‘Yadda masu garkuwa da mutane suka gaza tafiya da ni’

Wani fitaccen dan kasuwa da ke karamar Hukumar Ribah a Jihar Kebbi Alhaji dan Musa Ribah, ya tsallake rijiya da baya a ranar Juma’ar da ta gabata bayan da wasu masu garkuwa da mutane suka so su sace shi, amma ba su yi nasara ba inda suka harbe shi a kafa. Alhaji dan Musa wanda […]

‘Yadda masu garkuwa da mutane suka gaza tafiya da ni’
‘Yadda masu garkuwa da mutane suka gaza tafiya da ni’

Wani fitaccen dan kasuwa da ke karamar Hukumar Ribah a Jihar Kebbi Alhaji dan Musa Ribah, ya tsallake rijiya da baya a ranar Juma’ar da ta gabata bayan da wasu masu garkuwa da mutane suka so su sace shi, amma ba su yi nasara ba inda suka harbe shi a kafa.

Alhaji dan Musa wanda Aminiya ta zanta da shi a Asibitin kashi da ke birnin Sakkwato bayan likita ya yi masa aiki a kafa a ranar Lahadin da ta gabata. Ya ce, “A ranar Juma’a da misalin karfe 7:30 na yamma, muna cikin masallaci a Ribah kawai sai wasu mutane dauke da bindiga suka shigo kuma suna ganina suka ce ga Alhajin nan mun tafi da shi, sai na ce ina? Kawai ba su amsa min ba suka yi kokarin dauka ta, ni kuma na ki muka rika kokawa da su don suna da yawa, ban iya gane yawansu, kuma bakin fuskoki ne a wurina.”
Ya kara da cewa “Muna cikin haka ne wani daga cikinsu ya sare ni a baya, amma bai sanya na karaya kan ceton raina ba, bayan na fizge kaina ne, sai na gudu daga nan suka harbe ni a kafa suka gudu, ’yan uwana suka dauko ni zuwa nan asibiti.”
Ya ce wannan hobbasa da ya yi tana da nasaba ga nasihar da wani malami a kasar nan ya yi cewa, kada mutane su rika jin tsoro su tsaya su jajirce don ceton kansu daga kowane batagari da ya tunkare su domin rai daya ne kuma tsoro ne ke sanya ayyukkan batagari ke kara yawa a kasar nan.
Ya ce, “Tun lokacin da na ji kalmomin Sheikh Jingir “Ban da tsoro” na kudurta aiki da shawararsa a duk lokacin da irin haka ta faru. Ba wani abu da zai ba ni tsoro, bin shawarar Shaikh Jingir ya sanya na fi karfin masu garkuwa da mutane da sun tafi da ni, a halayyar wadannan batagari da suka same ni ya tabbatar min da masu garkuwa da mutane ne. Don haka nake kira ga zababben Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi tsaye wajen magance wannan da matsalar tsaro ta haddasa, kuma mutane su daina nuna tsoro.”