Yadda masu yi wa kasa hidima 5 suka rasu a hatsarin mota

Motar da suke komawa gida a ciki bayan samun horo ta yi taho-mu-gama da wata tarakta Jihar Yobe.

Yadda masu yi wa kasa hidima 5 suka rasu a hatsarin mota

Wasu matasa masu yi wa kasa hidima lokacin karbar horo a sansaninsu.

Matasa masu yi wa kasa hidima biyar sun rasu a hanyarsu ta komawa gida bayan kammala samun horo a Karamar Hukumar Fika ta Jihar Yobe.

Matasan sun rasu ne a wani hatsarin mota da ya ritsa da su a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa garuruwansu a Jihar Yobe, bayan sun kammala samun horon kwana 21 a sansanin masu yi wa kasa hidima ta Jihar Taraba.

Wani ganau, Sule Audu, ya ce lamarin ya auku ne ranar Talata da yamma inda motar hayar da ta dauko matasan ta yi taho-mu-maga da wata tarakta.

Ya ce bayan hatsarin, an garzaya da matasan zuwa asibiti a garin Fika, inda wasunsu suka ce ga garinku nan.

Marigayan, wadanda ke cikin Rukunin C kashi na II na masu yi wa kasa hidima, takwarorinsu sun bayyana matukar kaduwa da samun labarin rasuwarsu.

Sauran wadanda suka samu raunin kuma an kai su Asibitin Kwararru da ke Damaturu.

Mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) Hussaini Haruna, ya tabbatar wa wakilinmu da aukuwar hatsarin, sai dai bai bayyana wurin da abin ya faru ba.

Aminiya ta garo cewa daga cikin wadanda suka rasun akwai Ali Muhammad Ahmad, wanda ya kammala karatun Digirin farko a fannin Kemistiri daga Jami’ar Tarayya da ke Dutse; Audu Sani Tatata, (Kemistiri daga Jami’ar Maiduguri), dukkansu ’yan asalin Potiskum; Auwal Hamisu Bashari, (B.A (Ed) Islamic Education) daga Jami’ar Jihar Yobe, dan asalin Nguru; da sauransu.