Yadda uba ya kashe ‘ya’yansa ya kuma jikkata mahaifinsa

Wani magidanci ya shiga hannu bayan zarginsa da hallaka ‘ya’yansa na cikinsa biyu da kuma jikkata mahaifinsa mai shekaru 72. Mutumin mai shekaru 34 ya sa tabarya ya yi ta bugun ‘ya’yan nasa, da suka hada mai shekaru biyar da mai shekaru bakwai a yayin da suke barci, sannan ya yi wa mahaifinsa mai shekaru […]

Yadda uba ya kashe ‘ya’yansa ya kuma jikkata mahaifinsa

Wanda ake zargin da ankwa, rike da tabaryar da ake zargi ya yi amfani da ita a aika-aikan

Wani magidanci ya shiga hannu bayan zarginsa da hallaka ‘ya’yansa na cikinsa biyu da kuma jikkata mahaifinsa mai shekaru 72.

Mutumin mai shekaru 34 ya sa tabarya ya yi ta bugun ‘ya’yan nasa, da suka hada mai shekaru biyar da mai shekaru bakwai a yayin da suke barci, sannan ya yi wa mahaifinsa mai shekaru 72 mummunan rauni da tabaryar.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Anambra SP Haruna Mohammed ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya ce ya auku da misalin 1.00 na dare a yankin Azu-Ogbunike, da ke Karamar Hukumar Oyi a jihar Anambra, kuma kame wanda ake zargin.

SP Mohammed Haruna ya ce an kai yaran asibiti inda likitoci suka tabbatar sun rasu aka kuma ajiye gawarwakinsu a dakin ajiyar gawa, yayin da ake kula da lafiyar dattijon mai shekaru 72.

Ya kara da cewa zuwa yanzu ba a san dalilin wanda ake zargin na yin aika-aikan ba, sai dai ana bincikar lamarin a Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar (CID) da ke Awka, babban birnin jihar Anambra.