Yadda mahara suka jefa bam a ofishin ‘yan sanda a Imo
Maharan sun jefa bama-bamai cikin ofishin ‘yan sanda amma ba su yi nasarar tashin su ba.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Imo ta yi nasarar dakile wani hari da wasu mahara suka kai a caji ofis na yankin Dikenafai da ke Karamar Hukumar Ideota ta Kudu.
Kakakin ‘yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, ya bayyana yadda maharan suka yi dandazo suka afka wa ofishin ‘yan sandan cikin daren ranar Alhamis, inda suka jefa wasu abubuwan fashewa.
- Wane sakamako ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda zai haifar?
- Rikicin Mali: Jonathan ya ziyarci Buhari
Abattam ya ce “A ranar 06/01/2022 da misalin karfe 2 na dare suka kai hari kan caji ofis din Karamar Hukumar Ideota ta Kudu, suka dinga harbi a iska sannan suka jefa bama-bamai.
“Sai dai an aike da karin jami’an tsaro wadanda suka cimma maharan sannan suka yi dauki ba dadi da su. Hakan ya sa da yawansu suka tsere zuwa daji da raunuka.
“Kazalika, ba a yi asarar makamai ba kuma ba su yi nasarar tashin bama-baman da suka jefa caji ofis din ba,” a cewar sanarwar da ya fitar.
Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kadan bayan harin da wasu mahara suka kai fadar basaraken Amaifeke, Eze E.C. Okeke, a Karamar Hukumar Orlu.