Yadda makiyaya a Yobe ke asarar dabbobinsu saboda bullar cuta

Wata bakuwar cutar dabbobi ta bulla a wasu yankunan Jihar Yobe, inda take addabar kafafu da bakin shanu, wannan ya sanya makiyayan jihar ke cikin fargaba. Inda aka fi samun cutar sun hada da unguwannin da ke Kananan hukumomin Jakusko, Fune, Nangere, Tarmuwa, Potiskum, Damaturu, Fika da Karamar hukumar Gulani duk a jihar. Makiyayan da […]

Yadda makiyaya a Yobe ke asarar dabbobinsu saboda bullar cuta

Yadda makiyaya a Yobe ke asarar

Wata bakuwar cutar dabbobi ta bulla a wasu yankunan Jihar Yobe, inda take addabar kafafu da bakin shanu, wannan ya sanya makiyayan jihar ke cikin fargaba.

Inda aka fi samun cutar sun hada da unguwannin da ke Kananan hukumomin Jakusko, Fune, Nangere, Tarmuwa, Potiskum, Damaturu, Fika da Karamar hukumar Gulani duk a jihar.

Makiyayan da cutar ta addabi dabbobinsu sun bayyana wa majiyarmu cewa, an fara samun bullar cutar ne lokaci kadan da daukewar damina wanda bullar cutar ta yi sanadin rasa dabbobi da dama

Shugaban Kungiyar makiyaya ta ‘Kullen Allah Cattle Breeders Association (KACRAN)’ na cibiyar Fika, Muhammad Alhaji Hassan, ya ce shi kansa ya yi asarar shanu uku sanadiyyagr bullar cutar.

Alhaji Hassan ya ce, cutar da take addaban kafafu da bakin dabbobi wanda ake kira da ‘boru disease’ an shigo da cutar cikin jihar ne ta hanyar shigo da wasu fararen shanu daga kasashen Chadi da Kamaru inda suka biyo ta cikin jihar Adamawa. Ban taba ganin wannan cutar a jikin rakuma ba. Cutar ta fi kama kafafun da bakin shanu.

Ya kuma ce, bullar cutar cikin kankanin lokaci ta kashe dabbobi a garuruwan Maluri da Gudi da Manawaji da sauran unguwanin Fulani.

“Wata daya daya gaba ta dabbobinmu sun ta fama da cutar huhu yanzu kuma ga wannan sabuwar bullar cutar ‘boru’ mai kama kafafu da baki. Wannan yasa Gwamnatin jihar ta baiwa likitocin dabbobi dama bin hanyoyin dakatar da yaduwar cutar a fadin jihar”, in ji Alhaji Hassan.

In banda an yi rigakafin dabbobi a farkon shekarar nan da cutar ta yi mummunan barna saboda saurin yaduwar cutar.

Wani shugaban makiyaya a garin Jakusko, Lamido Manu ya ce, an samu bullar cutar a yankin amma a yanzu babu rahoton mutuwar dabba da aka sanar.

Manu ya ce, bullar cutar dabbobi na kawo wa harkokin kasuwancinsu nakasu da rage darajar sana’arsu.

Manu ya kara da cewa, kiwon shanu shi ne muhimmin sana’ar mu, amma a yanzu ba ‘a sayan dabbobi da shan madarar shanu. Abu ne mai kyau a yanzu da aka yi saurin bin hanyoyin magance cutar a cikin lokaci.

Shugaban Kungiyar Kulen Allah Cattle Rearers Association (KACRAN) na kasa Khalil Muhamma Bello ya ce, sun samu rahoton bullar cutar dabbobin a wasu yankunan jihar, amma yanzu haka sun sanarwa da sashin shirin ci gaban makiyaya na jihar Yobe (PLDP) don kai agaji ga yankunan da cutar ta bulla.

“Ina farin cikin sanar da ku cewa, jama’ar yankunan sun fara kabar magunguna a ofishin cibiyoyin fadin jihar. Don sanar da koken makiyayan yayin da za a hada su da ofisoshi mafi kusa, don basu magungunan cutar”.

Bello ya ce, mafi yawan manoma na jinkirin sanar da rahoto ga gwamnati idan an samu bullar cutar dabbobi wanda za a iya yin rigakafi a karshe su koma su na yi wa dabbobin magungunan gargajiya.

A lokacin da cutar ta bulla wasu makiyaya sun fara shafa irin bagaruwa a wuraren da cutar ta take musamman a baki da kafafu. Ana su tunanin hakan shi ne rigakafin cutar boru, wannan yasa suka rasa dabbobinsu da dama.

Akan adadin dabbobin da suka mutu, an samu rahoton akalla dabbobi sama da 100 ne suka mutu a yankunan da cutar ta bulla. Ya kuma gode wa Gwamnatin jihar akan matakan gaggawa da ta dauka, don taimaka wa miliyoyin jama’ar da suke rayuwa da sana’ar su a jihar.

Shugaban shirin PLDP na jihar Yobe, Malam Mustafa, ya ce, an yi bude cibiyoyin bincike don dabbobin da suka kamu da cutar a kafafunsu da baki. An dai tabbatar da gwajin binciken cutar na kama baki da kafafu.

Manajan shirin ya ce, an shigo da cutar jihar ne ta hanyar shigo da wasu bakin dabbobi daga jihohin Adamawa da Taraba.

A yanzu haka hukumomi duk sun dauki matakan shigo wa jihar da bakin dabbobi a iyakokin jihar.