Yadda mata ta makale wa mota don ceton diyarta daga barayi

Wata mata mai suna Misis Priscilla Ekpenyong ta yi kuru cikin gwagwarmayar kubutar da diyarta mai kimanin wata tara daga hannun wasu mutane da suka yi yunkurin sace ta  a cikin wata tasi da ta shiga a matsayar mota da ke hotal din Pyramid, don komawa kauyensu Idoma da ke karamar Hukumar Biase.Al’amarin, wanda ya […]

Yadda mata ta makale wa mota don ceton diyarta daga barayi
Yadda mata ta makale wa mota don ceton diyarta daga barayi

Wata mata mai suna Misis Priscilla Ekpenyong ta yi kuru cikin gwagwarmayar kubutar da diyarta mai kimanin wata tara daga hannun wasu mutane da suka yi yunkurin sace ta  a cikin wata tasi da ta shiga a matsayar mota da ke hotal din Pyramid, don komawa kauyensu Idoma da ke karamar Hukumar Biase.
Al’amarin, wanda ya faru a kusa da Barikin Sojoji na Eburutu da ke kan babban titin Murtala Muhammad da ke garin Kalaba, babban birnin Jihar Cross Riber, ya ja wa matar kukkujewa a jika, amma ta kubutar da diyar tata.
Lokacin da take bayyana wa manema labarai yadda lamarin ya faru, a asibitin ’yan sanda da ke Kalaba, inda aka duba ta tare da diyarta, Misis Priscilla ta ce ta shiga motar, wadda kirar bolkswagen Jetta ce, inda ta iske wata mata a ciki, wadda ita ma take rike da yaronta a hannu. Bayan da motar ta yi tafiya kadan ne, sai ta tsaya don daukar wasu maza su biyu, wadanda jim kadan da shigarsu, sai suka bukaci ta ba su diyar da take goye da ita, ta ki.
Matar mai kimanin shekara 23, ta ce: “Na zauna a gaba tare da direba, ita kuma dayar matar tana zaune a baya tare da mutanen biyu, inda daya ya bukaci matar da ta mika musu dan nata. A daidai wannan lokacin ne kuma dayansu ya fara janye ’yata da na yi wa goyon gaba, lamarin da ya sa bai iya kwace ta da sauri ba, amma cikin kici-kicinmu, ya samu ya zaro hannunta. Ya ja hannun da karfi, kamar zai tsinke shi, sai ta fara tsandara kuka. Ni kuma sai na kama kururuwar neman agaji daga jama’a.
“Ganin asirinsu zai tonu, sai suka tunkudo ni wajen motar, amma sai na makale na ki sakin ’yata. Motar ta ja ni a kwalta har kusan nisan misalin mita 500 kafin wasu jami’an tsaro su kawo mana dauki, inda suka yi nasarar cafke mutumin da ya rike hannun diyata, suka kai shi wani ofishin ’yan sanda da ke kusa. Sauran kuma ban san inda suka yi ba.” Inji ta.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rudunar ’Yan Sanda ta Jihar Cross Riber, Mista Hogan Bassey, ya ce direban motar da sauran mutanen sun tsere, amma an kama dayansu, wanda ake tsare da shi a hedkwatar ’yan sanda da ke Kalaba.
Lokacin da yake bayyana dalilin aikata wannan mummunan aikin, wanda aka kama, mai suna bictor Edem-Bassey, mai kimanin shekara 30 da ya fito daga karamar Hukumar Akpabuyo da ke jihar, ya ce matsin rashin kudi ne ya sa shi shiga hakar satar yara, wadda wani abokinsa Essien ya ja shi cikinta.
Ya ce idan sun saci yaran sukan kai wa wani mutum ne mai suna Albertino a wani yanki na Mil 8 da ke Kalabaa, amma bai san inda yake zaune ba domin ya hadu da shi ne cikin wata motarsa kirar Jeep a titin Old Market.