Yadda masu satar mutane ke addabar Kalaba
Matsalar sace mutane ana garkuwa da su domin neman kudin fansa ta addabi mazauna garin Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba. Jihar na kuma fama da matsalar ’yan kungiyar asiri da ba sa ga maciji da juna. Mahaifin Shaikh Auwal Albani ya rasu ’Yan bindiga na neman fansar N270m kan daliban ABU Amurka na leken […]
Matsalar sace mutane ana garkuwa da su domin neman kudin fansa ta addabi mazauna garin Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba.
Jihar na kuma fama da matsalar ’yan kungiyar asiri da ba sa ga maciji da juna.
- Mahaifin Shaikh Auwal Albani ya rasu
- ’Yan bindiga na neman fansar N270m kan daliban ABU
- Amurka na leken asiri ta manhajar Muslim Pro
Garin Kalaba wanda ake wa lakabi da Aljannar mutane yanzu kirari nasa na neman gushewa kasancewar fargaba ta sa mazauna garin da wasu kananan hukumomi a jihar ba sa iya rintsawa.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna a kasa da mako daya an sace sama da mutum bakwai a wurare daban-daban a Kalaba da kuma Karamar Hukumar Akampa.
Masu sace mutanen kan zo da manya bindigogi suna harbe-harbe domin tsoratar da jama’a daga nan su suma su yi awon gaba da duk wanda suka zo daukewa a motocinsu.
Wasu lokutan sukan kira iyalan wanda suka kama su nemi a ba su makudan kudade daga Naira miliyan zuwa sama.
Kwanan baya an sa ce matar wakilin jaridar The sun a Kuros Riba, Judex Okoro da wasu lokitocin Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kalaba (UCTH).
Su ukun sai da aka biya kudin fansa aka sako su amma iyalansu sun ki bayyana adadin kudin da suka biya.
Wannan matsala ta girma ta yadda duk masu hannu da shuni ko da manyan ma’aikatan gwamnati ke rufe wayoyinsu ko komawa gida da wuri domin kauce wa fadawa a hannun masu garkuwar.
Ta bangaren jami’an tsaro kuwa, kodayaushe sukan kare kansu da cewa ba a sanar da su na ko ba su da labari.
Dagar ranar Litinin zuwa Laraba an sace mutum biyar a wurare daban-daban ciki har da mijin wata ’yar jarida a Kalaba mai suna Bassey Okon Essien da matar wani tsohon dan Majalisar Wakilai, Ani Oku Ita bayan mijinta Eno Patrick Orok ya fita daga gidansu da ke layin Edi-motop.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kuros Riba, Irene Ugbo, ta ce “mafi yawancin mutanen da ake sacewa ba a sanar da mu”.
Aminiya ta tuntubi Alhaji Sha’aban Abdullahi, Sakataren Al’ummar Hausa-Fulani da Musulmai mazauna jihar kan wannan matsala sai ya ce “Ba abun muke fama da shi face matsalar tsaro, babbar matsalar ita ce shi Gwamna wanda shi ne Babban jami’in tsaro ya ki ya kula da al’amarin”.
Ya ci gaba da cewa, “Ni ma akwai abokina wanda ranar Lahadi aka bi shi har gida aka dauke shi har yanzu ba su kira ba, ba a san halin da yake ciki ba; matsalar tsaro a Kuros Riba ta shiga wani yanayi mai ban tsoro”.