Yadda mata ta haihu a kan hanya a Zariya
Wata mata da ake zato mara lafiya ce ta haihu a wani rusasshen kango da ke gefen hanya a Zariya. Wani likita da ke hanyarsa ta zuwa Samaru, Dokta Mustapha Muhammad ne ya ba wa mai jegon wadda ba a san daga inda ta fito ba kulawar gaggawa. Budurwa ta rataye kanta a Kano Yadda […]
Wata mata da ake zato mara lafiya ce ta haihu a wani rusasshen kango da ke gefen hanya a Zariya.
Wani likita da ke hanyarsa ta zuwa Samaru, Dokta Mustapha Muhammad ne ya ba wa mai jegon wadda ba a san daga inda ta fito ba kulawar gaggawa.
- Budurwa ta rataye kanta a Kano
- Yadda ’yan bindiga suka yi ta mana fyade —Matan Katsina
- An yi garkuwa da dalibai 8 na Jami’ar Ahmadu Bello
- Gobara ta tashi a kamfanin wutar lantarki na Jos
“Matar ta haihu lafiya sai dai mahaifarta ba ta fita ba kuma ka san tunda ba yadda ta iya don haka sai ta dauki dan ta rungume, ka ji yadda aka yi, amma yanzu Allah Ya sa mahaifar ta fita kuma na yanke cibiyar”, inji shi.
Kangon da matar ta haihu na daura da ofishin Hukumar Kula da Kiyaye Handura ta Kasa (FRSC) a titin da ya tashi daga PZ zuwa Samaru, Karamar Hukumar Sabon Gari, Jihar Kaduna.
Daga baya Jami’an FRSC sun dauki matar a motarsu zuwa Sashen Kula da Walwala da Jin Dadi na karamar hukumar domin ci gaba da lura da ita.