Yadda masu hawan tsaunika suka gano jirgin saman da ya bace shekara 50 a Chile
Wadansu masu hawan tsaunika sun bayyana yadda suka gano wani jirgin saman da ya bace shekara 54 da ta wuce a kasar Chile a ranar Talatar da ta gabata.Masu hawan tsaunikan sun ce a lokacin da suke hawa tsaunika ne suka gano baraguzan jirgin da ya fadi a yankin Andes na kasar Chile, inda mutane […]
Wadansu masu hawan tsaunika sun bayyana yadda suka gano wani jirgin saman da ya bace shekara 54 da ta wuce a kasar Chile a ranar Talatar da ta gabata.
Masu hawan tsaunikan sun ce a lokacin da suke hawa tsaunika ne suka gano baraguzan jirgin da ya fadi a yankin Andes na kasar Chile, inda mutane 24 suka mutu ciki har da mutane 8 wadanda mambobin kungiyar kwallon kafa ta kasar Chile ne.
Sun ce sun gano baraguzan jirgin ne wani wuri mai nisan kafa 10, 500 (daidai da mita 3, 200) wato daidai da Mil 215 (Kilomita 360) a kan tsaunin yankin Andes.
daya daga cikin masu hawa tsaunikan mai suna Leonardo Albornoz ya bayyana wa gidan talabijin na Channel 7 a kasar Chile cewa sun ki bayyana hakikanin wurin da suka gano baraguzan jirgin ne don su magance wadanda za su yi zuwa wurin da wata mummunar manufa.
Idan ba a manta ba dai a ranar 3 ga Afrilu, 1961 ne wani jirgin sama mai suna Douglas DC-3 da yake dauke da ’yan wasan kungiyar kwallon kafar kasar Chile ya bace, inda aka kasa gano inda ya shiga, hakan ya gigita duniyar wasanni.
kungiyar kwallon kafar ta buga wasa a Osorno a lokacin da ake gasar Copa de Chile, inda aka hanyarsu ta dawo Santiago babban birnin kasar Chile ne jirgin nasu ya bace. ’Yan wasa sun hau jirgi daya, haka sauran jami’an kungiyar kwallon kafa suka hau wani jirgi daban.
A lokacin masu ceto sun shafe makonni wajen neman jirgin, amma a karshe aka hakura ba tare da an gano shi ba, inda aka jana’izar ’yan wasan ba tare da an gawarwakinsu ba.
“Babban abin farin ciki ne da muka gano baraguzan jirgin. Hakan zai sanya a kawo karshen rashin tabbas da ake ciki game da ’yan wasan da suka bace.” Inji Albornoz.
Masu hawan tsaunikan sun ce sun ga baraguzan jirgin hade kasusuwan mutane ba tare da sun yi tono ba, sai dai wurin da suka samu baraguzan jirgin ya bambanta da wurin jami’an kasar suka ce jirgin ya bace.