Yadda haramta sayar da gawayi ya jefa ’yan Zariya cikin kunci

Kamata ya yi jami’an tsaro su killace hanyoyin dazuka su kame duk masu shige da fice a ciki.

Yadda haramta sayar da gawayi ya jefa ’yan Zariya cikin kunci

Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna.

Matakin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauka na hana safarar itace da gawayin girki ya sanya talakawa cikin damuwa.

A makon jiya ne gwamnatin jihar ta haramta safarar itace da gawayi da hawa babura a fadin jihar a matsayin matakan tsaro, lamarin da ya sanya akasarin al’ummar jihar cikin kunci, musamman talakawa.

Wasu da Aminiya ta zanta da su sun bayyana mata irin yadda dokar ta gallabe su.

Malam Zubairu Sani mazaunin Anguwar Tudun Jukun Zariya, ya ce, “Ai mu da ba mu san cewa haka lamarin yake ba sai ga shi mun shiga wani irin halin da sai dai lahaula wala kuwata domin kusan duk wani abu da dan Adam zai rayu da shi yana dab da ya kubuce masa.

“Da muna sayen buhun gawayi Naira dubu daya da dari tara, sai ga shi yanzu cikin kwana biyu ya koma naira dubu uku, shi ko itace ma ai ba a magana; Haka hana hawa babur ko da naka ne, shi ma ya kara sanya mu cikin matsala saboda farashin mota ya tashi ya ninka har sau biyu.

“Al’ummomi na kira ga Gwamnan Nasiru El-Rufai da ya duba halin da talakawa ke ciki da kuncin rayuwa da matsin tattalin arziki ya haifar, ya kyale masu babura wadanda ba na haya ba su yi amfani da abinsu.

“Masu babura da ba na haya ba suna kai iyalansu makaranta suna zuwa gonakinsu sannan suna zuwa wajen aiki a kai.

“Shi kuwa gawayi da itace sun kasance abubuwa masu sauki wajen girki ga talakawa amma a halin yanzu al’amarin ya wuce hankalin talakawa,” inji shi.

Wasu alumomin kuwa cewa suka yi, kamata ya yi gwamna ya sa jami’an tsaro su killace hanyoyin dazuka tare da kame duk wadanda ke shige da fice a cikin dazukan, amma ba a shigo cikin gari a takura jama’a ba yayin da har yanzu masu satar mutane ke ci gaba da cin karensu babu babbaka.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno