Yadda Mai digiri ta fara sayar da kosai
Chinenye Odili, ‘yar shekara 26 ce wadda ta ce ba za ta taba yin aikin albashi ba, domin sana’ar da fara na yin koko da kosai ya biya ta, inda har ta dauki masu taya ta aiki guda biyu. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Ya aka yi kika fara yin sana’ar yin koko da […]

Chinenye Odili, ‘yar shekara 26 ce wadda ta ce ba za ta taba yin aikin albashi ba, domin sana’ar da fara na yin koko da kosai ya biya ta, inda har ta dauki masu taya ta aiki guda biyu. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ya aka yi kika fara yin sana’ar yin koko da kosai da sauransu bayan kina da digiri kuma ke ’yar gata ce?
Chinenye: Sunana Chinenye Odili , kuma shekaruna ashirin da takwas da wata biyar da kwanaki goma shatakwas. Na yi karatun digiri ne a jami’ar Abuja, inda na karanci fannin akanta na kula da kudi. Na kuma yi mataimakiyar shugabar dalibai na kasa, ni ‘yar asalin jihar Anambra ce. Kuma na fara wannan sana’ar yin kosai ne ranar Juma’a 30 ga Janairu, 2015, ina sayar da kosai a shatale-talen da ke rukunin gidajen Zangon Daura a Kado, Abuja.
Da na kammala makaranta sai na ce ba zan zauna ina jiran a ba ni ba, sannan ina ta yin wasa da waya ba gaira ba sabar. Sai na gaya wa iyayena, sai suka ce min hankalina ya tabu. Sannan na je wurin tsohon Gwamna Chukwuemeka Ezeife na jihar Anambra na gaya masa, sai yi yi mamaki. Daga nan sai na dauki mai keke-Napep haya na ce ya yi ta yawo da ni har na iso nan shataletalen Sani Zangon Daura da ke Kado a Abuja, sai na fada wa Alhaji Tijjani Mai sayar da kayan lambu cewa ina son in rika yin kosai. Da yake na sanya kwat ne irin na ma’aikatan banki, sai suka yi mamaki. Na salami mai keke-Napepe na bashi Naira dubu uku. Mahaifina yana da digiri, mahaifiyata tana da dagiri, sai babana da wana suka ce min kai na ya kwance.
Aminiya: Ya kika yi kafin a fara sanini ki?
Chinenye: Na fito da asuba na baje kolin tuyar kosai. Sai wata mata ta zo da mota za ta ture min kaya, da na yi mata magana sai ta ce min ya nake sayar da abinci a daf da titi? Sai na ce ai ofishi na ke nan. Sai ta gyara fakin ta fito tace me nake nufi, sai nace ina sayar da kosai kafin in tafi aikin bautar kasa, don na gama karatun digiri. Wannan ya sa ita ta fara yi min ciniki, ta sayi kosai na Naira hamsin. Ranar farko na yi cinikin Naira 380, amma ban karaya ba. Ba a dade ba sai lokacin zabe ya yi, da dare ya yi sai aka ce in sanya kendir, na je na sawo.
Aminiya: Da jarin nawa kika fara?
Chinenye: Na fara da jarin Naira dubu biyar, na sayo rabin mudun wake da doya da jarka mai lita goma, na man gyada da sauransu. Dama ina da tukunyar gas wanda na yi makaranta da shi. Amma a yanzu a ranar aiki ina yin mudu hudu, kuma a ranar hutun asabar da lahadi ina aikata mudu shida da soyayyen ayaba da doya da kamu da madara.
Aminiya: Idan mutane sun zo da yawa ya kike yi da su?
Chinenye: Ina bin ka’ida a wannan ofishi nawa, don komin girman mukaminka, ko da jami’an tsaro ka zo, sai ka bi layi, don duk wanda ya fara zuwa shi nake fara sallama.
Aminiya: Kin gamsu da wannan sana’a da keki yi?
Chinenye: Eh! domin ina bude ofis da karfe biyar da rabi na safe kuma ina tashi ofis da karfe goma zuwa sha daya sai gobe. Amma a da sai in kai karfe biyu na yamma ban sayar ba. Don a da ina yin kwanaki uku ban yi cinikin Naira dubu daya ba. Sai da na yi wata daya da kwana uku kafin na fara cinikin Naira dubu daya a wuni.
Aminiya: Yaushe kika dauki mai taya ki aiki?
Chinenye: A yanzu ina da masu aiki su biyu. Ga daya kuna gani, daya kuma na aike ta kasuwa. Na dauki mai aika ta farko bayan na cika shekara daya ba kwanaki uku. Ta biyu kuma ranar Juma’ar da ta wuce. A shekarar farko ina yin cinikin Naira dubu goma sha uku, a wanna shekara ta biyu ina yin cinikin Naira goma sha shida a wuni. Amma ba zan fadi ribar da nake samu ba. A kwanakin baya, ma’aikatan banki sun zo sun yi min tayin in karbi bashi, amma na gaya musu cewa ba nason wani ya ba ni bashin jari, don ba na son wani ya zo ya tsare ni ya tayar min da hankali don bashi. Kuma ina son lokacin da za mu hadu da tsohon Gwamnan jiharmu Chukwuemeka Ezeife ni ma na kafu.
Aminiya: Wannan sana’a na tare da yin asubanci, ya kike yin wannan shiri?
Chinenye: Ina tashi ne da karfe uku na asuba in fara shirin gyara wake da sauran su. Sannan karfe biyar da rabi ina nan ofishin nawa ina sayar da kosai.
Aminiya: Idan aka ba ki aikin albashi za ki yi?
Chinenye: Ba zan yi ba, domin ina da burin fadada wannan sana’a sosai. Domin idan na tashi ina zuwa gida in kwanta in fara shirin gobe. Idan aikin albashi nake yi za a ajiye ni a ofis tun safe har dare, wanda ni wannan shiri bai yi min ba.
Aminiya: Ya ake kiranki a gida a yanzu?
Chinenye: Musamman ma babana, idan zai kira ni sai ya ce “Mai kosai.”
Aminiya: Mene ne kiranki ga matasa?
Chinenye: Su dubi abin da za su yi don su taimaka wa kansu. Kowa na da abin da zai iya yi don ya taimaki kansa, ba ya tsaya yana jiran a yi masa ba.
Aminiya: Ya bayanin yin bautar kasa?
Chinenye: Zan tafi a watan Yuli a kashi na biyu. Amma da ba don tilas ba ne da ba zan je ba, domin yin kosai ya fi min. Kuma ba zan bar wannan wajen haka ba, sai dai in bar masu aikina su ci gaba da aikin, sannan ni kuma idan na kammala in dawo in dasa daga inda suka tsaya. Ni ba zan iya yadda wata ta yi ba, ta gama digiri ta zauna a gida na shekaru biyu, sannan aka samar mata aikin Naira dubu ashirin da biyar a wata. Wasu kuma sai sun sha wuya sannan su ce sun fara koyon girki, ko yin sarka da rini. Ni kam na yi gaba. Bai dace matasa su zauna ba sa komai tun daga safe har dare ba sai wasa da waya, ni na wuce nan.
Aminiya: Wane kalubale kike samu?
Chinenye: Jami’an tsaftace muhalli da ake cewa AEPB sun taba kwashe min kaya, amma na yi tsayin daka su ka ba ni abuna. Bayan kawanaki sai suka zo wai in ba su kyauta, sai na ce idan na je kasuwa biya nake, su ma duk mai son kayana ya biya. Sannan wani ya taba damfara ta ya ba ni takardar Naira dubu daya ta jabu. Burina shi ne in dauki ma’aikata da yawa aiki nana gaba.
Aminiya: Me yake sanya ke ki murna?
Chinenye: Ina da masu sayen kosai da sauransu dake zuwa daga nesa, watau Maitama da Asokoro da Apo da Gwarimpa da suransu. Kuma wani ne ya ce in rika yin koko, yanzu sati uku ke nan da na fara, sai kuma wani ya ce in rika sayar da madara, sai na fara. Da ina da benci, yanzu na sa kujerun roba da lema don inganta wurin. Ina sai da kamu Naira hamsin, kosai Naira hamsin, kuma idan mutum na son madara, akwai na ruwa, akwai na gari.