Yadda mata suke soyayyar karya a makarantu

Yaudara wata aba ce da ke kasancewa a tsakanin mace da namiji, amma ba soyayyar hakika suke yi ba. Ta yiwu namijin yana sonta ba da gaske ba amma ita mace da gaske take yi har zuciyarta, ko macen ba da gaske take yi ba amma namijin da gaske yake yi ko ma dukansu ba […]

Yadda mata suke soyayyar karya a makarantu

Yaudara wata aba ce da ke kasancewa a tsakanin mace da namiji, amma ba soyayyar hakika suke yi ba. Ta yiwu namijin yana sonta ba da gaske ba amma ita mace da gaske take yi har zuciyarta, ko macen ba da gaske take yi ba amma namijin da gaske yake yi ko ma dukansu ba da gaske suke yi ba.

Yin hakan bai dace ba domin duk soyayyar da za a yi ba da niyyar aure ba, to ba ta da amfani. Saboda haka ya kamata maza da mata a makaranta ko a gida su shiga hankalinsu don daina irin wadannan abubuwa.

Karatun zamani ko karatun addini ko na koyon sana’a duk sun zama dole saboda yanayin da ake ciki a wannan lokaci. Amma a wannan rubutun za mu mayar da hankali ne wajen yadda mata ke yaudarar maza a makarantu. Akwai dalilai da yawa ta yadda hakan zai iya faruwa. Amma za mu yi kokarin kallon abubuwa kamar hudu ko biyar:

Sukan yaudari namiji idan ya kassance mai kokari a makaranta. Zai kasance ita wannan mace za ta rika bin namiji kamar suna soyayya amma kawai taimakon karatu take nema. Irin wannan sai ka ga macen da namijin suna rayuwa irin ta masoya amman duk na yaudara ce. Shi mai kokarin zai rika ba ta duk taimako tun daga koyar da ita karatu bayan aji da taya ta aikin gida. Har takan kasance ana taimaka mata wurin yin jarrabawa. Amma tunda soyayyar ba ta gaskiya ba ce daga an gama makaranta to gaba daya sai ya zamo ko kiransa ba za ta yi ba, in kuma ya kira ba dole ta dauka ba. To fa a haka za su yi ta tafiya ko Allah Ya taimake shi ya gane ko ta yi aurenta ta kyale shi.

Wadansu ’yan matan kuma sukan yi yaudara saboda suna da bukatar abin duniya. Irin wannan za ka ga cewa sona soyayyar ce kawai da wanda ke da dukiya idan kuma dalibin ba mai dukiya ba ne to fa ba za su yi soyayya da shi ba. Duk da yana da kudin burinsu ba wai su yi aure ba ne, amma dai su rika samun kudin da za su rika harkokinsu na makaranta. Duk inda ake kwalama a makaranta to za ka ga sun san wurin. Kawai dai harkar hutu ake yi ba abin da ya kai su makarantar ba. Kuma irin wannan ba sai an gama makarantan suke yaudarar ba, daga zarar sun ga wadanda suka fi wadancan dukiya kawai za su yaudare su ne. Ya zama dole ne duk mai soyayyar a makaranta idan har yana neman macen arziki ya lura da mata masu wannan hali a koyaushe. Kuma irin wadannan ’yan mata za ka ga a wasu lokuta ba sa zaman makaranta kawai suna tafiya ne daga gari zuwa gari inda samarin suke. Irin matan nan kwadayin duniya ne kawai a gabansu,  kullum suna neman mai dukiya ne kawai. A rika yawo da su a cikin motoci duk inda za a je su ne a gaban mota kawai.

Wadansu ’yan matan kuma suna yaudara saboda samarin sun yi fice a makaranta. Akwai samari wadanda su ne ke kungiyoyin dalibai na makarantu, irin wadannan duk inda suka leka a makaranta an san su. Saboda duk macen da suke tare dole su ma za su yi fice a makatantar daga ta wuce za a ce ga budurwar wane. Duk sa’ar da za a yi wani taro na dalibai dole ne a saka su cikin harkokin. Ya zama dole mata a makarantu su yi kokarin sanin abin da ya kawo su makaranta. Su tsaya zu jajirce ta hanyar yin abin da ya kamata. Duk da haka mazan da suka yi fice domin suna da kyau sosai da kwalliya, mata sukan yi soyayya da su a makarantu su ma amma ba soyayyar gaskiya ba, ita dai kawai burinta a rika nuna ta ana cewa ga budurwar wane.

Da yawan lokuta irin wadannan matan sukan jawo wa iyayensu zagi da cin mutunci domin da an kammala makaranta, namijin ya zo gidansu sai a ce ba a san da shi ba domin an riga an yi mata miji. Don haka ya kamata iyaye su rika jan kunnen ’ya’yansu, kuma su rika ziyartarsu a makarantu.

Haka kuma tsadar aure yana daga cikin abin da ka iya kawo yaudara a tsakanin masoya. Wannan shi ne ta yadda mace za ta tara samari da yawa amma killa  iyayenta suna da abin da suka tsara yadda za su yi mata aure. To irin wannan za ka ga iyayenta koma ita kanta za ta rika zaben samari ne, wadanda za su iya dauke mata wasu hidima a auratayya. Ya zama dole a duba abin da ya kamata wajen rage hidimomin aure.

A karshe za mu iya fahimtar cewa yaudara a wannan zamanin ta zama ruwan dare. Yin hakan a wurin mata ko maza ba laifi ba ne. A lokacin baya yaudara ba ta yi yawa ba. Saboda soyyaya akan yi ta ce  saboda ana son yin aure. Namiji idan yana son mace zai je wurin iyayenta ne don a ba shi damar neman auren. Kuma burin da iyaye suke sawa a  maganar aure yakan kawo yaudara.

Da fatan wannan rubutu zai amfanar da mu baki daya.

Daga Aliyu Khalid, Kaduna. 08038597907