Yadda masu kwacen waya suke jefa Kanawa a tashin hankali
Masu kwacen wayar na amfani da makamai suna suke sara ko sukar mutane.
Kwacen waya a Jihar Kano, musamman a babban birnin jihar lamari ne da yake neman zama ruwan dare a kusan ko’ina a Arewa a yanzu.
Bayanai sun nuna cewa a Jihar Kano lamarin ya kai intaha tare da yin kamari musamman a kananan hukumomin da ke cikin birnin.
Masu kwacen wayar sukan yi amfani da makamai inda suke sara ko sukar mutanen da suka kwace wa wayoyin inda suke raunata su wani lokacin ma har da kisan kai.
Kwacen wayar bai tsaya a kan maza kawai ba, har ma ya hada da mata musamman ma ’yan mata wadanda ake ganin sun fi rike manyan wayoyi masu tsada.
Haka ba sai da daddare masu kwacen wayar suke gudanar da ta’asarsu ba, suna yi har da rana ido yana ganin ido.
Babu wanda ya tsira daga kwacen waya tun daga kan mai tafiya da kafa har zuwa wanda yake cikin mota, ta gida, ko ta haya inda ake tare mutane a kwace wayoyinsu.
Hatta direbobin Keke-NAPEP a Kano ba su tsira ba, domin an sha tare su a kan hanya a kwace wayar ko Keken dungurugum.
Binciken Aminiya ya gano cewa masu satar wayoyin wadanda yawancinsu matasa ne sukan yi ne don samun kudin sayen kayan maye kamar yadda wadansu daga cikin masu kwacen wayar suka rika shaida wa manema labarai a lokacin da ’yan sanda suka kama su.
Yadda aka yi kwacen waya a Masallacin Juma’a
A watan Ramadan da ya gabata an samu wadansu masu kwacen wayoyi da suka taru suka yi wa Masallacin Juma’a na Khalifa Isyaku Rabi’u da ke Gwauron Dutse tsinke inda suka karbe wayoyin mafi yawan mutanen da suka je masallacin don yin Sallar dare.
Wani bincike na baya-bayan nan ya nuna cewa idan matasan suka kwaci wayoyin jama’a sukan sayar ga masu damfara ta intanet wato wadanda aka fi sani da ’yan Yahoo inda su kuma a nasu bangaren sukan yi yadda za su yi wajen ganin sun wawushe duk abin da mutum ya mallaka a cikin asusun ajiyarsa na banki.
‘Yadda aka kwace mana wayoyinmu’
Wadansu da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana cewa masu kwacen wayar sai da suka ci zalinsu kafin daga bisani su karbi wayoyin nasu.
Ahmad Ali ya ce, “Sau uku suka tare ni suna kwace min waya a wurare daban-daban.
“An taba yi min a Kabuga, an yi min a Kwanar FCE Kano, haka an kwace min wata wayar ta uku.”
Wata da aka kwace mata waya a gidansu a daidai lokacin da take barci, mai suna A’isha Ahmad ta bayyana yadda lamarin ya faru.
“Wata rana ina kwance ina barci sai na ji motsi a dakin da nake, ban yi saurin magana ba saboda tsoro.
“Can sai wanda ya shigo ya sa hannunsa zai dauke min waya ni kuma sai na yi saurin daukewa.
“Ganin haka sai ya ja hannuna yana kokarin kwacewa inda ni kuma na rike wayar sosai.
“Sai ya dora min wuka a kan ruwan cikina. Hakan ya sa na yi saurin sake masa wayar.
“Ina kallon shi ya fice daga dakin tare da wayar a hannunsa,” inji ta.
Fatima Abdussamad Umar ta bayyana yadda masu kwacen waya suka kwace mata waya kamar haka:
“Wata rana da Sallah mun fita kallon Hawa. Kasancewar ina so in sa hotunan a kafafen sada zumunta na zamani, sai na fito da wayata ina daukar hotuna. Ai kuwa sai na ji an fizge wayar daga hanuna.”
‘Yadda na sha bugu kafin su karbe wayata’
Wata daliba mai suna Maryam Dauda Nasir ta shaida wa Aminiya cewa, “Wata rana mun je wurin biki muna zaune sai kawai wadansu samari suka zo wurin, nan da nan mutane suka shiga guje-guje ina zaune ban gudu ba.
“Da na fahimci abin da yake faruwa sai na tashi da gudu na shiga wani gida.
“Sai suka bi ni har cikin gidan suka yi min duka suka tattaka ni suka karbi jakata suka zazzage ta, sannan suka dauke wayata suka tafi.”
Muhammad Auwal ya bayyana wa Aminiya cewa, “Wata rana ina tare da matata a kan hanyar bayan Jami’ar Northwest, sai aka kira ni a waya, don haka sai na ba ta amsa saboda ina tuki.
“Ba mu yi aune ba sai kawai ganin mutane muka yi a kanmu sun zazzare wukake suna kokarin soka min.
“Sai suka kama dana suka rike suka ce dole sai na bayar da wayata kafn su saki yaron.”
‘Yadda suka bar ni cikin jini bayan kwace min waya’
Wani dan jarida mai suna Rabi’u Anas Aboki, ya hadu da masu kwacen wayar, inda suka raunata shi bayan kwace wayar da suka yi.
“Na fito daga masallaci a wajen Gidan Bashir Tofa sai wadansu mutum biyu suka tare ni inda suka soka min wuka tare da kwace wayata.
“Lokacin da suka nufo ni na dauka suna so su yi tambaya ce, don haka ban damu ba.
“Sai suka yiwo kaina suka kama ni da kokawa sannan suka zaro wukake suka yanyanke ni a hannu da gefen kaina.
“Sannan suka dauke wayar suka kuma bar ni kwance cikin jini.”
‘Yadda aka kashe min dan uwa wajen kwace masa waya’
Mustapha Adamu, dan uwan marigayi Umar Muhammad ne wanda masu kwacen wayar suka hallaka a Kofar Mata.
Ya shaida wa Aminiya cewa bayan sun kwace wa dan uwansa wayar ce kuma suka biyo baya suka soke shi.
“Masu kwacen waya ne suka hallaka dan uwanmu domin mutanen da suke gefen wurin sun shaida mana cewa sun hango lokacin da ake musayar yawu da masu kwacen wayar, inda suka fito da wuka suka sossoke shi a ciki lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.
“Nan aka dauke shi aka kai gawarsa dakin ajiye gawarwaki na Asibitin Kwararu na Murtala,” inji shi.
Yawancin masu kwacen wayar matasa ne wadanda ake ganin sun shiga wannan hanya ce sakamakon rashin aikin yi da kuma mutuwar zuciya kamar yadda wani masanin halayyar dan Adam ya shaida wa Aminiya.
Ana samun sauki –’Yan sanda
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, a tattaunawarsa da Aminiya ya ce rundunarsu tana bakin kokarinta wajen dakile lamarin kwacen waya a jihar kuma hakan ne ya sa lamarin ya yi sauki.
“Idan kin yi nazari lamarin kwacen waya a yanzu ya yi sauki sosai.
“Sai abin da ba a rasa ba wannan kuwa ya faru ne saboda daukar matakai da muka yi a kan lamarin; Domin a lokuta daban-daban mun kama mutanen da yaran da suke kwacen wayar a wurare daban-daban na jihar.
“A kwanakin baya a nan mahadar Titin Dan’agundi mun kama sama da masu kwacen waya 39 ban da wasu wuraren.
“Haka a wasu wuraren mun gudanar da irin wannan kame.
“A gaskiya muna samun nasara ta hanyar samun hadin kai daga mutanen gari wadanda su suke ba mu bayanai a kan hakan.
“Mun riga mun bayar da lambar waya ga jama’a don sanar da mu abin da yake faruwa kuma jama’a suna ba mu hadinkai domin a wasu lokutan ma masu kwacen wayar ba su barin wurin mukan je mu kama su,” inji shi.
‘Barayin sun canja salo’
A cewar Abdullahi Kiyawa a yanzu masu kwacen wayar sun canja salon satar wayar inda suka koma haura gidaje suna satar wayoyin.
“Kasancewar mun hana su sakewa a yanzu sun canja salo sun koma haura gidaje suna daukar wayoyin mutanen gida.
“Ko a kwanan nan mun samu korafe-korafe a kan haka. Har ma mun kama mutum biyu da suka haura wasu gidaje suka dauki wayoyin mutanen gidan.
“Zan yi amfani da wanann kafa na yi kira ga al’umma da su sa ido wajen kula da gidajensu tare da kayayyakinsu.
“Kuma su yi gagagwar sanar da ’yan sanda da zarar sun ga irin hakan na shirin faruwa ko lokacin da lamarin yake faruwa don daukar matakin da ya kamata a kan lokaci,” inji shi.