Yadda mahaifinsu ya shekara bakwai yana lalata da su
Wani magidanci mai shekaru 50 da ya shafe shekaru yana lalata da ‘ya’yansa mata ya fada komar ‘yan sanda. Wanda ake zargin, Peter Ayemoba ya ce ya shekara bakwai yana saduwa da ‘ya’yan cikinsa mata su biyu tun bayan rasuwar matarsa. A cewarsa, kwanciyar da ya keyi da ‘yayan na cikinsa ta ba shi damar […]
Wani magidanci mai shekaru 50 da ya shafe shekaru yana lalata da ‘ya’yansa mata ya fada komar ‘yan sanda.
Wanda ake zargin, Peter Ayemoba ya ce ya shekara bakwai yana saduwa da ‘ya’yan cikinsa mata su biyu tun bayan rasuwar matarsa.
A cewarsa, kwanciyar da ya keyi da ‘yayan na cikinsa ta ba shi damar kara samun kusanci da matarsa da ta mutu tare da kuma shakuwa da yara nasa.
“Mutuwar matata ta dimauta ni sosai domin ban san yadda har na fara lalata da ‘ya’yana mata ba”, inji shi.
- Kotu ta saki yarinyar da ta kashe wanda zai yi mata fyade
- An kai mutumin da ya yi wa diyarsa jaririya fyade kurkuku
- Yadda matashin da ya yi wa mata 40 fyade a Kano ya shiga hannu
“Ina jin baki aka yi min, saboda gaskiya wannan abun da na shekara bakwai ina aikatawa abu ne da ba saba gani ba.
“Tun bayan mutuwar mai dakina sai na yi kokarin samun kusanci da ‘ya’yana mata har ta kai ga na fara saduwa da su”, inji shi.
Ayemoba ya ce da yardar yaran yake saduwa da su ya kuma ci gaba da hakan har bayan ya auri matarsa ta biyu.
“Bayan bikin binne mai dakina sai na sami kusanci da ‘ya’ana mata biyu, inda nake saduwa da su a lokuta daban-daban a kai a kai, kuma ba su damu ba.
“Wani lokacin in na bukaci in sadu da su amma suka ki na kan yi musu barazana cewa zan kashe su na kuma kashe kai na.
“Ina nuna masu cewa ba laifi ba idan mutum ya sadu da ‘ya’yansa. Ina amfani da littafin linjija na nuna masu cewa ko a littafin ba a hana ba.
“Da suka ga ina yawan matsa musu sai suka bukaci na kara aure amma ko bayan da na yi auren ina saduwa da su a duk lokacin da matata ba ta gida.
“Ba su fada wa matata ba kasancewar ba su da kusanci da ita, saboda haka ba ta abin da ke faruwa ba. Su ma ‘ya’yana maza hudu ba su san halin da na shiga da ‘yan uwansu ba.
“Asiri na ya tonu ne bayan yaran sun fada wasu danginmu wadanda su kuma suka sanar da ‘yan sanda.
“Na yi mamakin abin da ‘ya’yan nawa su kayi, domin da yardarsu nake yin wannan kazamar mu’amalar da su”, inji shi.
Ayemoba ya ce ya kan yi nadamar mummunan abin da yake aikatawa da ‘ya’yansa na cikinsa.
Ya ce duk sadda yake lalata da su akwai shedani da ke rada masa a zuciyarsa cewa ai ba shi ne farkon wanda ke saduwa da ‘ya’yansa ba.