Yadda manhajar OneBank za ta sauya harkar banki a Najeriya – Bankin Sterling
Bankin kasuwanci na Sterling ya kirkiro manhajar da ke dauke da duk abin da abokan huldarsa ke bukata. Babban jami’in fasaha na bankin, Mista Olayinka Oni ya ce an tsara manhajar mai suna OneBank ne ta yadda kwastomomi za su iya yin kowacce irin hada-hada da ita cikin sauki. Yanzu da OneBank, Sterling Bank ya zarce […]
Bankin kasuwanci na Sterling ya kirkiro manhajar da ke dauke da duk abin da abokan huldarsa ke bukata.
Babban jami’in fasaha na bankin, Mista Olayinka Oni ya ce an tsara manhajar mai suna OneBank ne ta yadda kwastomomi za su iya yin kowacce irin hada-hada da ita cikin sauki.
Yanzu da OneBank, Sterling Bank ya zarce takwarorinsa ta fannin kirkira a Najeriya, in ji shi.
A cewarsa, OneBank ta dace da tsarin cinikayya na zamani da ba a taba ganin irinsa ba a harkar banki a kasar.
Abubuwan da OneBank ke yi sun hada da bude asusun ajiya nan take, tura kudi a ciki da wajen kasa, cirar kudi ta na’urar ATM ba tare da kati ba, da biyan kudin ruwa da na wuta.
Sauran sun hada da biyan kudin kallon tashoshin talbijin da rijistar kungiyoyi da sayen katin waya da data.
A ‘yan kwanakin nan ne bankin na Sterling ya lashe kyautar gwarzon shekara karo na hudu a matsayin jagaba ta bangaren kirkira a tsakanin bankunan kasar wacce Babban Bankin Kasa na CBN ya ke bayarwa.