi ta sowa da tsuma ’yan wasan nasu domin ganin sun kara jefa manakwallaye.”

Amma mafi munin doke kasar da aka yi shi ne lokacin da ta kara da Jamus inda aka lallasa San Marinon da 13 da nema a 2006.

Nasarar da San Marino ta samu ta karshe ita ce ta wasan sada zumunta da ta doke Liechtenstein da ci 1-0 a watan Afrilun 2004, lokacin da Andy Selva, wanda ya fi kowa zura kwallo a raga a kasar da kwallaye takwas, ya kafa tarihin da za a dade ana tunawa da shi.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja