Yadda manoma da kamfanonin shinkafa ke murna da rufe iyakokin Najeriya
Manoma da kamfanonin shinkafa na Najeriya, sun bayyana matukar farin cikinsu kan matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na rufe iyakokin kasar nan. Manoma da kamfanonin sun ce wannan mataki da Gwamnatin Tarayya ta dauka, zai dada taimakawa wajen bunkasa harkokin noma da tattalin arzikin kasar nan. Don haka sun nuna goyon bayansu ga wannan […]
Manoma da kamfanonin shinkafa na Najeriya, sun bayyana matukar farin cikinsu kan matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na rufe iyakokin kasar nan. Manoma da kamfanonin sun ce wannan mataki da Gwamnatin Tarayya ta dauka, zai dada taimakawa wajen bunkasa harkokin noma da tattalin arzikin kasar nan. Don haka sun nuna goyon bayansu ga wannan mataki.
Manoma da kamfanonin sun ce sakamakon wannan mataki da gwamnatin ta dauka na rufe kan iyakokin kasar nan, farashin shinkafa ’yar gida ya yi tashin gwauron zabo – saboda masu fasakwauri ba sa samun damar shigo da shinkafar kasashen waje.
Yanzu ayyukan kamfanonin da suke sarrafa shinkafa na gida sun kankama, sakamakon daukar mataki da aka yi. Kuma farashin shinkafar ’yar gida ya tashi sama. Misali yanzu buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 na Mama da Kamfanin Kayayyakin Amfanin gona na Olam ke yi a Rukubi da ke Jihar Nasarawa ana sayar da shi kan Naira 19,500, yayin da ake sayar da buhun shinkafa ’yar waje, mai suna Tomato kan Naira 21,000 zuwa Naira 23,000.
Wakilinmu ya gane wa idonsa yadda manoman shinfaka da masu gudanar da harkokin kasuwancinta, suke ta murna da farin ciki a yankin Doma da ke Jihar Nasarawa.
A zantawar da wakilinmu ya yi da Manajan Daraktan Kamfanin Shinkafa na Labana Rice Mills da ke Birnin Kebbi a Jihar Kebbi, Alhaji Abdullahi Idris Zuru kan wannan al’amari, ya bayyana matukar farin cikinsa da daukar wannan mataki.
Ya ce wannan mataki da aka dauka ya dada bunkasa ayyukan kamfanin da kuma cinikin da suke yi. Ya ce kafin gwamnati ta dauki wannan mataki na rufe kan iyakokin kasar nan, shinkafar da kamfanonin shinkafa na gida suke yi suna jibge ta ce a sito-sito, saboda rashin kasuwa. A yayin da wasu kamfanonin suka dakatar da gudanar da ayyukansu saboda rashin ciniki.
Abdullahi Zuru ya ce babu shakka barin masu fasakwauri, suna ci gaba da shigo da shinkafa daga waje yana da matukar hadari ga manoman Najeriya. Domin zai sanya manoma su kasa biyan rancen noma da Babban Bankin Najeriya ke bayarwa saboda rashin darajar kayayyakin amfanin gonar da suke nomawa.
A zantawarsa da wakilinmu kan wannan al’amari wani babban jami’i a Kamfanin Kayayyakin Amfanin Gona na Olam, Mista Ade Adefeko, ya ce duk shekara akalla masu fasakwauri suna shigo da shinkafa tan miliyan biyu, ta kan iyakokin Najeriya da aka rufe. Ya ce babu shakka wannan mataki da Gwamnatin Tarayya ta dauka, ya dace kwarai da gaske. Domin zai kare ’yan kasuwa masu zuba jari a kamfanonin sarrafa shinkafa na Najeriya.
Shi ma a zantawarsa da wakilinmu Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya [RIFAN] Alhaji Mohammed Abubakar Maifata, ya ce rufe kan iyakokin kasar nan ya yi daidai. Shugaban ya fada a wajen wani taron ’yan jarida da suka kira a Babban Birnin Tarayya , Abuja, cewa matukar Gwamnatin Tarayya ba ta dauki wannan matakin ba, Najeriya za ta rika yin asarar sama da Naira biliyan 150 duk shekara saboda fasakwaurin shigo da shinkafa daga kasashen waje.
Wakilinmu a Jihar Ebonyi, jihar da take kan gaba wajen noman shinkafa a yankin Kudu maso Gabas ya gano yadda harkokin kasuwancin shinkafa ’yar gida suka dada bunkasa sakamakon wannan mataki.
Wakilinmu ya zanta da wani dan kasuwa da ke sayar da shinkafa sama da shekara 46 da suka gabata a garin Abakaliki mai suna Mista Peter Simeon, inda ya roki Gwamnatin Tarayya da kada ta sake bude kan iyakokin kasar nan. Kuma ta ci gaba da bai wa manoman shinkafa a kasar nan rancen kudi, domin su dada bunkasa noman shinkafar.
Ya ce tunda aka rufe kan iyakokin kasar nan, ’yan kasuwa daga Legas da Anambra da Aba da Fatakwal suke zuwa yankin suna sayen shinkafa. Ya ce yanzu manoman shinkafa suna zuwa kasuwa su koma gidajensu cikin farin ciki, saboda darajar da shinkafar ta yi, sabanin baya da suke zuwa kasuwa babu masu saye.
Shi ma a zantawarsa da wakilinmu Sarkin Hatsin Saminaka da ke Jihar Kaduna, Manu Isah Idris, ya ce su manoma suna goyon bayan matakin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dauka, na rufe kan iyakokin kasar nan.
Ya ce duk mai son ci gaban Najeriya ya kamata ya goyi bayan matakin da gwamnati ta dauka, saboda zai tallafa wa talakawan Najeriya wadanda mafiya yawansu manoma ne.
Ya ce idan manoma suka yi noma suka fadi, babu yadda za a yi su samu karfin gwiwar ci gaba da yin noman.
“Don haka rufe kan iyakokin kasar nan da gwamnati ta yi don hana shigo da shinkafa ko masara ya yi daidai. Hakan zai sanya mu tsaya mu ciyar da kanmu. Don haka matakin ya taimaka wa manoman kasar nan,’’ inji shi.
Sarkin Hatsin ya ce manoman da suka yi noma a bara sun fadi. Amma yanzu sakamakon daukar wannan mataki, manomi zai samu kwarin gwiwa.
Ya yi kira ga masu sukar matakin da gwamnati ta dauka, su bari, domin Shugaban Kasa ya dauki matakin ne don ya taimaka wa talakawan Najeriya.