Yadda makafi uku, wa da kanne ke nikan alabo

Wadansu makafi a jihar Oyo  ba su bari makantar da suke fama da ita ta durkusar da su sun zama nauyi ga al’aumma ba, domin kuwa sun tashi tsaye wajen neman abin rufin asiri ta hanyar amfani da injin nika suna samar da garin alabo.Su dai wadannan makafin magidanta ne su uku ‘yan uwan juna […]

Yadda makafi uku, wa da kanne ke nikan alabo

Wadansu makafi a jihar Oyo  ba su bari makantar da suke fama da ita ta durkusar da su sun zama nauyi ga al’aumma ba, domin kuwa sun tashi tsaye wajen neman abin rufin asiri ta hanyar amfani da injin nika suna samar da garin alabo.
Su dai wadannan makafin magidanta ne su uku ‘yan uwan juna (uwa daya uba daya) da suka kamu da cutar makanta a lokuta daban daban a cikin shekaru 12 da suka gabata. Kafin su kamu da wannan ciwo, kowannensu yana da aikin hannu da yake yi domin dogaro da kai.
Wadannan mutane da ke zaune da iyalansu da mahaifinsu a garin Ago-Are cikin karamar Hukumar Atisbo a Jihar Oyo, ba su bari makantsar ta jefa su yin barace-barace ba, a maimakon haka sai daya daga cikinsu ne ya sayo musu injin yin surfe da nika busassun doya da rogo da ake mayar da su garin Alabo da ake yin tuwon Amala da shi.
 Duk da namijin kokarin da suka yi a matsayinsu na nakasassu ba su taba samun wani tallafi daga mahukunta a Jihar Oyo ba. Amma a shekarun baya wani Shugaban karamar Hukumar Atisbo, ya taba yi musu alkawarin ba su tallafin kudi fiye da naira miliyan daya, wanda har zuwa yanzu shiru kake ji.
Wakilinmu ya yi tattaki zuwa garin na Ago-Are, mazaunin wadannan makafi a inda ya ga yadda suke gudanar da aikin nasu. Duk da yake ba gani suke yi ba, su ne suke kunna wutar inji da hannunsu, su lalubo bel su sanya shi a mazauninsa, sai dayansu ya zauna yana surfe da nika a cikin inji, shi kuma dayan ya sanya hannu yana tabawa domin gano laushin garin. Har ila yau, idan wata matsala ta samu su ne suke kwance wannan na’ura su yi daidai da ita su gyara ta ci gaba da aiki. Shi kuma na ukunsu yana cikin shaguna guda uku da aka tara buhunan busasshiyar doya da masara da yake sayarwa.
 A tattaunawar da wakilinmu ya yi da su, babban yayan nasu mai suna Muhammadu Sa’adu Isyaka, mai shekaru 53 da haihuwa, cewa ya yi, ”Asalinmu daga garin Oyo muka fito, amma a nan garin Ago-Are, aka haife ni kuma a nan na fara karatun firamare har zuwa aji uku kafin iyayena su dauke ni zuwa garin Yawuri inda na kammala zuwa aji shida a can. An yi kokarin ganin na ci gaba da karatu a sakandare amma ni na ki yarda, sai suka kai ni wajen koyon aikin rediyo inda na yi shekara daya aka dawo da ni garin Ago-Are na ci gaba da koyon gyaran rediyo a garin Shaki. Bayan shekaru hudu da iya aiki sai na fara cin gashin kaina a shekarar 1981. kanena mai suna Suleiman, shi ne ya fara
Cigaba a shafi na 4