Yadda mata za su lura da lebbansu
Lebba na daya daga cikin abubuwan da ke kara wa mata kyawu, don haka ya kamata su rika kula da lebbansu. Kula da lebba na da mahimmanci kamar yadda ake kula da sauran gabban jiki. Idan lebba suka fashe ko suka tsage sukan rage kyawun mace. Wani lokaci lebba za su kumbura, wanda hakan ma […]
Lebba na daya daga cikin abubuwan da ke kara wa mata kyawu, don haka ya kamata su rika kula da lebbansu. Kula da lebba na da mahimmanci kamar yadda ake kula da sauran gabban jiki. Idan lebba suka fashe ko suka tsage sukan rage kyawun mace. Wani lokaci lebba za su kumbura, wanda hakan ma yakan sanya mata su yi muni. Akwai hanyoyi da dama wadanda suka kamata a bi don kare lebba daga tsagewa. Mata da dama na son ganin sun mallaki lebba masu kyawu, domin hakan na kara wa murmushinsu kima da kyawu.
Wanke lebba: Idan ana da busassun lebba, to ya kamata a rika wanke su kafin a shafa musu kayan kwalliya. Za a iya amfani da buroshin goge baki domin kankare busasshiyar fatar da ke kan lebba. Za a rika zagaya buroshin a kan lebba saboda samun biyan bukata. Za a iya amfani da man zaitun da ruwan soda ko ru wa domin samun sakamako mai kyau.
Amfani da man lebba: Amfani da man lebba na rage fashewar lebba, kuma hakan na sanya lebba laushi da damshi. A yawaita shan ruwa hakan na rage bushewar lebba.
Idan an gama wanke laeba, sai a shafa mata jan baki ko man baki na zamani domin kawata kwalliya.