Yadda mata ta kulle dan kishiyarta shekara bakwai a daki
’Yan sanda a Jihar Kano sun ceto wani matashi mai suna Ahmad Aliyu mai shekara 32 da kishiyar mahaifiyarsa ta kulle a daki tsawon shekara bakwai saboda zargin shan miyagun kwayoyi. Ana zargin kishiyar mahifiyar matashin da hada baki da mahaifinsa wanda dukkanninsu suka zarge shi da ta’ammalai da miyagun kwayoyi. Aliyu dai na zaune […]
’Yan sanda a Jihar Kano sun ceto wani matashi mai suna Ahmad Aliyu mai shekara 32 da kishiyar mahaifiyarsa ta kulle a daki tsawon shekara bakwai saboda zargin shan miyagun kwayoyi.
Ana zargin kishiyar mahifiyar matashin da hada baki da mahaifinsa wanda dukkanninsu suka zarge shi da ta’ammalai da miyagun kwayoyi.
Aliyu dai na zaune ne a unguwar Farawa da ke Mariri a cikin Karamar Hukumar Kumbotso.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sun kubutar da matashin ne a ranar Alhamis bayan samun rahotannin sirri daga makwabta a unguwar.
Muna tafe da karin bayani…