Yadda masu garkuwa suka kashe min da bayan karbar diyyar miliyan N1.5
Wani magidanci mai suna Eguaku Anya, ya ce masu garkuwa da mutane sun kashe dansa mai suna Stephen Anya dan shekara 15, sannan suka jefar da gawarsa bayan sun karbi diyyar Naira miliyan daya da rabi. Babban wanda ake zargi da sace yaron, yana cikin wadanda Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta gabatar da ake […]
Wani magidanci mai suna Eguaku Anya, ya ce masu garkuwa da mutane sun kashe dansa mai suna Stephen Anya dan shekara 15, sannan suka jefar da gawarsa bayan sun karbi diyyar Naira miliyan daya da rabi.
Babban wanda ake zargi da sace yaron, yana cikin wadanda Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta gabatar da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban a jihar.
Da yake zantawa da manema labarai, Mista Anya ya ce, “masu garkuwar sun bukaci mu ba su Naira miliyan 40 da farko.
“Sun zo gidana ne a ranar 27 ga watan Mayu, inda shi wannan Sylvester din da wasu suka mana barna da dama, duka tafi da wayoyinmu. Sannan sai suka sace dana.
“Su biyu ne suka zo gidana, daya daga cikinsu unguwarmu daya ta Gonin Gora a Kaduna.
“Dana shekararsa 15, kuma ya rubuta jarabawar JAMB, inda ya samu maki 245, kuma ya samu nasarara a jarabawar WAEC da NECO, kawai jira yake ya samu makarantar gaba, ya fara karatu.
“Bayan sun bukaci Naira miliyan 40 da farko, sai muka shirya za su karbi Naira miliyan 1.
“Bayan an kai musu sai suka ce wai kudin ya yi kadan, sai muka kara Naira dubu 500.
“Duk lokacin da muke yin wannan muna ta rokonsu da su bari mu yi magana da yaron, suka ki.
“Sai suka ce za mu kara musu Naira miliyan daya da rabi kuma, muka amince za mu nema kudin mu kawo, amma da yarjejeniyar sai mun ji muryar yaron. Ba mu sani ba ashe sun riga sun kashe yaron tun washegarin da suke sace shi”, a cewarsa.
A nasa jawabin, wanda ake zargin ya karyata zargin inda ya ce, “ban san komai a kan abin da ake magana na garkuwa da mutane ba.
“Ni dai na san na ajiye wani (dayan wanda ake zargin) a gidana, ban san mai garkuwa da mutane ba ne. A Gonin Gora nake zama, kusa da kamfanin da ya ce yana aiki.
“Ya ce yana neman daki, muka nema ba mu samu. Sai ya biya ni Naira dubu 7 ya zauna a wajena na mako 3 daga nan ya tafi, inda ya kusan shekara ban gan shi ba”, a ta bakinsa.
Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammad Jelige ya ce bayan sun kashe yaron, sai suka jefar da gawarsa a rijiya, sannan suka zuba kusan bulon siminti guda 20 a samansa domin kada gawar ta yi wari.