Yadda manajana ya yaudare ni na sanya hannu akulob din Eklo na Beljiyam a shekarar 1988 -dahiru Sadi(1)

dahiru Sadi, shahararren dan kwallo ne da ke zaune a garin Kaduna.  Ya buga wa kulob da dama wasa a cikin gida da kuma waje.  Hasalima ya yi wasa a kasashen Beljiyam da Indonesiya da Malesiya kafin ya yi ritaya a shekarar 1997.  Yanzu haka shi ne Shugaban kungiyar da ke kare hakkin ’yan kwallo […]

Yadda manajana ya yaudare ni na sanya hannu akulob din Eklo na Beljiyam a shekarar 1988 -dahiru Sadi(1)
Yadda manajana ya yaudare ni na sanya hannu akulob din Eklo na Beljiyam a shekarar 1988 -dahiru Sadi(1)

dahiru Sadi, shahararren dan kwallo ne da ke zaune a garin Kaduna.  Ya buga wa kulob da dama wasa a cikin gida da kuma waje.  Hasalima ya yi wasa a kasashen Beljiyam da Indonesiya da Malesiya kafin ya yi ritaya a shekarar 1997.  Yanzu haka shi ne Shugaban kungiyar da ke kare hakkin ’yan kwallo a duniya reshen Najeriya.  Ya zanta da Aminiya a kan batutuwa da dama, ciki har da tarihin kwallonsa da kalubale da kuma nasarorin da ya samu kamar haka:

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?

dahiru Sadi: Sunana dahiru Sadi MFR. Tsohon dan kwallo, amma yanzu ni ne Shugaban kungiyar da ke kare hakkin ’yan kwallo ta duniya reshen Najeriya watau (President of Nigerian Players Union). Kuma har yanzu muna harkar kwallon, don ba mu daina yi ba amma a fannin kula da yadda ake tafiyar da shugabancin gudanar da kwallo, ba a matsayin koci ba. Akwai irin wannan kungiyar ta kare hakkin ’yan kwallo a duniya, to ni ne shugabanta na Najeriya. Kowace kasa tana da irin wannan kungiya, amma yanzu kimanin shekara biyar kenan da muka fara a Najeriya. Kuma mun samu amincewar Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da ta Najeriya NFF wajen kafa wannan kungiya. In ban da lalurar kafa da take damuna da yanzu haka ina Namibiya wajen taron kungiyar na yankin Afirka, amma sai na tura sakatarena. Sannan nan gaba kadan za a yi taro a matakin na duniya a Chile, kuma muna sa ran za mu halarta.

Aminiya: Yaya tarihin kwallon kafarka a ciki da kuma wajen Najeriya?
dahiru Sadi: Zan iya cewa ni mutum ne mai son zama a kulob daya, amma da farko na fara yin kwallo ne a kulob din Golden Stars karkashin kocin da ake kira NDA a Tudun Wada, Kaduna daga nan na koma KKD a karkashin horarwar Lawan Basko daga nan na wuce DIC da ke Kaduna inda daga baya ta koma Ranchers Bees duk a garin Kaduna. Daga nan bayan mun buga kofin kalubale watau Challenge Cup a tsakanin shekarar 1983 zuwa 1984 sai na koma kulob din Abiola Babes da ke Abeokuta kuma har na zama kyaftin. Da Sanata Ahmed Aruwa ya saye kulob din DIC Bees da ke Kaduna kuma aka canza mata suna ta koma Ranchesr Bees ne sai na sake komawa Kaduna na cigaba da yin wasa a kulob din. Ba ni kadai na koma Ranchers Bees daga Abiola Babes a wancan lokaci ba.
Akwai ’yan wasa irin su Ayo Ogunlana da Tajuddeen Olaiya da bictor Ogunsanya da sauransu. Daga nan ne na samu fita zuwa kasar waje a shekarar 1988. Na tafi zuwa Beljiyam ne inda na yi wasa a wani kulob da ake kira Eklo. Na shafe shekara biyar ina kwallo a Eklo da ke Beljiyam. Sai dai na samu matsala da kulob din tun kwantaragina bai kare da su ba. Yakamata ne a ce na yi shekara biyar, amma shekara hudu kawai na yi saboda yadda aka kware ni wajen sanya hannu a kwantaragin tun farko. Abu ne da manaja na ya hada baki da mahukunta kulob din wajen yi mini rufa-rufa na sanya hannu, don sun yi mini ne da yarensu, kuma ni a lokacin ban san me suke fada ba, sai bayan kwantaragin ta yi nisa ne wajen shekara hudu na fahimci inda aka sanya gaba. Ta kai sai na shafe watanni uku ko fiye ba a biya ni albashi ba, ashe hakan na daga cikin abin da kwantaragin ta kunsa. Ni kuma daga nan ne na yi musu bore, na tattara kayana na komo gida Najeriya duk da ina da sauran kwantaragin shekara daya da su. Ta kai hatta manajana sai da ya yi rigima da Dominic Iorfa a wancan lokaci, tun da manajanmu daya ne, kuma yana da halin cuta, maimakon ya yi mana fassara da turanci don mu gane abin da suke fada sai ya kyale mu kurum mu sanya hannu a kan abin da ba mu sani ba, hakan ta sa na ki komawa Beljiyam. Daga nan na wuce Indonesiya, amma Malesiya na fara zuwa.
Na je Malesiya ne ni da Stephen Keshi kocin Super Eagles na yanzu. Har mun samu wani kulob amma muna jiran shugaban kulob din ya dawo daga Hong Kong don mu sanya hannu a kulob din to akwai wani dan kwallon Kamaru da muka yi kwallo tare da shi sai ya kira bictor Ogunsanya, to bictor Ogunsanya kuma ni na kawo shi Kaduna daga Abiola Babes kuma ina zaune ne a gidansa da ke can Malesiya shi kuma bictor sun yi wasa a kulob daya a Fotugal da dan Kamaru din sai ya kira shi ya shaida masa akwai wani kulob a Indonesiya da suke neman dan kwallon tsakiya (attacking midfielder) sai shi kuma ya fada masa ai ina can Malesiya. To haka aka yi suka tuntube ni na canza ra’ayi na bar Malesiya na koma wani kulob a Indonesiya. To ka ji yadda aka yi na yi wa wani kulob kwallo a Indonesiya har na tsawon shekara biyu. To muna cikin kwallo ne sai wata musiba ta barke a garin inda aka yi ta tafka yaki ana ta kashe-kashe. A takaice dai mu a ofishin Jakadancin Najeriya da ke can aka boye mu. Sai da muka kwashe kwanaki 14 muna boye saboda yakin ya fi karfin inda ake tunani.
Daga nan ne aka fitar da mu daga cikin kasar a helikopta (helicopter) zuwa Singafo. Kowa daga cikinmu bai dauki komai daga gidansa ba, don yadda mutum ya fito haka muka dawo gida Najeriya babu shiri. To bayan mun dawo Najeriya ne sai Abdulmuminu Aminu tsohon shugaban Hukumar NFF ya roke mu wajen taimaka masa wajen farfado da kungiyar kwallon kafa ta Katsina United. Hakan kuwa aka yi muka amince muka tafi Katsina a matsayin masu bayar da shawara har kulob din ya yi karfi. Ya ce min in zan iya buga kwallo a kulob din in buga, in kuma ba zan iya ba, to mu nemo masa matasan da za su yi kwallo a kulob din. To haka muka yi wajen zakulo hazikan ’yan kwallo daga sassan kasar nan muka tattara su a Katsina United. A lokacin ne Katsina United ta lashe kofuna da dama, kuma ta samu nasarori masu dimbin yawa.

Aminiya:To wadanne nasarori ka samu a harkar kwallo?
dahiru Sadi: Gaskiya babbar nasarar da zan ce na samu ita ce na yi wa kasata Najeriya kwallo sannan na fita kasashen waje kuma na yi kwallo a matsayin gwani na gwanaye watau Professional a kulob daban-daban. Na yi wa a kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Green Eagles wasa a tsakanin 1983 zuwa 1984. Kuma wata nasarar da zan ce na samu ita ce ni ne dan kwallon da na ci wa Najeriya kwallo a gasar neman gurbi na gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a kungiyar Flying Eagles da hakan ya sa muka haye zuwa gasar cin kofin duniya na matsa da ya gudana a Meziko a shekarar 1983. Ba zan manta ba, bayan mun yi kunnen doki da Kwaddebuwa da ci 1 da 1 a can sai suka biyo mu Najeriya inda nan ma muka yi kunnen doki da ci 1-1. Ana gab da tashi ne sai na zura kwallo ta biyu da hakan ya sa Najeriya ta haye gasar cin kofin duniya na matsa. Kuma a gaban shugaban kasa Shehu Shagari a filin wasa na kasa da ke Legas abin ya faru. To bayan mun dawo daga gasar cin kofin duniya ne mu kusan biyar aka mayar da mu babbar kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Green Eagles don mu cigaba da yin kwallo a wancan lokaci.

Aminiya: A wace shekara ka daina buga kwallo?
dahiru Sadi: Ina jin na daina yin kwallo ne a shekarar 1997 zuwa 1998.

Aminiya: Ta bangaren horar wa fa?
dahiru Sadi: Eh ni ban taba horar da wata kungiya ba, amma dai ina taka rawar kodineta, watau mai bayar da shawarwari a tsakanin koci da ’yan kwallo da kuma mahukunta. da sauransu. Na yi kodineta a kungiyar kwallon kafa ta U-17 da kuma ta U-23. Yanzu haka kuma ina daga cikin ’yan kwamitin da ke bayar da shawara ga kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da hukumar NFF.

Aminiya: Ta ta bangaren iyali fa, sai da ka gama kwallo ka yi aure?
dahiru Sadi: A’a, ni tun kafin ma in tafi kasar Beljiyam na yi aure. Hasalima biyu daga cikin ’ya’yana a Beljiyam na haife su, don haka suna da takardar zama ’yan kasa a can Beljiyam da kuma ta nan gida Najeriya. Yanzu haka ina da mata biyu da ’ya’ya tara.

Aminiya: Mene ne shawararka ga matasa?
dahiru Sadi: Shawarata ita ce su rika bin komai sannu a hankali, ba cikin gaggawa ba. Yin gaggawa shi zai kawo da-na-sani. Kuma su mayar da hankali a wajen nuna kwazo da juriya da hakuri a duk lokacin da suke kwallo. Su rika yin biyayya ga shugabanninsu da kuma amfani da irin shawarwarin da za a rika ba su.

Aminiya: Mece ce shawararka ga gwamnati a harkar kwallo?
dahiru Sadi: A fitar da tsarin da za a rika bi don ganin an bunkasa wasan kwallo a Najeriya, kamar yadda ake yi a sassan duniya. A daina yawan zargi ko korar koci da zarar an samu rashin nasara. Korar koci ba shi ne mafita ba. kasashen da suka cigaba irin su Brazil da Jamus da Faransa da Italiya da sauransu, sun binm tsarin ne tun daga matakin kanana zuwa na matsakaita zuwa na manya a harkar kwallo. Kamar makaranta ce watau daga aji daya zuwa na biyu zuwa sama, amma mu a nan Najeriya abin ba haka yake ba.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram