Yadda mahara suka kwace barikin soja suka sanya tutarsu

Wasu ’yan bindiga sun kai hari ga barikin soja na Bama da ke Jihar Borno a safiyar Juma’ar da ta gabata inda suka samu nasarar kwace barikin tare da sanya tutocinsu bayan sun kashe sojoji da dama da kuma iyalansu.Wata babbar majiyar tsaro wadda ta shaida wa Aminiya haka ta ce daruruwan mayakan Boko Haram […]

Yadda mahara suka kwace barikin soja suka sanya tutarsu
Yadda mahara suka kwace barikin soja suka sanya tutarsu

Wasu ’yan bindiga sun kai hari ga barikin soja na Bama da ke Jihar Borno a safiyar Juma’ar da ta gabata inda suka samu nasarar kwace barikin tare da sanya tutocinsu bayan sun kashe sojoji da dama da kuma iyalansu.
Wata babbar majiyar tsaro wadda ta shaida wa Aminiya haka ta ce daruruwan mayakan Boko Haram sun kaddamar da hari kan barikin bataliyar tankokin yaki ta 202 da ke nisan kilomita 78 daga Maiduguri a Jihar Borno.
Majiyoyin soja sun ce ’yan ta’adda “da suka fito daga mazaunansu a kan iyakar Najeriya da Kamaru suka kaddamar da harin ta biyowa ta hanyar garin Banki.”
Wata sanarwa daga Daraktan Labarai na Hedkwatar Soja, Manjo Janar Chris Olukolade, ta ce: “An yi amfani da manyan makamai kamar na harbo jiragen sama da bindigogin harba roka a yayin harin da ya dauki awanni da dama.”
Ya kara da cewa, “sojojin kasa da na sama sun mayar da martani ga maharan kuma suna bin sawun maharan.”
Ya ce, za a bayyana adadin wadanda suka rasu bayan sojojin sun kammala “kange yankin da bincike.” Kuma Shugaba Jonathan ya kira taro da manyan hafsoshin tsaro kan harin da aka kai wa barikin.
Sai dai wata babbar majiyar tsaro ta shaida wa akilinmu ranar Asabar cewa za a iya bayyana harin da “Mafi muni da aka taba kaiwa kuma mafi girma da aka kai wa matsugunin sojoji.”
Wakilinmu ya samu bayanin cewa maharan wadanda daruruwa ne sun zo ne a jerin gwanon motoci kafin su yi kawanya ga barikin suna harba manyan makamai. “Wadannan ’yan ta’adda sun yi kaca-kaca da barikin sannan suka fice daga cikinsa a kashin kansu da tsakar rana,” inji majiyar.
Ya ce, zuwa jirgin yaki daga Yola ya ba wasu sojojin da aka rutsa a harin damar tsira a daidai lokacin da ’yan ta’addan ke tafka ta’asarsu.  
Wata majiya ma ta ce, maharan sun yanyanka wasu da suka rutsa da su, inda ta kara da cewa daya daga cikinsu wanda Kyaftin ne an kashe shi ne a filin fareti na barikin. Ya ce an ruguza gine-gine da dama a yayin harin.
Wata majiyar tsaro ta ce, sojojin da suke kasa a lokacin sun gaza yin komai, kuma an kunyata su inda suka zargi Gwamnatin Tarayya da hannu a cikin lamarin.
“Babban abin bakin ciki shi ne a lokacin da aka sanar da manya a Abuja game da abin da ke faruwa a Bama, ba su nuna damuwa ba. Maimakon haka sai suka ci gaba da gudanar da bikin makala karin girma ga manyan jami’an soja da Shugaban kasa ya kara wa girma a wurin shakatwar manyan hafsoshi na rundunar da ke Abuja,” inji majiyar.
Wata majiyar ta kara da cewa, “Wasu daga iyalan sojojin sun bace – mai yiwuwa ’yan Boko Haram ne suka tafi da su, kuma an lalata kayayyaki da dam.”   
Bayanai sun ce mayakan Boko Haram sun harba roka ga wani jirgin soja mai saukar ungulu da ke dauke da kwamndan birged na 21 na birged din sojojin tanka na sojojin Najeriya lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Bama a ranar Juma’a domin ganin harin da aka kai wa barikin.
“Abin bakin ciki, an harbi jirgi mai saukar ungulu da ya fito daga Maiduguri dauke da kwamandan birged inda tilas ya juya. Kuma ya kama wuta a lokacin da yake sauka, sai dai an yi kokarin kashe wutar ba tare da wani ya ji rauni ba,” inji majiyar.
Harin na ranar Juma’a ga barikin ya zo kasa da mako uku da kai irin wannan shiryayyen hari ga barikokin sojan kasa da na sama a garin Maiduguri inda a ciki aka lalata jiragen soja biyar.
A ranar Litinin da ta gabata hukumomin tsaron kasar nan sun ce rundunar soji na kokarin kwato mata da ’ya’yan sojojin da ’yan bindigar suka kwashe a harin da suka Bama.
Kakakin Hedkwatar Soja Manjo Janar Chris Olukolade ya ce sojojin sun kashe akalla mahara 50 a fafatawar da suke yi ta neman kwato iyalan sojojin.