Yadda manoma za su tallata hajarsu ta shafukan sada zumunta
A sakamakon cigaban kimiyya da fasaha da a kullum Najeriya ke samu, wata kungiyar kwararrun masana kimiyya a Abuja, IHIFId Technology Nigeria, ta bullo da wani sabon shiri wadda shi ne irinsa na farko wajen horar da manoma sabbin dabarun hanyoyin shiga kafafen sadarwa na zamani da zumar tallata kayayyakin gonakinsu da sauran hajar su […]
A sakamakon cigaban kimiyya da fasaha da a kullum Najeriya ke samu, wata kungiyar kwararrun masana kimiyya a Abuja, IHIFId Technology Nigeria, ta bullo da wani sabon shiri wadda shi ne irinsa na farko wajen horar da manoma sabbin dabarun hanyoyin shiga kafafen sadarwa na zamani da zumar tallata kayayyakin gonakinsu da sauran hajar su a kyauta.
Shugaban kungiyar ta IHIFId Technology Nigeria, Mista Adikpe Odeh ya bayyana cewa an yi hakan ne don tabbatar da cewa manoman Najeriya na tafiya da hikimomi da fasahohin zamani kamar sauran takwarorinsu na kasashen duniya. Za su rika daukar hotunan kayayyakin amfanin gonarsu domin sayarwa a shafukan dillalan kayan gwari da sauran kayan abinci a shafukan intanet.
“Shirin na da matukar alfanu ga manoman kasar nan domin hakan zai taimaka masu ta hanyoyi daban-daban domin magance irin hatsarin da manoman ke fadawa ciki, musamman ma irin asarar da dillalai ke janyo masu da kuma rage yadda suke shan wahalar fitowa da kayayyakin daga gonakinsu.”
Mista Adikpe ya ce amfani da fasahohin zamani wajen bunkasa harkar noma a duniya na farfado da darajar amfanin gona, domin ko da manomi ya sanya amfanin gonarsa ba a saya ba, to kayan nasa na tare da shi. Saboda haka ne ma ya janyo hankalin manoma wajen shiga kafafen sadarwa domin neman kungiyoyin dillalan kayayyakin amfanin gonakinsu.
A yayin da wakilinmu ya tuntubi wani manomi da ya halarci taron, ya bayyana masa jin dadinsa haka kuma ya nuna da cewa wannan babban cigaba ne aka samu a fannin noma, kuma wannan dabara za ta rage yawan asarar da manoma ke tafkawa da kuma magance yadda dillalai ke cin =kazamin riba fiye da manoman.