Yadda mahara suka hallaka mutum 17 a Jos
Akalla mutum 17 ne suka rasu inda wasu da dama suka samu rauni a garin Jos, Jihar Filato sakamakon jefa musu bama-bamai da aka yi a tashar mota ta Bauchi Road da karamar tashar mota da ke fuskantar kofar shiga Jami’ar Jos a yammacin ranar Alhamis din makon jiya. A cikin wadanda suka rasu har […]
Akalla mutum 17 ne suka rasu inda wasu da dama suka samu rauni a garin Jos, Jihar Filato sakamakon jefa musu bama-bamai da aka yi a tashar mota ta Bauchi Road da karamar tashar mota da ke fuskantar kofar shiga Jami’ar Jos a yammacin ranar Alhamis din makon jiya.
A cikin wadanda suka rasu har da shugaban ’yan kasuwar bakin tashar Bauchi Road Malam Muhammad Adam Maikasuwa da aka fi sani da dan Bauchi da wani dan sanda da ke bayar da hanu a kofar tashar.
Bam na farko da ya tashi a tashar motar kofar Jami’ar Jos a kan hayar Bauchi, wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa ya tashi ne da misalin karfe 5:30 na yamma.
Majiyar ta ce ana zargin wani dan kunar bakin wake ne ya je tashar da ake daukar fasinja daga Jos zuwa Bauchi da Gombe ya tayar da bam din bayan an zo da shi a cikin wata mota kirar jeep, inda ya sauka ya ce yana neman motar zuwa Gombe.
Majiyar ta ce nan take aka karbi jakarsa aka sa a cikin motar da take lodi, mutum wanda ke sanye da doguwar riga na tsaye da sauran jama’ar da ya samu a wurin, sai ya tayar da bam din da yake jikinsa. Bam din ya tarwatsa jikinsa ya cire kansa tare da tarwatsa naman mutanen da suke tare da shi, inji majiyar.
Shi kuma bam na biyu wanda ya tashi a kofar tashar Bauchi Road bayan ’yan mintina da tashin na farko, wadanda abin ya faru a kan idonsu sun shaida wa wakilinmu cewa wata mata ce da ta fake wa ruwan sama da ake yi ta tayar da shi. Suka ce nan take bam din ya hallaka ta tare da wasu mutanen da ke waje.
Malam Shu’aibu Haruna Abdul’aziz daya daga cikin wadanda suka ji rauni a harin, ya shaida wa wakilinmu cewa “Ina zaune cikin Keke NAPEP a bakin tasha ana yayyafi, sai na ji karar wani abu ya tashi da na daga kai, sai na ga karafuna suna ta fado mana suna yayyaka mu, shi ne aka dauke muzuwa asibiti.”
Babbban Daraktan Asibitin kwararru na Filato Dokta Filimon Gwolwa ya ce sun karbi gawarwakin mutum 17 da suka rasu a harin. Ya ce sun kwantar da mutum 14 da suka samu raunuka a hare-haren.
Da aka tuntubi kakakin rundunar tsaro mai aikin samar da zaman lafiya a Jihar Filato (STF), Kyaftin Ikedichi Iweha kan hare-haren ya tabbatar da faruruwarsu, sai dai ya ce mutum 13 ne suka rasu a hare-haren.
Da yake zantawa da wakilinmu kan hare-haren da ake kaiwa a kasar nan shugaban kungiyar masu shayi ta kasa Alhaji Shu’aibu Abubakar da ke zaune a jikin tashar Bauchi Road, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi su tashi tsaye su shawo kan wannan matsala.
Ya ce wadannan kashe-kashe sun yi yawa, don haka ya zama wajibi gwamnati ta tashi ta kare rayukan al’ummar kasar nan, kuma ya yi kira ga jama’a su sanya ido ga mutanen da suke shige da fice a dukkan wuraren da suke zaune.
Shi ma a zantawarsa da wakilinmu shugaban kungiyar direbobi ta kasa NURTW reshen tashar motar kofar shiga Jami’ar Jos Alhaji Muhammad Rabi’u ya yi Allah wadai da harin da aka kai musu, ya ce, “Muna zaune da ’yan uwanmu ba su ji ba, ba su gani ba haka kawai wani ya zo ya kashe kansa ya kashe su, a gaskiya mun yi matukar bakin ciki da faruwar lamarin.”
Ya yi kira ga jama’a su rika sanya ido ga mutanen da suke kai da komowa a masallatai da coci-coci da kasuwanni da tashoshin mota, “Yanzu lokaci ya wuce da jama’a za su zauna su ce sun yarda da kowa, saboda wannan hali da muka shiga,” inji shi.