Yadda magidanci ya daɓa wa amaryarsa wuƙa ya babbake gawarta

Mijin ya daɓa wa matar wuƙa kuma ya kulle ta a ɗaki, sannan ya banka mata wuta, inda ya raunata kansa.

Yadda magidanci ya daɓa wa amaryarsa wuƙa ya babbake gawarta

Wuka

Wani magidanci mai shekara 30, mai suna Motunrayo Olaniyi, ya daɓa wa sabuwar amaryarsa mai suna Olajumoke wuƙa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarta.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar yannkin rukunin gidaje na Amazing Grace da ke Elepe a yankin Ikorodu a Jihar Legas, bayan wata zazzafar taƙaddama da ta ɓarke a tsakanin ma’auratan da ba su daɗe da aure ba.

A yayin da Rundunar ’yan sandan Jihar Legas take tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da mai magana da yawunta, Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Asabar, ta bayyana cewa, Motunrayo ya daɓa wa matarsa mai shekara 25 wuƙa sau da dama yayin rikicin, inda ya kulle ta a ɗaki, sannan ya banka mata wuta.

Ya ƙara da cewa, wanda ake zargin ya kuma raunata kansa bayan ya yi aika-aikar.

Ya ce, jami’an ’yan sandan da suka isa wurin su ne suka kashe gobarar da matashin ya kunna bayan da ya yi kisan, inda suka gano gawar Olajumoke da raunuka a jikinta.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “an ankarar da rundunar ne ta hanyar kiran waya a ranar 4 ga Oktoba a yankin Ikorodu cewa, wasu ma’aurata da suka yi aure ba da jimawa ba, Motunrayo Olaniyi mai shekaru 30 da matarsa Olajumoke mai shekara 25, an yi zargin sun kaure da faɗa a gidansu da ke yankin rukunin gidajen na Amazing Grace, Elepe, Ikorodu.

Inda mijin ya daɓa wa matar wuƙa kuma ya kulle ta a ɗaki, sannan ya banka mata wuta, inda ya raunata kansa. ’Yan sanda daga sashin Ikorodu sun amsa kiran da aka yi musu, tare da kashe gobarar, inda suka gano gawar Olajumoke da raunuka a jikinta.”

Kakakin ’yan sandan ya ci gaba da cewa, an ceto Olaniyi kuma aka garzaya da shi wani asibiti da ke kusa, inda aka yi masa magani, aka sallame shi kafin daga bisani ’yan sanda suka tsare shi.

A cewarsa, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, wanda ake zargin ya daɓa wa matarsa wuƙa ne a yayin rikicin tare da yi wa kansa ƙananan raunuka.

“An ajiye gawar matar a ɗakin ajiye gawa na babban asibitin Ikorodu domin ci gaba da bincike,” in ji shi.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tags