Yadda masu wasa a gidan gala ke nutsuwa a lokacin azumi

Wata budurwa ta ce zaman-kai ko zaman gidan gala yana da daɗi na wani dan lokaci, “Amma rayuwa ce mai wahala.”

Yadda masu wasa a gidan gala ke nutsuwa a lokacin azumi

Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha. (Hoto: Twitter/@abbaelmustaph1)

A daidai lokacin da ake shirye-shiryen fara azumin bana ne, Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta bayar da umarnin rufe gidajen gala a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan wata ganawa da shugaban hukumar ya yi da jagororin kungiyar masu gidajen gala da ke jihar a ofishinsa.

A cewar shugaban hukumar, Abba El-Mustapha dokar za ta fara aiki ne daga ranar Lahadi, wato ana gobe za a fara azumi, har zuwa 1 ga watan Shawwal, wato ranar Karamar Sallah.

Abba El-Mustapha ya gargadi masu gidajen wasanni na gala su guji karya doka domin duk wanda hukumar ta samu da laifin karya dokar, za ta dauki tsattsauran mataki a kansa ta hanyar soke lasisinsa.

El-Mustapha ya kuma gode wa shugabannin gidajen galar tare al’ummar Jihar Kano bisa hadin kan da suke bai wa hukumar a kowane lokaci.

Kazalika, ya ja hankalin al’ummar jihar cewa, kofarsa a bude take domin ba shi shawara ko sanar da hukumar duk wani al’amari da zai taimake ta domin samun nasarar ayyukan da ta sanya a gaba.

A shekarun baya, an fi sanin Gidan Solo ko Gidan Gala da sunan Gidan Dirama, wanda wani tsarin nishadantarwa ne dadadde da ake gudanarwa a wasu birane, musamman a Arewacin Nijeriya kafin ya yi naso zuwa Kudancin kasar nan.

Kamar yadda tsarin yake tun asali, matasa ne maza da mata ke taruwa, suna gabatar da wasan kwaikwayo na barkwanci da kadekade da raye-raye, domin nishadantarwa.

Haka kuma, yawancin ’yan wasan da ke gudanar da shirin, a nan suke fara haskawa, kafin daga bisani su dawo Masana’antar Kannywood domin shirya finafinan zamani na Hausa.

Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa, Shu’aibu Idris, wanda aka fi sani da lakanin Lilisco ne ya kirkiri sunan Solo ko ’Yan Solo a 1999 a gidan Diramar Tarauni da ke Kano.

Daga lokacin ne aka maye sunan Gidan Dirama da Gidan Solo kuma tun daga lokacin lamarin ya fara tabarbarewa.

Aminiya ta ruwaito yadda ake zargin lalata tarbiyyar mata a gidajen gala, inda wasu suke koyon shaye-shaye da sauran harkokin badala.

A wata ziyarar bad-dakama da Aminiya ta kai gidajen gala a Abuja da Kaduna ta gano cewa, bayan raye-rayen da ake yi a gidajen, ana wasu harkokin badala ta bayan fage.

Aminiya ta zanta a wancan lokacin da wasu mata da suka bayyana yadda suka tsinci kansu a wata muguwar rayuwa da yadda suka koyi shaye-shaye da ma yadda wata ta bayyana yadda suke zubar da ciki.

Sai dai a wani yanayi da ake kira yayar zana, musamman a Kano da wasu jihohin Arewa maso Yamma, da zarar azumi ya zo, matan sukan watse daga gidajen gala, su koma gidajen iyayensu, inda wasunsu sukan yi rahar cewa an daure Shaidan.

Wata budurwa da takan koma gida duk lokacin da Ramadan ya shigo, ta bayyana wa Aminiya cewa, ita da kawayenta ne sukan koma gida domin gudanar da ibadar azumi.

A cewar budurwar, wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, zaman-kai ko zaman gidan gala yana da daɗi na wani dan lokaci, “Amma rayuwa ce mai wahala.

“Na riga na shiga, amma ba na fatan wata ’yar uwata ta shiga wannan yanayi. Mu da muke yi, muna addu’ar Allah Ya shiryar da mu,” in ji ta.

A game da ko za ta koma bayan Sallah, sai ta yi gum na wani dan lokaci, sannan ta ce, “A dai taya mu da addu’a kawai. Idan lokacin bari ya yi, dole zan bari.”

Sannan ta kara da cewa, babban burinta a rayuwa shi ne ta yi aure, ta hayayyafa.

Aminiya ta gano cewa, ana gudanar da harkokin gidan gala ne yawanci da yamma, inda akan yi hutun rabin lokaci, a yayin Sallar Magariba, a je a yi Sallah, a dawo a dora daga inda aka tsaya.

Bayan hutun na Kano, wasu gidajen da kansu ma sukan rufe a lokacin azumi, yayin da wasu kuma sukan koma wasan dare ne kawai.

HOTUNA: An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Ondo

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS