Yadda mai tallan kifi ya sayar da zinaren sata na N60m a Abuja

Rundunar ta ce za ta gurfanar da su a kotu da zarar ta kammala bincike.

Yadda mai tallan kifi ya sayar da zinaren sata na N60m a Abuja

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja ta kama wasu mutum uku da ake zargi da fasa wani gida tare da sace zinare da wasu kayayyaki masu tsada a Abuja.

Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi ne, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

An kama mutanen ne bayan wani bincike da tawagar Binciken Bayanan Sirri (IRT) ta gudanar, wanda ya gano wadanda ke da hannu a laifin.

Bincike ya nuna cewa babban wanda ake zargi yana sana’ar sayar da kifi a Kasuwar Kifi ta Kado da ke Abuja.

Sanarwar ta ce “waɗanda ake zargin sun yi wa gidaje uku fashi a unguwar Lugbe, kafin su shiga na huɗu sun yi amfani da wani ƙarfe wajen banƙara tagar gidan inda ta nan suka samu damar shiga gidan.

“Suna shiga gidan, kai-tsaye suka shiga binciken abin da za su uya sacewa.

“A lokacin da suke lalube, sai suka hangi wani akwati a ajiye, nan take suka ɗauka suka tafi da shi.

“Sun yi amfani da guduma wajen buɗe akwatin, inda suka samu kuɗi, takardu, da zinare a ciki.

“Babban wanda ake zargin, ya kira mai saye sannan ya sayar da kayan satar, kan kuɗi Naira miliyan 60,” a cewar sanarwar.

Rundunar ta ce da zarar ta kammala bincike za ta miƙa su zuwa kotu domim girbar abin da suka aikta.