Yadda mai ciki ta botsare wa masu garkuwa da mutane

A kwanakin baya ne wasu iyalai mai mutum 11 wadanda suka fito daga wani bikin aure suka fada hannun masu garkuwa da mutane a hanyarsu ta dawowa Abuja, inda 10 daga cikinsu suka shafe kwana shida a hannunsu a wani daji da ke Jihar Kaduna.  daya daga cikinsu wadda mai juna biyu ne ta turje […]

Yadda mai ciki ta botsare wa masu garkuwa da mutane

A kwanakin baya ne wasu iyalai mai mutum 11 wadanda suka fito daga wani bikin aure suka fada hannun masu garkuwa da mutane a hanyarsu ta dawowa Abuja, inda 10 daga cikinsu suka shafe kwana shida a hannunsu a wani daji da ke Jihar Kaduna.  daya daga cikinsu wadda mai juna biyu ne ta turje inda ta ce ba za ta bi masu garkuwa da mutanen ba duk da barazanar kisa da suka yi mata. A miniya ta zanta da daya daga cikin iyalan kan halin da suka shiga:

 

Mene ne sunan malamin?

Sunanana Magaji Ali ina da zaune a yankin Birnin Tarayya, Abuja

 

Yaya aka yi kuka fada hannun masu garkuwa da mutane?

Wannan abu ya faru da mu ne a ranar wata Laraba da misalin karfe 2 na dare a wani wuri da ake kira Abdu-Jongom kafin a iso kauyen Rijana idan aka fito daga Kaduna lokacin da muke dawowa daga wurin biki a kauyenmu. A baya mun so mu kwana a Kano a wurin wadansu ’yan uwanmu amma saboda muna da yawa sai muka sauya shawara muka ci gaba da tafiyar maimakon dora musu larura, tunda dai motarmu ce ba ta fasinja ba. Kafin mu kai inda masu garkuwar suke mun hadu da wani shingen sojoji sun tsayar da mu suka dudduba mu suka ce mu wuce. Bayan rabuwarmu da su ba mu yi tafiyar kilomita 5 ba, sai ga wani shingen, bayan mun wuce wata gada. Suka haska mana fitila na nan muka tsaya, shi ke nan sai muka rage gudun mota, bayan mu wuce mutum na farko da na biyu gaba dayansu da manyan bindga, na ukun sai ya yi mana tsawa, muna tsayawa a inda yake sai ya tunkaro direba ya nuna masa bndiga ya ce kashe motar. Kafin a ce wani abu sai kawai suka bubbude kofofin motar kuma sai ga wani gungu ya bullo sun kewaye mu ba su ma bar wani ya sauka da kansa ba sai suka jawo nu zuwa waje. Mu 11 ne manya 5 ni da abokina sai matata da ’yan uwana mata 2 sai kuma ’ya’yana 4 da na wani abokina da na rike sai kuma ’yar wata ’yar uwata. Mu manya kowannenmu yana rike da yaro. Sai na tambayesu me ke faruwa sai wadanda suke rike da adduna a cikinsu suka shiga dukanmu da adduna ba sara ba, suna jan mu zuwa cikin daji. Nan muka bar motarmu tare da mabudinta a jiki. Da farko na nemi su karbi kudin da ke hannunmu su bar mu amma sai suka ce ai su ba ’yan fashi ba ne satarmu suka yi. A nan na gane cewa masu garkuwa da mutane ne. Nan suka yi ta harbe-harbe na razanarwa sannan suka karbi wayoyinmu da kudin muka dunguma cikin daji wadansu daga cikinmu babu ko takalmi a kafarsu, ga kaya ga itatuwa muka yi ta tafiya wajen awa 5 kafin muka tsaya da misalin karfe 7 na safe a wani zango da wadansu abokan harkarsu suke. Su ma suna tare da akalla mutum 10 da suka yi garkuwa da su. Bayan mun yi karyawar safe sai aka hada mu muka yi ta bin daji haka nan.

Amma kafin nan daya daga cikinmu wata ’yar uwata ta nuna turjiya tun a farkon lokacin da suka kama mu ta nuna ita ba za ta iya tafiya ba, ta kwanta a kasa ta ce da su za ta haihu kasancewar tana da juna biyu sun buga sun buga, amma ta ce ba za ta iya tafiyar ba. Sun dora mata wuka a wuya suka ce za su fa yanka ta, amma sai ta ce musu ai ko sun bar ta a raye ma mutuwa za ta yi saboda cikin da take da shi. Daga nan sai suka dauko itace suka buge ta da shi amma ta ki tashi. Bayan nan ne sai suka bar ta a kwance a wajen suka tafi da mu. To daga baya ne ta bi hanya sai dai ita din ma kamar yadda ta yi mana bayani ba ta samu fitowa bakin hanya ba sai zuwa wayewar gari aka kai ta wajen wadansu sojoji da ke kan hanyar suka ka ita wani asibiti kafin aka sa ta a mota ya kai ta gida. Mu kuma aka yi ta tafiya da mu a cikin kungurmin daji, ba maganar tsayawa a wuri guda a tsawon kwana 6 da muka yi a hannunsu, inda za mu kwana daban inda za mu wuni daban ko ka daga kanka sama ba ka ganin komai sai dai duhun itatuwa ta yadda ko jirgi ne ya ratsa ta wajen ba zai iya ganin komai ba daga kasa sai dai kurmi kawai. Idan kuma an tashi tsayawa don hutawa ko cin abinci ko kwana idan karfe 9 na dare ta yi, sai dai a kan tsauni za a tsaya, inda hakan ke ba su damar yin waya da ’yan uwansu ko ’yan uwanmu da ke gida kan kudin fansa. Gari na wayewa kuma ko karyawa ba za a yi a wurin ba sai a matsa wani wurin tukuna sannan a tsaya a karya.

 

A yadda kuka fahimce su akwai alamar sun san dazukan ko dai suna tafiyar ce kawai?

A gaskiya bisa ga dukan alamu sun san dazukan. Dalili shi ne akwai ’yan uwansu da ke zuwa kan titi suna kawo musu abinci da wadanda ke sanar da su ta tsaunukan da suke idan suka kama wadansu inda za ka ji suna ambato wuraren da irin sunayen da suka ba su ckin harshensu na Fulatanci.

 

Yaushe suka fara magana da mutanenku?

Ai tun wayewar garin ranar da suka kama mu suka fara magana da su a tsaunin da muka yada zango na farko a lokacin da muke karyawa. Dama tun a lokacin da suka tsayar da mu suka amshe wayoyinmu da ’yan kudadenmu, suka kashe wasu wayoyin suka bar wasu. Da farko idan aka kira waya ko da sun dauka sai su ce ba mai wayar ba ne, daga baya ne suka ba mu damar yin magana ta waya tare da gargadin mu yi magana da wadanda za su ba da kudi kawai. Sun yi mana barazana iri-iri kamar na za su aikata lalata da matanmu su kuma kashe mu idan ba a ba da abin da suke nema ba a kan lokaci, sannan su sayar da sassan jikinmu inda suka ce kwayar ido daya kadai suna sayar da ita a kan Naira miliyan 20. 

 

Yaya batun abinci da kuma Sallah? 

A gaskiya muna samun abinci, suna tafiya tare da shinkafarsu da wake a wani zubin har da doya. Duk inda aka tsaya sai matanmu su dafa abinci a rarraba, ga nasu ga namu ga na mata da yara, idan bai isa ba ma sai su ce a sake dafa wata. Ruwa kuma duk dazukan da muka tsaya ba a rasa rafuka a can ake diban ruwan sha. Da farko mu suke sa wa mu dibo ruwa mutum guda a cikinsu na gaba wani na biye shi ko mai diban ruwa a tsakiya, to da wani babbansu ya zo ne sai ya ce kada su sake wannan kuskuren, su rika dibar ruwa da kansu, dafa abinci ne kadai za su bai wa matanmu. Dama shi mai gidansu ba ya zama a wajen da ake gadin jama’a kuma ba ya zuwa a lokacin nemansu, sai dai idan aka tashi biyan kudin fansa ne bayan an shirya sai a sanar da shi ya karbi kudin, ya kuma ba su umarnin su raka wadanda aka sake zuwa hanyar fita saboda mutum ba zai iya fita daga wajen ba idan ba sun yi masa jagora ba. Batun Sallah kuwa a lokacin da muka shiga hannunsu bayan wayewar gari mun nemi yin Sallah amma sai wani daga cikinsu ya ce ba a yin Sallah a wajen. Matsalar da aka samu kuwa ita ce wadanda muka samu a hannunsu wadanda sun yi kamar kwana 5 da su kafin zuwanmu, wani daga cikinsu yana yin waya da jama’arsa sai suka ji ana ba shi shawarar idan sun yi Sallah su rika yin addu’a kaza insha Allahu za su kubuta daga hannunsu. To da yake duk wayar da za ka yi dole sai ka sa ta a sifika kowa yana ji, sai suka ce to daga yau Sallar ma an hana. Bayan kamar kwana uku ne sai suka gaya wa dayanmu ka je ka wanke fuska mana, sai ya ce ina amfanin wanke fuska ba Sallah zai yi ba, sai ya ce ai ba a hana ku yin Sallah ba, su ma wadancan da aka hana akwai dalili. To daga nan ne muka fara Salla kafin daga baya kuma wadansu da aka sauya suka hana mu.

 

Yaya batun yawansu da kuma makamai?

A gaskiya suna da yawa duk da dai ba ka iya ganinsu gaba daya, sai dai a lokacin da suke kai mu wajen a kiyasce wadanda ke gabanmu kadai sun kai 20 wadanda  ke bayanmu ne ban san adadinsu saboda ba na ganinsu. Sannan yawancinsu suna dauke da manyan bindigogi irin AK 47, wadansu kuma kananan bindigogi ko adda, sannan gaba dayansu maza ne ba mata. Babu ruwansu da maganar jin rediyo bare karanta jarida illa ’yan kananan wayoyinsu da suke rike da su wadanda ba a ma iya shiga Intanet da su.  

 

Yaya batun fansa ko dai sake ku suka yi haka nan?

Tun muna da kwana daya a wajen suka fara magana da gida a kan kudin fansa. To a ranar da Allah Ya kaddari fitarmu sai suka sassauta kudin saboda su kansu sun saduda da lamarinmu suna ta cewa mu taya su da addu’a su daina wannan abin da suke yi, mu kuma yafe musu muna ganin a ranar ko da ba a biya kudi ba kamar za su bar mu, watakila addu’ar da aka rika yi ne a garin da muka baro da kuma inda muke da zama ta yi tasiri a kansu. Dama kuma duk wadanda muka same su da su sun sallame su sai mu kadai da kuma wani mutum daya da aka kamo bayan zuwanmu wajen muka rage. To bayan sun daidaita da gida wanda daga baya na samu labarin cewa an tsaya a kan Naira dubu 550, aka tura wani ya dauki shatar mai babur daga bakin hanya zuwa inda suka nemi ya kai kudin, daga nan sai suka tambaye shi wane irin kaya ya sa, ya ce iri kaza, sai suka ce mun gan ka ajiye kudin a kan abu kaza ka yi tafiyarka. Sannan bayan sun dauki kudin sun kirga sai suka yi wa masu tsaronmu waya cewa an biya kudinmu a sake mu. Sai wasunsu suka yi mana rakiya da misalin karfe hudu na yamma sannan da kamar karfe 9 na dare ta yi sai muka kwana a kan wani tsauni, bayan wayewar gari kamar karfe 7 muka ci gaba da tafiya kamar ta awa daya da su zuwa wata hanyar daji da manyan motoci da ke dauko itace suke bi. Daga nan muka rabu da su suka ce mu bi wannar hanyar har zuwa babban hanya inda muka yi tafiya ta kamar awa daya da rabi kafin muka isa aka kai mu inda sojoji suke. Dama kuma bayan sojojin sun ji harbin bindiga a daren da aka yi garkuwa da mu sun je inda muka bar motarmu suka ja ta zuwa sansaninsu, bayan sako mu suka ba mu motar muka shiga muka dawo gida.

 

Mun samu labarin cewa bayan an sako ku hukuma ta gayyaci ku zuwa Kaduna me ya faru?

Kasancewar sojoji sun yi bakin kokarinsu, domin tun a ranar da aka kama mu washegari mun ji harbe-harben bindiga sai dai ba mu sani ba, harbin na abokan masu garkuwan da mu ne ko na sojojin ne. Saboda su kansu masu garkuwar sukan harba bindiga idan suna neman junansu. Sai dai abu guda da muka kula da shi a lokacin shi ne; bayan sun ji harbin sun hanzarta barin wurin wanda hakan ya nuna ba harbin mutanensu ba ne na sjoji ne. To bayan dawowarmu inda muke da zama da kamar kwana daya, sai sojojin suka gayyace mu zuwa hedikwatarsu da ke Mando, Kaduna aka yi mana wasu ’yan tambayoyi a kan lamarin sannan muka dawo. Alhamdulillahi mun dawo gida lafiya ba tare da wanii rauni ba in ban da kumburar sawu da mutuwar farce ga wasunmu saboda sun tara jini ga tuntube a yayin tafiya cikin daji da kuma ta ka kaya domin wadansu daga cikinmu ba su da takalma a kafa lokacin da suka fito da mu daga cikin mota.