Yadda mai bakar fata za ta yi kwalliya

Wasu daga cikin mata ba su cika sha’awar kwalliya ba, musamman masu bakar fata. Bakar fata ba ta cika fitar da ado a fuskar mace ba, saboda launinta ko rashin sanin irin fandeshi da hoda da kuma jan-bakin da ya dace da ita. A wannan makon mun kawo hanyoyi masu sauki da mai bakar fata […]

Yadda mai bakar fata za ta yi kwalliya

Nau’ikan fandeshin da mai bakar fata za ta shafaWasu daga cikin mata ba su cika sha’awar kwalliya ba, musamman masu bakar fata. Bakar fata ba ta cika fitar da ado a fuskar mace ba, saboda launinta ko rashin sanin irin fandeshi da hoda da kuma jan-bakin da ya dace da ita. A wannan makon mun kawo hanyoyi masu sauki da mai bakar fata ce za ta yi amfani da su wajen inganta kwalliyarta. Amfani da wadannan hanyoyi za su sanya kwalliya ta bayyana.
Fandeshi: Ya kamata mai bakar fata ta san irin fandeshi da ya dace da kalarta kafin ta saya. Yana da kyau idan mai bakar fata za ta sayi fandeshi, ta sayi kalar da ta fi  fatarta haske kadan. Za ta iya amfani da buroshin fuska don shafa shi, amma hanyar da ta fi sauki ita ce amfani da yatsu wurin shafawa.
Hoda: Yawancin masu bakar fata sukan yi fama da gumi da ko maikon fuska. Amma akwai abubuwan da suke taimakawa wurin rage gumi da maikon fuska, wanda kuma mun yi bayaninsa a makon da ya gabata. Yana da kyau idan mai bakar fata ta tashi sayan hoda, ta sayo mai kyau kuma kada tabi arha. Ana so ta shafa hoda kalar fatarta ba wanda take dauke da kalar dorawa ba. Idan aka sayi hoda mai tsada takan maye gurbin fandeshi. Muna ba mata shawarar sayar hoda mai tsada don za ta kara wa kwalliyarsu armashi.
Blush: Mun san za a yi mamaki idan mun ce mai bakar fata za ta iya sanya blush. Lallai za ta iya domin blush zai kara mata kyawu. Ba kowace irin blush mai bakar fata za ta sanya ba sai mai launin ja ko kusa da ita.
Jan-baki: Yin amfani da launika daban-daban na inganta kwalliyar mace, amma shin an san wacce irin kala ta dace da mai bakar fata? Idan mai bakar fata ta yi amfani da jan-bakin da bai dace da kalarta ba, ana ganinta za a ga kamar ba ta da lafiya ko ciwon sanyi ya kama ta. Za a iya amfani da jan janbaki, ko mai kama da ruwan kasa. Bayan haka, sai a dora wa labban ‘lip gloss’ don su yi sheki.
Gazal da adon ido: Tun da fatar baka ce, za a iya sanya ‘eye shadow’ mai yawa a kan ido. Za a iya shafa kalar zinare ko pink ko silber. Bayan an gama, sai a sanya gazal mai sheki a ido domin kara fito da kwalliyar.