Yadda mahara suka hallaka mutane a masallatai da Coci a Borno da Adamawa
Shugaban dakarun kare al’umma, watau Cibilian JTF, na kauyen Kawuri da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno, inda wadansu da ake zaton ‘yan Boko Haram ne suka kai wa hari a ranar lahadin da ta gabata, Lawal Mustapha, ya bayyana cewa yana cikin wadanda suka yi jana’izar mutane 83 da aka kashe ranar litinin […]
????????????????????????????????????

Shugaban dakarun kare al’umma, watau Cibilian JTF, na kauyen Kawuri da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno, inda wadansu da ake zaton ‘yan Boko Haram ne suka kai wa hari a ranar lahadin da ta gabata, Lawal Mustapha, ya bayyana cewa yana cikin wadanda suka yi jana’izar mutane 83 da aka kashe ranar litinin a sakamakon farmakin da aka kai kauyen. Kuma daga baya sun sake gano gawarwakin mutane biyu da suka kone.
Da yake bayanin yadda maharan suka fada wa kauyen, ya ce, sun shiga kauyen ne a cikin ayarin motoci 22, ciki har da motoci yaki guda biyu da motocin soja kirar Hilud guda shida. Sun fara farmakin daga kasuwa ne, sannan suka wuce sauran wurare. Bayaninsa ya nuna cewa adadin wadanda aka kashe ya kai 85 ke nan.
Mutanen kauyen sun bayyana wa wakilinmu da ya je kauyen cewa, maharan sun kona masallatai bakwai, ciki har da babban masallacin kauyen.
Shi ma da yake karin bayani, kansila mai wakiltar Kawuri, Dala Lawal, ya ce, an bude wa kauyen wuta ne da misalin karfe 5 na yamman ranar lahadi har zuwa karfe daya na dare, ya ce an kashe limamin daya daga cikin masallatan da aka kona, kuma an kashe wadansu mutane a yayin da suke sallah a wani masallaci.
Ya ce,mutane 35 suna kwance a asibitin Konduga, 10 kuma suna kwance a asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri, a yayin da guda biyar kuma suke kwance a asibitin Bama.
Gwamna Kashim Shettima wanda ya ziyarci kauyen Kawuri domin jajanta musu sai da ya zubar da hawaye, inda ya bukaci duk wadanda aka kai wa hari su rika kare kansu da kansu a duk lokacin da aka fada musu. Ya bayar da gudunmuwar Naira dubu 250 ga kowane iyalen wadanda suka rasu. Kuma an raba wa sauran mutanen kauyen abinci da sauran kayayyaki. Ya kuma kai ziyara asibitin Konduga.
A jihar Adamawa ma an kai farmakin ranar lahadin inda aka kashe mutane 32, mutane 11 suka jikkata.
Shugaban karamar hukumar Madagali, Maina Ularamu, ya ce mutane 32 ne aka kashe a yayin farmakin, inda maharan suka yi wa mutane 12 yankan rago a Coci, suka harbi mutane 20, a yayin farmakion da suka kwashe awowi hudu suna cin karensu babu babbaka.
Ya ce, ‘wadansu mutanen kauye sun kira ni suka ce an kai musu farmaki, nan da nan na sanar da jami’an tsaro, amma babu wanda ya je wurin sai DPO da mutanensa, wanda shi ma aka yi masa kwanton-bauna, aka kashe masa mutum biyu, aka kwace motarsu. Haka aka ci gaba da farmakin har karfe biyu na dare.’’
Shugaban ya ci gaba da cewa, ‘’DPO ya fada mini cewa ya yi magana da sojoji wadanda suka tabbatar masa cewa sun riga sun isa wurin, amma da ya je wurin tare da mutanensa sai aka bude musu wuta, inda shi da wadansu ‘yan sanda bakwai suka tsira da raunuka.’
A cewarsa, ‘’fiye da mutane 30 aka kashe a yayin farmakin, aka fille wa mutane 12 kawuna. Aka dora a kan jikkunansu, sauran kuma an harbe su ne a kusa da kusa.