Yadda Makarfi ya zama halastaccen shugaban PDP
Aranar Larabar da ta gabata ce Kotun Qoli ta Qasa ta tabbatar da Tshohon Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi a matsayin halastaccen Shugaban Babbar Jam’iyyar Adawa ta PDP. Wannan hukunci ya warware doguwar taqaddamar da ta shiga tsakanin manyan jigogin jam’iyyar tsawon lokaci Rigimar wacce ta shafe kimanin shekara biyu akan shugabancin jam’iyyar wacce […]

Aranar Larabar da ta gabata ce Kotun Qoli ta Qasa ta tabbatar da Tshohon Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi a matsayin halastaccen Shugaban Babbar Jam’iyyar Adawa ta PDP. Wannan hukunci ya warware doguwar taqaddamar da ta shiga tsakanin manyan jigogin jam’iyyar tsawon lokaci Rigimar wacce ta shafe kimanin shekara biyu akan shugabancin jam’iyyar wacce ta shafe shekara 16 tana jan ragamar kasar karashin shugabanni daban-daban. Lamarin da ya raba kawunan ‘ya’yan jam’iyyar a sassan najeriya daban-daban. Rahotanni sun bayyana cewa jami’an vangaren Ahmed Makarfi da suka halarci zaman kotun, sun nuna farin cikinsu ga hukuncin. Haka kuma tuni wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar suka yi maraba da hukuncin.
Haka zalika Tsohon Kakakin Jam’iyyar, Cif Olisa Metuh ya bayyana cewa babu wanda ya yi nasara ko ya fadi sakamakon hukuncin, yana mai cewa dama ce aka samu ta a hadu tare a mance da bambance-bambancen dake tsakani domin inganta jam’iyyar anan gaba.
A wata sanarwa da ya fitar, ya ce wajibi ne su sake bude kofa ga dukkan ‘yan Najeriya da ke son ganin tsarin demokuradiyya ya tabbata.
A wani vangare kuma wanda ya ja hankalin al’umma shi ne yadda babban jigon da ke goya wa Ali Madu Sheriff baya, kuma tsohon mai baiwa shugaban qasa shawara kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak, jim kadan bayan hukumcin kotun qolin, ya ce sun gamsu da hukuncin da kotun ta yanke kuma za su dauki kaddara