‘Yadda mata ’yan Boko Haram suka hilace mu’

A makon jiya ne mutanen Maiduguri suka yi yammaci da jin kararrakin bama-bamai da bindigogi a Barikin Sojoji na Giwa,, lokacin da sojojin suka yi ta ba-ta-kashi da mayakan Boko Haram da suka kawo musu hari. daya daga cikin matan sojojin da ke barikin na Giwa da ta tsira da ta nemia sakaye sunanta ta […]

‘Yadda mata ’yan Boko Haram suka hilace mu’
‘Yadda mata ’yan Boko Haram suka hilace mu’

A makon jiya ne mutanen Maiduguri suka yi yammaci da jin kararrakin bama-bamai da bindigogi a Barikin Sojoji na Giwa,, lokacin da sojojin suka yi ta ba-ta-kashi da mayakan Boko Haram da suka kawo musu hari.

daya daga cikin matan sojojin da ke barikin na Giwa da ta tsira da ta nemia sakaye sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa tana cikin barikin lokacin da Boko Haram suka shiga, inda ta ce, “Wasu mata ’yan Boko Haram ne suka shiga barikin da farko suna ihu cewa sun zo gudun hijira ne a taimake su a ba su mafaka ga Boko Haram can sun shigo, ashe karya suke yi, sun shigo ne su saje da mu kuma su cuce mu. Shi ke nan sai muka saki jiki da su har zuwa dare ashe akwai bama-bamai a jikinsu, kafin mu ankara suka shiga tayarwa, can kuma mazajensu suka fara ketowa suka kuma shiga arangama da sojojin da suke cikin barikin har aka ci karfinsu, mu dai muna wani cikin rami, har kafin mu samu kanmu.”
Ta kara da cewa “A karshe sai muka ji an ce an ci karfinsu, amma wadacan bama-baman ba su yi mana illa ba a gefen da muka fake, sai dai sun yi illa a wani bangaren barikin.”
Wannan hari ne ya sa Rundunar Soja ta Bakwai da ke Maiduguri ta kafaa dokar hana zirga-zirga na tsawon awa 24 kafin ta sassauta daga baya.
Kuma dokar ce kungiyar Lauyoyi ta Jihar Borno ta ce ba za ta lamunta ba, inda Shugaban kungiyar na jihar Wasi’u Alfa, ya ce dokar da jami’an tsaro ke sa wa al’umma da sunan kare lafiyansu tana ta’azzara wa al’umma ta fuskar rayuwarsu, domin wani sai ya fita yake samun abin kalaci, “To yau an hana fita na wuni guda ko biyu ko daga wani lokaci zuwa wani lokaci, kuma ba a samar masa da yanayin da zai ci abinci da iyalinsa ba, wannan abin ba ya cikin kundin tsarin mulki,” inji shi.