Yadda Man City ta lallasa Real Madrid a gida
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tasha kashi a hannun kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a gasar zakaru ta Nahiyar Turai da ci 2-1 a ranar Laraba. Man City, dai ta samu narasa ta hannun dan wasanta Gabriel Jesus, wanda ya zura kwallon farko da Madrid din ta ci ta hannun Isco. A nan […]
Manchester City da Real Madrid
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tasha kashi a hannun kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a gasar zakaru ta Nahiyar Turai da ci 2-1 a ranar Laraba.
Man City, dai ta samu narasa ta hannun dan wasanta Gabriel Jesus, wanda ya zura kwallon farko da Madrid din ta ci ta hannun Isco.
A nan ne Man City din tayi azama takara kwallo daya wanda ya bata nasara a bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida ta hannun dan wasanta na tsakiya Kevin De Bruyne.
Karon farko kenan da City din ta samu nasara a kan Real Madrid a gasar zakarun turai. Man City ta buga wasanni 5 da Madrid a gasar, a yayin da Madrid din ta doke ta sau biyu aka yi canjaras sau biyu.
Kociyan Man City din dai, Pep Guardiola, wanda tsohon mai horarwa ne a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, bai taba jagorantar kungiya zuwa filin wasa na Bernabeu ba ba tare da nasara ba.