Yadda makabarta ta koma wajen kashi da zubar da shara a Abuja

Gundumar Utako da ke Birnin Tarayya Abuja na cikin wurare kalilan da suka rage a kwaryar birnin da ke da kananan gine-gine da ba na zamani ba. ’Yan kabilar Gbagyi daya daga cikin ’yan asalin yankin birni, su ke sarauta a yankin da kuma fara zama a bangaren gundumar da ake kira da kauyen Utako, […]

Yadda makabarta ta koma wajen kashi da zubar da shara a Abuja

Maqabartar Utako da a yanzu take kewaye da manyan gidaje

Gundumar Utako da ke Birnin Tarayya Abuja na cikin wurare kalilan da suka rage a kwaryar birnin da ke da kananan gine-gine da ba na zamani ba. ’Yan kabilar Gbagyi daya daga cikin ’yan asalin yankin birni, su ke sarauta a yankin da kuma fara zama a bangaren gundumar da ake kira da kauyen Utako, kuma a matsayin wurare kalilan da shirin sake matsuguni ga ’yan asalin yankin Abuja da ke cikin birni da rusa kananan gine-gine, bai shafa ba.

Wakilin Aminiya ya ziyarci yankin wanda ke da tazarar kamar kilomita 1 daga Shatale-talen Bega, inda ya gano wani abin da ya saba da zamantakewar jama’a da ke faruwa a wurin, inda ya tarar ana yin kashi a makabartar da ake binne mazauna yankin kuma ake zubar da shara a ciki. Hakan na faruwa ne, kamar yadda bincike ya gano a dalilin rashin tanadin makewayi a mafi yawan gidajen  da ke yankin.

Bincike ya gano cewa duk da cewa akwai gidajen wanka da na ba-haya na kudi a unguwar, wadansu na karauce wa wuraren saboda jin nauyin dan abin da ake karba,  yayin da wadansu kuma ke aikata hakan ne a dalilin ba za su iya yin ba-haya a ginanne wuri ba sai a fili kamar yadda suka saba kaka-da-kakanni. Haka nan bayanai sun ce daga cikin masu yin ba-haya a makabartar akwai masu aikin tasi-tasi da hanya ke biyo da su ta wurin, inda suke tsayar da motocinsu a lokacin da ba su dauke da fasinja, su kutsa cikin makabartar su yi ba-haya.

Wadansu mazauna kusa da wurin da masu gudanar da sana’a da Aminiya ta zanta da su, sun koka a kan lamarin, inda suka ce warin ba-haya da ke tasowa daga makabartar na damunsu; musamman ma a lokacin damina.

Yunkurin jin ta bakin Dagacin Utako Malam Abdullahi Isa Nyaminu bai samu nasara ba, inda ya ce hukuma ta hana su zantawa da ’yan jarida a kan al’amuran al’umma saboda haka sai ya shawarci wakilinmu ya tuntubi Sarkin Garki, wanda yankin ke karkashin masarautarsa.

Sai dai wani jagoran al’umma da ya bukaci a sakaya sunansa ya koka cewa a baya sun kai korafi ga gwamnatoci da suka gabata a Karamar Hukumar Birni da Kewayen Abuja (AMAC) kan a taimaka a killace musu makabartar ba tare da nasara ba. Kuma ya ce sun tuntubi Hukumar Kare Muhalli ta Abuja (AEPB) wadda ke da alhakin magance abin da ya shafi shara da sauran al’amuran muhalli a kan matsalar, amma a cewarsa sai hukumar ta shawar ce su da su rika kai mamatansu zuwa babbar makabartar Abuja da ke Apo.

Da aka tambaye shi ko me ya sa ba su bi umarnin hukumar ba sai ya ce “Waccan makabartar an yi ta ce saboda baki, mu da muke ’yan kasa ba yadda za mu kai mamatanmu wajen mu binne su, wannan ya saba da al’adarmu” inji shi. Ya kuma yi korafi a kan zargin sauya sunan yankin daga “Kutako” da ke nufin babban dutsi, da ya ce masu tsara birnin Abuja suka yi zuwa sunan yanzu wato Utako, inda ya ce sun yi ta korafi a kan lamarin amma ba tare da an ji kokensu ba.

Da yake ba da tarihin dutsin na “Kutako” dattijon ya ce wajen har yanzu haka na matsayin wajen bautarsu da suke garzayawa su nemi biyan bukata a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Haka ya yi bayani a kan wani abin da ya ce ya faru a lokacin da masu aikin titin da a yanzu haka ake kira Arab Junction suka karaso wajen da aikinsu.

Ya ce “Mun bukaci su jinkirta yin aikin har sai mun ba da baiko tukuna amma suka yi biris da umarnin, sai ga shi injin fasa dutsensu ya makale a wajen. Bayan kwana 4 ba tare da nasarar fitar da shi ba ne, sai suka garzaya wajen shugabanmu tare da bayyana nadamarsu. “An karbi tubarsu sannan nan take injin ya tashi suka ci gaba da aiki,” inji shi.

Ya ce a lokacin da aikin makarantar firamare ta yankin ya tashi sun bukaci a guji sanya dutsen a harabarta saboda ba za su lamunci neman sai an bude musu kofar makaranta ba a duk lokacin da bukatar yin bautar dutsen ta bijiro, inda hukuma ta amince, kamar yadda ya yi bayani.